Ranar karshe ta ziyara a yankin Wuqing

Ko shakka babu dole a cewa mijin iya baba, dan kuwa kusan duk lardi da yankin da mutum ya zagaya a kasar Sin zai ga ayyukan binkasa na ci gaba duk kuwa da irin tarnakin da matsalar hada-hadar kudi ta duniya ke ci gaba da yiwa kasa da kas.


A yini na uku kuma na karshe da tawagar CRI ta yi ziyara a yankin Wuqing dake birnin Tianjin na arewcin kasar ta Sin, ta bakunci wasu muhimman masana’antu uku. Biyu daga cikin masana’antun na kerawa da harhada kekuna ne, ta farko tana kerawa da hada kekuna da matasa da magidanta ka iya yin amfani da su, a yayin da dayar ke samara da kekunan kananan yara, gami da ‘yam motocin renon jarirai.
Abin sha’awa ne a san cewar, a masana’antar dake samar da kekunan manya, tawagar ta CRI ta sheda wani ci gaban zamani da aka samu, wanda yana da alaka da kera kekunan dake amfani da batiran da kan samar da karfin wutar da kan murza wilin keken, wanda zai iya maye gurbin babura masu amfani da man fetur da bakin mai. Ko shakka babu wannan zai yi tasiri game da yunkurin kiyayewa da kyautata muhalli gami da saukaka dumamar yanayi.


Wani batu da mahukuntan kamfanin suka koka a kai shi ne na ci bayan yawan bukatun da ake da su a kan kayayyaki ko kekunan da suke samarwa, wannan kamar yadda suka kara bayani, yana da nasaba da rikicin hada-hadar kudi, wanda ya zama ruwan dare mai game duniya. Sai dai a cewar mahukuntan kamfanin hakan bai sa sun rage yawan ma’aikatansu ba.