Garin Wuqing da turakunsa na bunkas

A ci gaba da ziyarar da tawagar gidan rediyon kasar Sin take yi a garin Wuqing, a yini na biyu ta halarci wurare da suka kasance za a iya kira da ginshikai ko turakun tabbatar da samun bunkasa mai dorewa a garin da ma a ce yankin Tianjin baki dayansa.


Da farkon fari tawagar ta ziyarci katafariyar harabar “Tiens”, wanda kamfani ne na hadin gwiwar kasa da kasa da ya kunshi kasashe 180. Bayan sauraron jawabi daga mahukuntan kamfanin, tawagar ta ci gaba da kewayawa a garin na Wuqing inda ta sheda ire-iren ayyukan bunkasa kamfuna da kakkafa muhallai ke ci gaba da gudana. A yayin zagayawar ne kuma tawagar ta yi arba da sabuwar tashar jirgin kasa mai saurin tafiyar nisan sama da kilomita 300 a sa’a guda.


Har ila yau, abin alfahari ne a bayyana ziyartar wani kauyen da aka sabuntawa manoman dake zaune a wurin ta hanyar giggina musu sabbin gidajen zamani, mai suna “Hou Pu Ba”, wanda ake cike da fatan zai samu damar jawo hankalin masu sha’awar yawon shakatawa.