Yankin Wuqing mai karamci ga baki


Tawagar gidan rediyon kasar Sin da ta ziyarci garin Wuqing dake yammacin birnin Tianjin na kasar ta Sin a ranar Juma'a 8 ga watan Mayun shekara ta 2009, ta samu kyakkyawar tarba daga mahukuntan garin.


Mun sauka a otal din Swan lake International Hotel inda aka shirya mana kyakkyawar tarba ta hanyar shirya mana lokacin cin abinci na gargajiyar garin, koda yake dama Sinawa sun saba saukar baki ta hanyar shirya kabakin nau'o'in abinci. Bayan kammala cin abinci, an kai mu wajen da aka shirya mana wasannin wake-wake da wasu daga cikin mahukunta garin da kansu suka rera.


Kafin mu kai ga wannan waje na kasaita da muka sauka, wani abin sha'awa shi ne mun wurwuce wasu manya-manyan kamfuna da suka yi mana marhabi.