http://www.beijing-olympic.org.cn/
Disamba, 2008 / Home / Sin Ciki da Waje / Email Us /Print this page

Gabatarewa:

 

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 30 da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin. A cikin wadannan shekaru 30 da suka gabata, kasar Sin da kasashen Afirka sun kuma kara yin hadin guiwa domin neman cigaba tare. Sannan kuma Sinawa sun samu sauye-sauye sosai a fannonin tufafi da abinci da gidajen kwana da zirga-zirga a cikin wadannan shekaru 30 da suka gabata...

Babi na farko:
  Madam Yang wadda ta gina wata babbar hasumiya mai samar da ruwa a Hamadar Sahara
Babi na biyu:
  Dalibai masu dalibta na Sin da Afirka sun shimfida gadar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu
Babi na uku:
  Cibiyar fasahar wasannin gargajiya ta kasar Sin ta yi bikin baje koli don mai da hankali kan fasahar wasannin gargajiya ta Afirka
Babi na hudu:
Sannu! Likita!
Babi na biyar:
  Cigaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru 30 da suka gabata a fannonin tufafi
Babi na shida:
  Bunkasuwar abinci na jama'ar kasar Sin cikin shekaru 30 da suka wuce
Babi na bakwai:
  Bunkasuwar gidajen kwana na jama'ar kasar Sin cikin shekaru 30 da suka wuce
Babi na takwas:
  Sauyawar keke samfurin ¡°Yong Jiu¡± a cikin shekaru 30 da suka gabata
Zabi sonka:   Kai Sama
Babi na farko Babi na biyu Babi na uku Babi na hudu Babi na biyar Babi na shida Babi na bakwai Babi na takwas
Babi na farko Babi na biyu Babi na uku Babi na hudu Babi na biyar Babi na shida Babi na bakwai Babi na takwas
 
 
  Babi na farko: Kai Sama
Madam Yang wadda ta gina wata babbar hasumiya mai samar da ruwa a Hamadar Sahara

Shekarar nan shekara ce ta 30 da aka gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa a kasar Sin. A cikin wadannan shekaru 30, an samu babbar bunkasuwa a dukkan fannoni, ba ma kawai sakamakon da aka samu wajen aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ya kawo moriya ga jama¡¯ar kasar Sin ba, hatta ma, ya ingiza bunkasuwar dangantakar abokantaka dake kasancewa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

A cikin wadannan shekaru 30, kasar Sin tana yin iyakacin kokari wajen ba da tallafi ga kasashen Afrika, ya zuwa karshen shekara ta 2007, ta yi wa kasashen Afrika ayyuka fiye da 800, wadanda suka shafi masana¡¯antu da aikin noma da zirga-zirga da tarbiyya da kiwon lafiya da kuma manyan ayyukan yau da kullum da dai sauransu. Suna takawa muhimmiyar rawa a wadannan kasashe. Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani bayani game da aikin samar da ruwa da kasar Sin ta gina a Jamhuriyar Nijer.

Ruwa mahaifiyar rayuka ce. Shi ya sa, darajar ruwa dake a yanki dake fama da karancin ruwa kan daga. Ranar 24 ga watan Yuni na shekarar 2005 wata rana ce ta farin ciki ga mutanen birnin Zinder. A wannan rana, mutanen birnin suna cike da jikuwa, sun fito daga gidaje don yin murnar gama aikin gina hasumiyar samar da ruwa a wannan wurin dake kudancin hamadar Sahara, wadda za ta kawo karshen matsalar rashin ruwan sha a nan.

Don haka, mutanen birnin ba za su manta da wadda ta tsara fasalin wannan hasumiya wato Madam Yang Fenglan ba. Madam Yang dake aiki a kwalejin bincike da tsara fasali kan ayyukan ruwa na birnin Beijing ta taba zuwa kasar Nijer har sau 4, mutanen kasar Nijer suna kiranta Madam Yang.

Mun yi sa¡¯a, a kwanakin baya, mun samu damar neman labari daga wajenta, inda ta gaya mana halin kasancewarta na watanni 21 da take aiki a birnin Zinder na kasar Nijer.

Birnin Zinder shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijer a cikin tarihi, amma sabo da karancin ruwa a kowace shekara, gwamnatin Nijer ta zabi birnin Niamey ya zama hedkwatar kasar don maye gurbin birnin Zinder. Daga bisani, birnin Zinder yana fama da rashin ruwa, mutane fiye da dubu dari ba su samun issashen ruwan sha.

Ya zuwa watan Satumba na shekarar 2002, injiniyoyin ruwa na kasar Sin sun isa Jamhuriyar Nijer a karo na farko don fara gina ayyukan samar da ruwa a birnin Zinder. Madam Yang Fenglan ta yi waiwaye adon tafiya ta ce,¡°Daga watan Satumba zuwa watan Oktoba na shekarar 2002, mun yi bincike a wurin, daga bisani, mun dawo gida mun tsara fasali na matakin farko. Sa¡¯anan, a watan Afril zuwa watan Mayu na shekarar 2004, mun yi bincike da nazari a karo na 2 a wurin. A karshe dai, a watan Oktoba na shekarar 2003, mun fara ayyukanmu.¡±

Kyakkyawan mafari wani kashi ne mafi muhimmanci na wani aiki. Yin bincike a matakin farko na aikinmu, shi ma wani muhimmin mataki ne. Amma, injiniyoyin kasar Sin sun gamu da wahalhalu da yawa a wannan mataki. Madam Yang ta ce, ¡°A wancan lokaci, lalle mun gamu da wahalhalu da yawa, ko da yake mun yi aikin share fage sosai. Ambaliyar ruwa ta datse hanyarmu, mun yi sa¡¯o¡¯I 27 muna jiran taimako.¡±

Ban da wannan kuma, sabo da rashin takamaiman rahoto kan yanayi da koguna dake wurin, injiniyoyin kasar Sin sun yi bincike su da kansu. Ko da yake, sun gamu da wahalhalu da yawa, amma a karshe dai, sun gama aikin bincike da kyau, Madam Yang ta ce, ¡°Tsawon manyan bututun samar da ruwa ya kai kilomita 25, kuma tsawon sauran bututu ya kai kilomita 12, muna bukatar yin bincike kan dukkan wadannan bututu. A karo na farko da muka je birnin, muhimmin aikinmu shi ne tabbatar da wuraren da wadannan bututun za su wuce, shi ya sa, mu kan yi kai da kawowa a kan wannan hanyar wadda tsawonta ya kai kilomita 30.¡±
Kasar Sin ta dauki nauyin tsara fasali da yin wannan aikin samar da ruwa, kuma kasar Sin ta ware kudaden don gina shi. A yayin da take magana kan dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta yi wannan aiki, Madam Yang ta ce, ¡°An mai da wannan aiki a matsayin aikin gaggawa a Jamhuriyar Nijer. Mazaunan birnin ba su iya samun ruwa ko kadan ba a yanayin rani. Na ga farar hula da yawa dake neman ruwa a ko ina. A yanayin damina, akwai ruwa a tabki, amma a yanayin rani, ruwa yana kasancewa tare da rairayi, sabo da haka, ana kasa yin amfani da wannan ruwa. Kasar Sin ta yi wannan aiki ne don daidaita matsalar da farar hula suke fuskanta.¡±

Duk wanda ya taba zuwa birnin Zinder yana iya ganin wani shahararren gini, wato babbar hasumiya mai samar da ruwa. A ran 24 ga watan Yuni na shekarar 2005, bayan watanni 21 da aka yi kokarin aikin bincike da tsara fasali da kuma ginawa, kasar Sin ta cimma nasarar gama aikin gina babbar hasumiya mai samar da ruwa a birnin Zinder. A wannan rana, dukkan mutanen birnin Zinder sun yi farin ciki matuka, dubban mutane sun taru a gindin hasumiyar. Shugaban kasar Nijer Mamadou Tandja, shugaban majalisar wakilan jama¡¯ar kasar Mamman Usman da kuma sauran ministocin kasar da ¡®yan majalisa da yawa su ma sun halarci bikin yanke kyalle ga babbar hasumiya a birnin Zinder dake da nisan kilomita fiye da 900 daga birnin Niamey, babban birnin kasar Nijer. Madam Yang ta waiwaya da cewa, ¡°A lokacin da muke gina hasumiyar, mazaunan birnin suna ta dora muhimmanci sosai kan aikinmu, kuma suna yin bege ga wannan hasumiyar samar da ruwa. Sabo da haka, a yayin da muka gama aikin, kusan daukacin mutanen birnin sun tsaya a kan titi don yin murna. Wannan hasumiyar da muka gina yana kan wani tsauni, amma mun kasa ganin wannan tsauni, sabo da yawan mutanen dake wajen, shugaban kasar Nijer da shugabanni da ¡®yan majalisa na kasar da kuma ma¡¯aikatan ofishohin jakadancin kasashen waje su ma sun halarci bikin yanke kyalle.¡±

Madam Yang ta gaya mana cewa, birnin Zinder garin shugaba Tandja ne. A gun bikin, malam Tandja ya yi bayani kan tarihin neman ruwa a wannan birni. Ya ce, an yi shekaru da yawa ana tattaunawa kan wannan aikin samar da ruwa, bangaren Nijer ya nemi tallafi daga kasashe daban daban. Bayan kasar Nijer ta nemi taimako wajen kasar Sin, Sin ta amsa gayyatar kasar Nijer nan da nan. Ya furta cewa, kasar Sin kawar ainihi ce ta Jamhuriyar Nijer, ya nuna godiya ga tallafin da gwamnatin kasar Sin ta bayar.
Aikin samar da ruwa ya ceci birnin Zinder dake karancin ruwa a tsawon tarihi. Muna iya cewa, ya samu yabawa sosai daga mutanen birnin. Bayan da aka cimma nasarar gama aikin gina hasumiyar samar da ruwa, farashin ruwa ya sauka, zaman rayuwar jama¡¯a ya samu kyautattuwa sosai. A sa¡¯i daya kuma, wannan aiki ya sada sassan birnin da ruwa, fiye da da, mutanen dake cibiyar birnin suna iya samun ruwa kai tsaye, yanzu, galibi dai, aikin ya daidaita matsalar karancin ruwan sha a birnin. An labarta cewa, za a cigaba da gina wannan aikin samar da ruwa, za a hada sabon bututu da wadanda Madam Yang ta gina, za a iya cimma burin samar da ruwa zuwa wajen birnin Zinder.

Injiniyoyin kasar Sin sun samu girmamawa daga gwamnati da jama¡¯ar kasar Nijer, haka kuma, shugaban kasar Nijer ya gana da Madam Yang da sauran injiniyoyin kasar Sin har sau 4, Madam Yang ta samu lambar yabo da shugaban Nijer ya bayar a watan Agusta na shekarar 2006.

Aikin samar da ruwa da kasar Sin ta yi ya kyautata zaman rayuwar mutanen birnin Zinder, kuma ya sada dankon zumunci tsakanin kasashen biyu. A lokacin da take aiki a birnin Zinder, Madam Yang ba ta saba da yanayin wurin ba, ta kamu da zazzabin cizon sauro har sau 2. Amma, ta ci gaba da aiki a can.

Madam Yang Fenglan ta ce, abin da ya ba ta kwarin gwiwar cigaba da gudanar da aiki shi ne zumuncin dake tsakaninta da mazaunan birnin. Ta ce, ¡°Na yi iyakacin kokari a kan wannan aiki, a sa¡¯I daya kuma, na fahimci mutanen Afrika ta wannan aiki. A wadannan shekaru biyu, na gamu da wahalhalu da yawa, alal misali, zazzabin cizon sauro. A lokacin da nake fama da zazzabin cizon sauro, ina kwana a kan gado, kawayena na Afrika suna zuwa wurina don gaishe ni tare da ba ni kyauta. Amma a hakika dai, suna fama da talauci sosai. Ta haka, sun burge ni kwarai da gaske. A wadannan watanni 21, ko da yake, na yi fama da wahalhalu da yawa, amma na yi farin ciki, kuma ina son Afrika matuka.¡±

A shekarar 2006, Madam Yang Fenglan ta je birnin Zinder a karo na 4. A lokacin da ta isa birnin, dahun dare ya yi, amma ba ta yi tsammani ba, mazaunan birnin da yawa sun riga suna jiranta a can. Madam Yang ta ce, ¡°Mazaunan birnin da yawa sun tsabtace wurin da na taba zama a da, suna fatan zan cigaba da zama a can. Sun yi tadi da ni kan aikin samar da ruwa. Sun burge ni sosai¡­.¡±

Madam Yang ta tuna da mazaunan birnin sosai. Tana fatan za ta gaishe da kawayenta dake kasar Nijer daga nan gidan rediyon kasar Sin.

¡°Sannunku, mutanen birnin Zinder, na gode muku sabo da taimakon da kuka ba ni. Kuma ina tunawa da ku sosai da sosai. Ina fatan za ku ji dadin zamanku, ku zama lafiya!¡±

  Babi na biyu:   Kai Sama
Dalibai masu dalibta na Sin da Afirka sun shimfida gadar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu

G: Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, shirin da kuke saurara shi ne shirin musamman da muka tsara kan hadin gwiwar Sin da Afirka a cikin shekaru 30 da suka gabata don samun bunkasuwa tare. Kuma ni ne Garba Shuaibu Dakata tare kuma da abokiyar aikina, Lubabatu muke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

L: Masu sauraro, assalamu alaikum. A cikin shekaru kusan 60 da suka gabata bayan kafuwar Jamhuriyar Jama¡¯ar Kasar Sin, musamman ma a cikin shekaru 30 da suka gabata bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar bude kofa ga waje da kuma yin kwaskwarima a gida, dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta samu ci gaba yadda ya kamata, kuma bangarorin biyu suna ta inganta hadin kansu a fannin aikin koyarwa. Ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta kulla dangantaka tare da kasashen Afirka fiye da 50 kan yin cudanyar aikin koyarwa ta hannyoyi daban daban.

G: Masu sauraro, abin da kuka saurara tsaraba ce da wakilinmu ya samu daga wani ajin koyon harshen Hausa na jami¡¯ar koyon harsunan waje ta Beijing. Sunan malamar wannan aji Suwaiba, wadda ta fara koyon harshen Hausa tun shekaru 12 da suka gabata.

L: E, haka ne, Malam Garba, watakila ba ka sani ba, Suwaiba malamata ce lokacin da nake karatu a jami¡¯a. A shekarar 2003, bisa yarjejeniyar ilmi da aka kulla tsakanin gwamnatin Sin da ta Nijeriya, an tura malama Suwaiba tare da takwaran aikinta zuwa Nijeriya, inda gwamnatin Nijeriya ta ba su kyautar kudin karatu da kuma dakunan kwana. Bayan da Suwaiba ta dawo gida bayan da ta gama karatunta a Nijeriya, ta taba gaya mini cewa, ta je yawon bude ido a wurare daban daban na Nijeriya, kuma lallai ta karo ilmi kwarai da gaske dangane da harshen Hausa. ¡°Wannan ziyara ta kara mini kyakkyawar fahimta game da kasar Nijeriya har ma da nahiyar Afirka baki daya. Wannan na da ma¡¯ana ta musamman, sabo da mu masu koyon harshen Hausa kamar manzanni ne dake tsakanin Sin da Nijeriya, samun kyakkyawar fahimta wani tushe ne lokacin da muke yada al¡¯adu na kasashen nan biyu.¡±

G: Bayan da malama Suwaiba ta komo gida, tana nan ta dukufa ka¡¯in da na¡¯in kan aikin koyarwa. Ta cigaba da bayyana cewar: ¡°Dukkan ilimi da na samu daga Nijeriya ya amfana mini kwarai da gaske, na koyar da dalibaina Kananci, da tarihin Hausawa, da irin tasirin da Musulunci ke yiwa arewacin Nijeriya da dai sauransu, ina fata in bayar da ¡®yar gudummowa wajen kara dankon zumunci tsakanin Sin da Nijeriya, ni a wajena kuma har abada ba zan manta da zumuncin da dukkanin jama¡¯ar Nijeriya suka nuna mini ba.¡±

L: Gaskiya ne, aikawa da dalibai ga kasashen juna wani muhimmin fanni ne wajen yin cudanya da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin koyarwa. Kuma har kullum kasar Sin tana sa muhimmanci kan daukar dalibai daga Afirka. Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama¡¯ar kasar Sin a shekara ta 1949 ba da jimawa ba, kasar Sin ta taba karbar dalibai fiye da goma da suka zo daga kasashen Masar da Kenya da Kamaru da dai sauransu, amma ya zuwa karshen watan Satumba na shekara ta 2007, gwamnatin kasar Sin ta riga ta samar da tallafin karatu gadalibai dubu 21 na kasashen Afirka 50.

G: Ba kawai karuwar yawan daliban masu dalibta na Afirka a kasar Sin ba, har ma lallai sun samu gogewa sosai. A cikin wadannan daliban Afirka da kasar Sin ta horar, wasu sun zama shugabannin majalisun dokoki da ministoci, wasu kuma suna gudanar da ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka kan tattalin arziki da cinikayya, sabo da haka suna bayar da babbar gudummowa kan sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar aminci tsakanin Sin da Afirka.

L: A daidai sabo da haka, ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta zama daya daga cikin kasashen da daliban Afirka suka fi sha¡¯awar yin karatu gare su a ciki, haka kuma ita wata kasa ce da ta fi daukar yawan daliban Afirka a Asiya. Zhao Lingshan, shugaban sashen kula da daliban ketare da ke karo ilmi a Sin na ma¡¯aikatar ilmi ta kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, yawan daliban ketare na Afirka da suka zo kasar Sin don kara ilminsu ya samu saurin karuwa, kuma matsakaiciyar jimlar ta kan karu da kusan kashi 20 cikin kashi dari a ko wace shekara. Kuma ya ce, ¡°Bayan da ta bude kofa ga waje da kuma yin kwaskwarima a gida har shekaru 30, har kullum kasar kamarmu ta Sin tana cikin zaman kwanciyar hankalin siyasa, da samun bunkasuwar tattalin arziki, da kuma karin ci gaban kimiyya da fasaha. Sabo da haka kasarmu tana ta jawo hankulan matasa na duniya.¡±

G: Masu sauraro, ban da wadannan dalilan da suka sanya ¡®yan Afirka su nuna sha¡¯awa ga kasar Sin wajen kara ilminsu, wani muhimmin dalili daban shi ne a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka kan hadin gwiwa da aka yi a watan Nuwamba na shekara ta 2006, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya taba dan alkawarin cewa, kafin shekara ta 2009, yawan daliban Afirka da za su samu taffalin karatu daga wajen gwamnatin kasar Sin zai karu daga 2000 zuwa 4000 a ko wace shekara. Kuma lokacin da shugaba Hu ke jawabi a Jami¡¯ar Pretoria ta kasar Afirka ta Kudu a farkon shekara ta 2007, ya sake jaddada muhimmancin alkawari, inda yake cewa, ¡°Samu ko rasa kara samun bunkasuwar nahiyar Afirka suna dogara kan karfin matasa na Afirka. Matasa na Sin da Afirka muhimmin karfi ne wajen kara dankon zumunci tsakanin bangarorin biyu, haka kuma su muhimmin karfi ne wajen raya duniya mai jituwa. Gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsai da kudurin cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa, yawan daliban Afirka da za su samu taffalin kudin karatu daga wajen gwamnatin kasar Sin zai karu daga 2000 zuwa 4000 a ko wace shekara. Haka kuma gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin gayyatar matasan Afirka 500 ciki har da dalibai don yin ziyara a kasar Sin a cikin shekaru uku masu zuwa.¡±

L: Masu sauraro, abin da kuka saurara dazun nan wani dan bayani ne da Florintine, wata ¡®yar kasar Ghana ta yi da Sinanci domin gabatar da kanta. Yanzu Florintine tana koyan Sinanci a Jami¡¯ar koyon harsuna da al¡¯adu ta Beijing. Ta gaya wa wakilinmu cewa, ta yi sa¡¯a da ta iya samun wannan dama wajen koyon Sinanci a kasar Sin, shi ya sa tana yin matukar kokari wajen karatu. Kuma ta ce, ¡°A lokacin darasi, na kan mai da hankali a kan koyon Sinanci, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da wannan wata muhimmiyar hanya ce wajen koyon Sinanci, kuma bayan aji, na kan duba shirye-shiryen talibijin na kasar Sin, ta haka, na iya kara fahimtar fim da wasan kwaikwayo na Sin da kuma al¡¯adun kasar Sin.¡±

G: Haka kuma ta yin karatu a kasar Sin a ¡®yan shekarun nan da suka gabata, Florintine ta gano sauye-sauyen kasar Sin a fannoni daban daban wadanda a cewarta sun burge ta kwarai da gaske. Kuma ta ce, ¡°A ganina, bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen ketare da yin kwaskwarima a gida, lalle ta bude babbar kofa ga kasashen waje, ta yadda baki suka iya zuwa kasar Sin don yin ciniki da nazarin kimiyya da kara ilimi da sauransu. Kuma ta yin haka, kasar Sin ta samu ci babban ci gaba ta hanyar koyon sakamako masu kyau da kasashen waje suka samu wajen samun bunkasuwa. Kasar Ghana ita ma ta samu bunkasuwa sosai a fannonin muhimman ayyukan yau da kullum da tattalin arziki da kuma demokuradiya. Amma ba a iya raba bunkasuwar Ghana daga kasar Sin, wadda ta fi taka muhimmiyar rawa ga kasar Ghana, shi ya sa dangantakar tsakanin kasashen biyu ta samu ingantuwa ta hanyar hadin gwiwarsu.¡±

L: Gaskiya ne, hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin koyarwa ya sa kaimi sosai ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu kamar yadda ya kamata, da kara fahimtar juna, da kuma inganta zumuncin da ke tsakanin jama¡¯ar bangarorin biyu.

 
  Babi na uku:   Kai Sama
Cibiyar fasahar wasannin gargajiya ta kasar Sin ta yi bikin baje koli don mai da hankali kan fasahar wasannin gargajiya ta Afirka

Cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan musayar da kasar Sin da kasashen Afirka suke yi a wajen al¡¯adu, kuma za mu shiga cikin wata cibiyar fasahar wasanni ta kasar Sin, mu ga yadda ake mai da hankali kan fasahar wasannin gargajiya ta Afirka, da yadda ake kokarin yada al¡¯adun Afirka a kasar Sin don jama'a su kara samun wayewar kai.

¡°Kida kamar wani sako ne. Bisa sakon, an tara mutanensu a asirce. Sa¡¯an nan za a kashe sarkinsu. Shi ya sa da aka ji kidar, za a shiga hali na zaman dardar, kuma za a jira juyin sarauta.¡±

Cikin wata cibiyar nuna fasahar wasanni mai suna ¡®Gada¡¯ ta birnin Beijing, ana bayani kan wani tsohon kayan gargajiya da aka samu a kasar Kamaru, wadda ita ce wata gangar da tsayinta ya kai kirjin mutum. Shekaru dubu daya da suka wuce, cikin kungurmin dajin Kamaru, buga gangar na da alamar kirawo dattawa don su yanke shawarar tube da kuma kashe sarki maras kyaun hali na wannan zamani.

ran 30 ga watan Nuwamba, cikin cibiyar nuna fasahar wasanni ta Gada, an yi bikin bude wani baje koli mai taken ¡®fasahar wasannin gargajiya da zaman zamani¡¯, wanda kungiyar ¡®yan kasuwan kasashen Sin da Afirka, da ofishin jakadancin kasar Kamaru da ke nan birnin Beijing, da cibiyar Gada, suka hade wajen shirya baje kolin don nuna fasahar wasannin gargajiya na Afikra.

Za a kwashe wata daya ana yin wannan baje koli, kuma ana baje kolin kayayyakin gargajiya na Afirka fiye da 500, wadanda suka hada da kayan sassakar itace da dutse, da kayayyakin kida, da kayayyakin addini, da dai sauransu. Ban da gangar da muka ambata, ya kasance da gumakan da aka yi su da dutsen tauraro, da kayan sassakar itace mai siffar giwa, da kujeru, da katakon dara, da abubuwan rufe fuska.

Guo Dong, wanda ya shirya bikin baje kolin, da kuma samar da yawancin kayayyakin baje koli, ya yi shekaru 18 yana zaune a kasar Uganda. Shi ya sa ya fahimci fasahar wasannin Afirka sosai. Yana tsammanin cewa fasahar wasannin gargajiya ta Afirka ta nuna halin mutanen Afirka na bin gaskiya da rashin yaudarar idanun mutane. Haka kuma, ta mika wa zuriyar baya tunanin mutum kan fasahar gargajiya, yadda ta yi babban tasiri kan fasahar wasannin zamani na kasashen Turai. Guo Dong ya ce, ¡®Ina gabatar da kayayyakin ga jama¡¯a, da nufin nuna musu yadda al¡¯adun Afirka suke. Haka kuma, mun ba masu zanen gine-gine da masu zanen hoto wata damar koyon darasi daga wajen. ¡¯ Guo Dong ya ce, wasu kwararrun fasahar wasannin Turai, kamar Mista Picasso na kasar Spain, sun koyi abubuwa da yawa daga fasahar wasannin gargajiya ta Afirka. Shi ya sa ya yi imanin cewa, za a iya hado wayewar kan mutanen kasar Sin da fasahar wasannin gargajiya ta Afirka tare.

Mista Zhao Shu-lin, shugaban cibiyar fasahar wasanni ta Gada, inda ake shirya baje kolin, ya ce, bisa musanyan al¡¯adu da kasar Sin da kasahen Afirka suke yi, za a samu amincewar juna kan tsarin ka¡¯idojin rayuwar mutanensu, duk da cewar, ya kasance da tazara mai nisa da bambancin al¡¯ummomi a tsakanin nahiyoyin 2. Shi ya sa musayar ka iya zaman wata gadar dake hada mutanen Sin da jama¡¯ar Afirka. Don haka, Mista Zhao ya kan shirya tarurrukan nune-nunen kayayyakin Afirka cikin cibiyarsa. Aikinsa ya samu tallafi daga wajen gwamnatocin Sin da kasahen Afirka.

Mista Zhao ya ce, lokacin da ake gasar wasannin Olympics a birnin Beijing a bana, cibiyar Gada ta shirya baje koli kan kayayyakin sassakar itace na kasashen Afirka, inda aka karbi baki ¡®yan afirka da yawa, cikinsu akwai jakadun kasashen Afirka fiye da 20, da shahararrun ¡®yan wasan motsa jiki na kasashen Afirka. Bayan wannan kuma, cibiyar Gada ta shirya taron gabatar da wuraren shakatawa na kasar Kamaru, don wayar da kan jama¡¯ar kasar Sin dangane da yadda za a yi yawon shakatawa a kasar Kamaru. Haka kuma, a wannan karo, an shirya baje koli na ¡®fasahar wasannin gargajiya ta Afirka da zaman zamani¡¯, don shigar da fasahar wasannin gargajiya ta Afirka cikin zaman yau da kullum na jama¡¯ar Sin, yadda za a iya duba kayayyakin keke da keke, da kuma saye da ajiye su a gida.

Ban da baje kolin kayayyakin gargajiya, an gayyaci jami¡¯an kasahen Afirka da kwararru a fagen fasahar wasanni na kasar Sin zuwa cibiyar, don bayyana da tattaunawa kan halin kayayyakin gargajiyar Afirka da darajarsu. Edouard Alluma, wani minista na ofishin jakadancin kasar Kongo Kinshasa dake Beijing ya gamsu da salon da ake bi don gudanar da bikin baje kolin, ya ce, ¡®Wani abu mai kyau shi ne, masu kallo za su iya matsowa kusa, su daba wadannan kayayyakin. Ba kamar cikin gidan kayan gargajiya ba, inda ake rufe kayan da gilashi. Don haka za a fahimci yadda ake amfani da kayayyakin cikin zaman rayuwar ¡®yan Afirka, za a san cewa kayan ba abin kallo ne ba. ¡¯

Frofesa Zhao Meng na kwalejin koyon fasahar wasanni ta jami¡¯ar Tsinhua da ke Beijing, ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka suna musaya da juna sosai kan tattalin arziki, amma, a wajen al¡¯adu, ba a samun musaya da yawa a tsakaninsu. Shi ya sa ganin kyawawan kayayyakin gargajiyar Afirka da yawa haka, ya sa shi mamaki da farin ciki. Yana da imani kan cewar kayayyakin gargajiyar Afirka za su kawo wa kasar Sin cigaban aikin fasahar wasanni. Frofesa Zhao Meng ya ce, ¡®Kayan gargajiyar Afirka ya ba da babban tasiri kan bunkasuwar fasahar wasannin zamani. Yau cibiyar Gada ta kawo kayayyakin gargajiyar Afirka zuwa Beijing, wannan zai yi amfani wajen inganta sanin juna da musayar da muke yi a wajen al¡¯adu. Ta hakan, watakila za a fara samun wasu kwararrun fasahar wasannin, da wasu nagartattun kayayyakin fasahar wasanni a kasar Sin.¡¯

Frofesa Emphraim Kamuntu, mataimakin ministan yawon shakatawa da cinikayya da masana¡¯antu na kasar Uganda, shi ma ya hallarci taron tattaunawar. Ya ce, duk da cewar ya zo kasar Sin don neman inganta hadin kan kasashen 2 kan cinikayya da masana¡¯antu, yana da sha¡¯awar shiga taron. Domin cikin kowace musayar da ake yi a tsakanin jama¡¯ar kasashen 2, ba za a rasa musayar al¡¯adu ba. Ganin wadannan kayayyakin Afirka a kasar Sin ya sa shi murna sosai, domin abun na da alamar cewa, aikin kare kayayyakin gargajiya a Afirka ya samu nasara. Frofesa Emphraim Kamuntu na ganin cewa, al¡¯adun Sin da Afirka na da halin da ya yi kama da juna, wanda za a mai da shi wani tushe na musayar juna, inda ya ce ¡®Kasar Sin da kasashen Afirka suna da tarihi da al¡¯adu da ke kama da juna, ra¡¯ayinmu kan addini da tsarin ka¡¯idojin rayuwar mutane kusan irin daya ne. Dukkanmu kwararru ne wajen fasahar wasannin bil adama .¡¯

Mutane masu tara kayayyakin gargajiya da jama¡¯a masu kallo sun nuna sha¡¯awa sosai kan baje kolin da ake yi. Madam Ma, mai son tara kayan gargajiya, ta bayyana cewa, ¡®Na ga kyawawan abubuwa da yawa, kuma na fara fahimtar tarihi da addini da al¡¯adu na mutanen Afirka. Samun wayewar kai kan wadannan abubuwa na da amfani sosai. Fatana shi ne, a nan gaba za a kara shirya baje koli kamar haka, ta yadda za a bayyana wa mutane halin da Afirka ke ciki.¡¯ Mista du da ke kashe kwarkwafar ido a bikin, ya ce, ¡®Da ma ina sha¡¯awar al¡¯adun Afirka sosai, sai dai ban samu damar gani da idanuna ba. Ga shi , yau na samu damar bude ido. Ya sa na kara sanin Afirka.¡¯

Mista Zhao Shulin, shugaban cibiyar Gada ya yi bayani kan shirinsa na gaba kan aikin cibiyarsa. Inda ya ce , ¡®Muna shirya gina wata cibiyar musayar al¡¯adu tsakanin Sin da Afirka a dab da cibiyarmu ta Gada, inda za mu dinga nuna wa mutane fasahar wasannin Afirka, da rawar Afirka, da kayan gargajiya.¡¯ Mista Zhao ya ce, za su hada kai da jami¡¯o¡¯in koyon fasahar wasanni, da cibiyoyin binciken Afirka, don kafa wani wurin da ake koyar da fasahar wasanni da ilimi dangane da Afirka. Haka kuma, za su gabatar wa jama¡¯ar Sin abincin Afirka da kowane irin fasahar wasannin Afirka, yadda jama¡¯a za su samu damar fahimtar kyawawan halayen nahiyar Afirka.

  Babi na hudu:   Kai Sama
Sannu! Likita!

Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 30 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga kasashen waje. A cikin wadannan shekaru 30, kasar Sin ta sami manyan sauye-sauye, haka kuma, ya raya hulda a tsakaninta da kasashen Afirka daga dukkan fannoni. In muna cewa, ingantuwar hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da ciniki ta kara kyautata huldarsu sosai, to, hadin gwiwarsu ta fuskar kiwon lafiya ita ce harsashin da suka aza domin raya huldarsu. Goman kungiyoyin kiwon lafiya da kasar Sin ta tura zuwa Afirka su ne suke nuna mana irin wannan kyakkyawar hadin gwiwa.
A shekarar 1963, kungiyar kiwon lafiya ta kasar Sin ta kaddamar da aikinta a kasar Algeria bisa gayyatar da gwamnatin Aljeria ta yi wa gwamnatin Sin. Daga nan kasar Sin ta fara sauke nauyin jin kai ga kasashen duniya. Wannan kungiyar kiwon lafiya ta zama ta farko da kasar Sin ta tura zuwa kasashen waje domin ba da hidimar kiwon lafiya, haka kuma, a Afirka.

Wang Liji, mataimakin darektan sashen yin hadin gwiwa da kasashen waje na ma¡¯aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya yi mana bayani kan halin da wannan kungiya ke ciki a wancan lokaci. Mr. Wang ya ce,¡°A shekarar 1963 kasar Sin ta tura kungiyar kiwon lafiya ta farko zuwa Algeria. A wancan lokaci, Algeria ta kafu ba da dadewa ba, tana karancin likitoci sosai, shi ya sa ta bukaci gwamnatin Sin ta tura mata kungiyar kiwon lafiya. Ko da yake a wancan lokaci, kasar Sin ita ma tana karancin likitoci, amma domin taimakawa kasashe masu tasowa, gwamnatin Sin ta kungiyoyin kiwon lafiya zuwa Afirka da sauran kasashe masu tasowa, ta dade tana yin haka har tsawon shekaru 45 ba tare da tsayawa ba.¡±

Har zuwa yanzu kungiyoyin kiwon lafiya na kasar Sin guda 50 da ke kunshe da mambobi 1278 suna aiki a kasashe 49 na duk duniya, ciki har da wasu 980 suna ba da hidimar kiwon lafiya ga jama¡¯ar Afirka.

Wadannan mambobin kungiyoyin kiwon lafiya da kasar Sin ta tura musu zuwa Afirka sun jure wahalhalu a zaman rayuwa da ayyuka da kuma harsuna, suna bauta wa mazauna wurin da zuciya daya kuma cikin sahihanci. Ba kawai suna warkar da cututtukan da aka saba kamawa ba, har ma sun sami nasarar kammala tiyata masu wuyar aikatawa kan zuciya da dai sauransu, sun kubutad da mutane da yawa da suka taba bakin mutuwa. Ban da wannan kuma, wadannan mambobin kungiyar kiwon lafiya na kasar Sin suna mai da hankali kan ba da taimako wajen kyautata matsayin kiwon lafiya na wurin, sun sa kaimi kan kyautatuwar matsayin kasashen Afirka da suke aiki a ciki a fannin kiwon lafiya.

Bugu da kari kuma, likitocin kasar Sin sun taimaka wa takwarorinsu na Afirka da su sami damar samun aikin horaswa a kasar Sin. Li Yun, wani likita ne daga birnin Beijing, ya komo Beijing ba da dadewa ba daga kasar Guinea ya gaya mana cewa,¡°A matsayina na shugaban kungiyar kiwon lafiya da kasar Sin ta tura zuwa Guinea, ina kokarin taimakawa takwarorina na Afirka samun aikin horaswa a kasar Sin. A cikin shekaru 2 da nake aiki a Guinea, na nemi dama guda 15 ga takwarorina na Afirka da su zo Beijing da Shanghai da kuma Chengdu domin samun aikin horaswa. Irin wannan aikin horaswa ya sami karbuwa sosai daga takwarorina na Afirka.¡±

Likitocin Afirka da yawa sun nuna babban yabo ga takwarorinsu na kasar Sin da suke aiki tare. Moliu Jape, wani likita daga tsibirin Zanzibar na kasar Tanzania ya sifanta abokin aikinsa na kasar Sin kamar haka¡°Likitocin kasar Sin na da kirki sosai kuma aiki tukuru, ko kusa ba su san gajiya ba, sun koya mana abubuwa da yawa. Dukkansu gwanaye ne. Dukkanmu da likitoci na sauran kasashe muna ganin cewa, suna da nagartacciyar fasahar likitanci. Yanzu kungiyar kiwon lafiya ta kasar Sin da mu mun zama iyali da abokai, muna fatan za mu iya zurfafa irin wannan kauna da abokantaka.¡±

A duk lokacin da wa¡¯adin aikin kungiyoyin kiwon lafiya na kasar Sin zai cika, kuma za su koma kasar Sin, mazauna wurin su kan shirya kasaitaccen bikin yin ban kwana domin nuna musu godiya, haka kuma, suna tambayarsu lokacin da za su dawo garinsu. Wei Zhenli, wani likita ne daga jihar kabilar Zhuang ta Guangxi mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ya taba aiki a kasar Nijer har tsawon shekaru 4 ko fiye ya gaya mana cikin sahihanci cewar,¡°A zahiri, na yi aiki a asibiti na kasar Nijer har tsawon shekaru 2 da rabi. Na mayar da abokan aikina na Afirka kamar ¡®yan uwana, shi ya sa ban da wasu 2 da suke aiki a asibitin, dukkan abokan aikina 5 da muke aiki tare a sashen kula da cututtukan cikin jikin dan Adam sun yi ban kwana da ni a filin jirgin sama, mu dauki wani hoto, inda ni ne kawai nake murmushi, sauran kuwa sun yi kuka, ba su so in bar su.¡±

A sakamakon ayyukan kiwon lafiya na shekara da shekaru, nagartacciyar fasahar likitocin kasar Sin da kuma kirkinsu sun sami amincewa sosai daga gwamnatocin Afirka da kuma jama¡¯ar Afirka. Mazauna Afirka su kan nuna godiya ga wadannan likitocin kasar Sin da ke ba su hidimar kiwon lafiya ba tare da neman samun kome ba.

Wata mace ta gaya mana cewa,¡°Dukkan likitocin kasar Sin na da kyau sosai. Mu majiyyata mun san aikin tukuru da suke yi, su duba lafiyarmu, su kawo mana magani, su taimake mu sosai. Mun gode musu kwarai da gaske!¡±

A zahiri, ba da hidimar kiwon lafiya a Afirka ba kawai ya iya kawo wa kasashe da jama¡¯ar Afirka alheri ba, haka kuma, ya iya kawo wa mambobin kungiyoyin kiwon lafiya na kasar Sin alheri. Mr. Wang Liji ya gaya mana cewa,¡°Ko da yake Afirka na baya-baya a fannonin sharuddan kiwon lafiya, amma jama¡¯ar Afirka na da matukar kirki, suna da saukin kai, suna girmama likita kwarai da gaske. Irin wannan kyakkyawar hulda a tsakanin likita da majiyyaci ya karfafa aniyar likitocinmu na kasar Sin. Likitoci da yawa da suka dawo kasar Sin daga Afirka sun gaya mini cewa, sun san makasudinsu na rayukansu, su ji alfahari sosai a matsayin likita.¡±
Baya ga kungiyoyin kiwon lafiya da ke aiki a Afirka, bayan da kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje, Sin da Afirka sun habaka fannonin yin hadin gwiwa ta fuskar kiwon lafiya. A shekarar 1987, Sin da Tanzania sun daddale yarjejeniyar yin hadin gwiwa kan yaki da cutar kanjamau ta hanyar amfani da magungunan gargajiya na kasar Sin. A cikin shekaru 20 ko fiye da suka wuce, masana masu ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin sun ba da magani ga masu fama da cutar kanjamau da kuma yi musu jiyya ba tare da samun kudi ba, ta haka, Afirka, wadda ke shan wahalar cutar kanjamau, ta sake samun sabon karfi.
Mr. Wang Liji ya gaya mana cewa,¡°Na san cewa, an sami sakamako mai kyau a fannin warkar da masu fama da cutar kanjamau ta hanyar amfani da magungunan gargajiya na kasar Sin a Tanzania, yanzu ana gudanar da wannan yarjejeniya yadda ya kamata. Idan wata rana an sami hakikanan sakamako kan shawo kan cutar kanjamau ta hanyar amfani da magungunan gargajiya na kasar Sin, to, wannan zai zama babbar gudummowa ga dukkan ¡®yan Adam.¡±

Gwamnatin Sin tana ba da hidimar kiwon lafiya a Afirka, tana kokarin fitar da jama¡¯ar Afirka daga cututtuka, a shekarun baya, gwamnatin Sin ta mai da hankali kan yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannin kyautata albarkatun kwadago ta fuskar kiwon lafiya, tana taimakawa kasashen Afirka su inganta karfinsu. Baya ga ci gaba da bayar da aikin horaswa a fannonin likitancin gargajiya na kasar Sin da kuma yaki da cutar zazzabin cizon sauro, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci kan shirya aikin horaswa a fannonin kula da harkokin kiwon lafiya da saukakka cututtuka masu yaduwa da kuma fasahar yin bincike.
Mr. Wang Liji ya yi karin bayani cewa,¡°Alal misali, a shekarar 2008 da muke ciki, hukumomin tsarin kiwon lafiya na kasar Sin mun shirya kos-kos sau 12, inda mutane 30 zuwa 50 suka iya samun aikin horaswa a ko wane karo. Ta haka, mun iya horar da mutane kimanin dubu 1 da dari 5 a ko wace shekara. Wadannan mutane sun zo ne daga kasashen Afirka da kuma na Asiya, wato dukkansu sun zo ne daga kasashe masu tasowa.¡±

Bayan da muka shiga karni na 21, musamman ma bayan da aka yi taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2006 a nan Beijing, gwamnatin Sin ta tabbatar da manufar kara mara wa kasashen duniya baya daga dukkan fannoni.

A gun taron koli na Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sanar da manufofi 8 na sa kaimi kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka daga fannoni daban daban, ciki har da kafa asibitoci 30 a Afirka da ba da taimakon kudi da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan 300 domin taimakawa Afirka wajen yaki da cutar zazzabin cizon sauro, za ta bayar da maganin sinadarin Arteannuin da kuma kafa cibiyoyi 30 na yaki da zazzabin cizon sauro.

Game da wadannan asibitoci 30 da ake nan ana ginawa, Mr. Wang ya yi bayanin cewa, ¡°Dalilin da ya sa gwamnatin Sin ta kafa wadannan asibitoci 30 a Afirka shi ne domin kasashen duniya suna matukar bukata. Gwamnatin Sin tana fatan wadannan asibitoci 30 za su iya ba da taimako wajen raya ayyukan kiwon lafiya na wadannan kasashe.¡±

Dadin dadawa kuma, Mr. Wang ya yi mana karin bayani kan manufar da Sin da Afirka za su bi wajen yin hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya. Ya ce,¡°Nan gaba za mu ci gaba da ba da tallafi bisa bukatun kasashe masu tasowa. Kasar Sin na samun bunkasutwar tattalin arziki, haka kuma, kasashe masu tasowa, shi ya sa watakila za su fito da sabbin bukatu a sakamakon bunkasuwar tattalin arziki da zaman al¡¯ummar kasa. Ta haka, za mu kyautata hanyoyi da tsare-tsaren kungiyoyin kiwon lafiya da za su tura zuwa Afirka bisa bunkasuwar Afirka da kuma bukatunsu. Makasudinmu shi ne ba da hidimar jiyya ta zamani mai inganci ga jama¡¯ar Afirka.¡±

  Babi na biyar:   Kai Sama
Cigaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru 30 da suka gabata a fannonin tufafi

Kande: Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanmu da saduwa ta wani shirin musamman da muka tsara kan ci gaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru 30 da suka gabata a fannonin tufafi da abinci da gidajen kwana da kuma zirga-zirga bisa gyare-gyaren da ta yi a gida, da kuma bude kofa ga kasashen waje. Ni ne Bello Wang tare da abokiyar aikina, Kande Gao muke gabatar muku da wannan shiri.

Bello: A farkon shekaru 70 na karnin da ya wuce, jama'ar kasar Sin su kan sa tuffafi masu launukan kore, da shudi, da baki, da toka-toka, kuma masu siga iri daya. Sinawa ba su san kalmar "Sabon yayi" ko kadan ba.

Kande: A wancan lokaci kuma, Sinawa ba su san mene ne "tuffafin kawa" ba, balle ma yaya za a zabi tuffafi masu launuka daban daban da suka dace ba.

Bello: Amma, a shekarar 1979, wato shekara ta biyu da aka soma gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, shahararren mai zanen tuffafi na kasar Faransa Pierre Cardin ya iso nan kasar Sin tare da tuffafinsa na kawa. Domin nuna alamarsa, Mr. Pierre Cardin ya zabi wata sakatariyar da ke aiki a ofishinsa da ta sa tuffafin da ya zana.

"Na ga wata kyakkyawar sakatariya, ko da ya ke ba ta da tsayi, amma tana da kiba kadan. Bayan da sakatariyar ta tube rigarta ta waje, na yi mamaki sosai, saboda tana sanye da tuffafi masu launika iri daban daban har guda 8."

Kande: Bayan da wannan sakatariya ta sa tuffafin da Mr. Cardin ya zana, dukkan mutanen da ke wurin sun nuna mamaki sosai kan kyawunta.

Bello: Bayan da aka shiga shekaru 80 na karni na 19, iskar "Sabon yayi" ta shiga ra'ayin jama'ar kasar Sin bisa kara gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. A cikin gajeren lokaci wasu tuffafi da kayayyakin ado, ciki har da tuffafi irin na Turawa, da rigar mata, da kuma tabarau, da dai sauransu. Suka samu karbuwa, Nan da nan Sinawa daga tsoffi da yara, maza ko mata dukkansu suka fara sanya tuffafi masu siga iri daya.

Kande: Wannan ya nuna cewa, kasar Sin na bude kofa ga kasashen waje, amma a waje daya kuma, ana iya ganin cewa, ba ta bude sosai ba, haka kuma, a hakika dai ra'ayin "Sabon yayi" bai gama shiga tunanin jama'a sosai ba. A shekarar 1984, Mr. Pierre Cardin ya yi nune-nunen tuffafi a birnin Beijing, wannan ne kuma karo na farko da aka shirya nune-nunen tuffafi masu alamomin kasashen waje a tarihin kasar Sin. Madam Zheng Siti, wadda take da alaka da Mr. Pierre Cardin ta yi waiwaye da cewa, "Ni daya ce daga cikin 'yan matan zamani a karo na farko da aka zaba a lokacin nune-nunen tuffafi da Mr. Cardin ya yi a kasar Sin. A lokacin, ba a bude kofa sosai a kasar Sin ba, saboda haka, mutane kadan ne suka san hanyar nune-nunen tuffafi."

Bello: Wannan nune-nunen tuffafi mai babban take na "Sabon yayi" da "Tuffafin kawa" ya jawo hankulan mutane sosai, har ma dakin motsa jiki da ke iya daukar mutane fiye da dubu goma ya cika da masu kallon nune-nunen.

Kande: Idan ana iya cewa, alamar "Pierre Cardin" ta gabatar da ra'ayi na "Sabon yayi" da "Tuffafin kawa" ga Sinawa, to haka kuma ana iya cewa, mujallar ELLE ta karfafa alaka a tsakanin "Sabon yayi" da tattalin arziki da zaman rayuwar Sinawa.

Bello: A shekarar 1988, mujallar ELLE ta iso nan kasar Sin bisa matsayinta na mujallar sabon yayi ta farko da ta shigo kasar Sin. Madam Yi Yan, wadda ta taba zaman shugabar kula da adabi ta mujallar ELLE ta waiwayi cewa, kasar Sin da ke lokacin wata kakar "Sabon yayi" ce, a wancan halin da ake ciki, mujallar "ELLE" na taka muhimmiyar rawa a duk yunkurin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin.

Kande: Saboda tuffafin da ake nunawa a cikin mujallar sun nuna sigar musamman ta kasar, don haka, cikin sauri mujallar "ELLE" ta zama abin koyi ga Sinawa wajen zaben tuffafin da suka dace a lokacin . Madam Yi Yan ta ce, "Ana iya ganin mujallar 'ELLE' a dukkan kasuwanni. A lokacin da Sinawa ke dinka tuffafi su kan zabi sigar da ake nunawa a cikin mujallar 'ELLE'. Mujallar ta zama wata hanyar jagoranci ga matasa don zaben sabon yayi, da kyan gani."

Bello: Bayan da aka shiga shekaru 90 na karni na 20, kasar Sin ta kara bude kofarta bisa kara gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje. Bisa karuwar matsayin zaman rayuwar jama'a, fararen hula na kasar Sin su kan ta fi neman sabon yayi, haka kuma tuffafi masu sabon salo da sigar musamman suna ta kara samun karbuwa a kasar.

Kande: Ba kawai canzawar tuffafi da Sinawa suka samu ta nuna manyan sauye sauyen da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ke kawowa ga tattalin arziki na kasar Sin ba, har ma ta nuna sauyawar ra'ayi na Sinnawa, da kuma karuwar matsayin wayin kai.

Bello: Bayan da aka shiga sabon karni, bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin na jawo hankalin duniya sakamakon yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Daya bayan daya tuffafi daga kasashen waje, da kuma tuffafin gayu sun shiga kasuwar kasar Sin, har ma ana iya samun kantunan musamman masu alamomi daban daban a cibiyoyin da ke birane, haka kuma aka kusantar tuffafi masu shahara na kawa a duniya. Tun daga lokacin kuma, Sinnawa sun soma sanin Versace, da Louis Vuitton, da Burberry, da kuma sauran shahararrun masu tsara tuffafi da kyawawan alamomi.

Kande: Ta wadannan alamomi, Sinawa sun fahimta da cewa, tuffafin ba kawai ana sawa don kiyaye jiki ne ba, har ma sun yi fice ta fannin tattalin arziki, da tarihi, da wayin kai, da kuma fasaha. Dukkan fahimtar da aka samu na da nasaba da shigar kasuwar kasar Sin da mujalloli irin na sabon yayi da duniya suka yi daya bayan daya. A shekarar 2001, mujallar BAZAAR, wadda ta fi shahara a kasar Amurka ta iso nan kasar Sin, kuma ta yi hadin gwiwa da kamfanin ELLE don fitar da mujallar BARZAAR. Tsohon mai kula da adabi na mujallar "BARZAAR" Mr. Hao Ning ya ce, "A hakika dai, kasar Sin ta samu farfadowa bayan shekaru 90 na karnin da ya wuce, daga shekarar 1997 zuwa shekarar 1998 kuma, ta kai wani sabon matsayi. A wancan lokaci, kasar Sin na bakin kofar shiga kungiyar ciniki ta duniya WTO, saboda haka ne, wasu abubuwan da ke da halin musamman na kasar Sin da na duniya suka bullo. Kamfanin "ELLE" ya fahimci wannan halin da ake ciki, kuma ya shigar da mujallar "BARZAAR" da ta fi samun nasara a tarihin kasar Amurka."

Bello: Ta wata hanyar musamman ce tuffafi na nuni da sauyawar tsarin siyasa, da tattalin arziki, da kuma al'adu na zaman al'umma. Tuffafi kuma wata muhimmiyar alama ta canjawar zamani, suna nuna cigaban zaman al'umma.

Kande: Tun yayin da nau'in "Pierre Cardin" ya shigar da "Sabon yayi" da "Tuffafin kawa" cikin kasar Sin a karshen shekaru 70 na karnin da ya wuce, da kuma yadda mujallar "ELLE" ta soma kawo tasiri kai tsaye ga tuffafin da Sinawa ke sanyawa a shekaru 80 na karnin da ya wuce, har zuwa lokacin hada kan ra'ayin "Sabon yayi" na Sinawa da na duniya a cikin sabon karni, lallai ana iya cewa, nan da shekaru 30 da aka soma yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, tuffafi sun zama wata tagar da ke gabatar da kasar Sin ga duniya, da kuma taimakawa duniya ta fahimci kasar Sin.

 
  Babi na shida:   Kai Sama
Bunkasuwar abinci na jama'ar kasar Sin cikin shekaru 30 da suka wuce

[Bello]: Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanmu da saduwa ta wani shirin musamman da muka tsara kan ci gaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru 30 da suka gabata a fannonin tufafi da abinci da gidajen kwana da kuma zirga-zirga bisa gyare-gyaren da ta yi a gida, da kuma bude kofa ga kasashen waje. Ni ne Bello Wang tare da abokiyar aikina, Kande Gao muke gabatar muku da wannan shiri.

[Kande]: Masu sauraro, assalamu alaikum, abinci na da muhimmanci gaban kome, ko a da ko kuma yanzu, mutane na sa lura sosai a kan abincin da suke ci.

[Bello]: Lalle, Kande, gaskiyarki! Amma, shin ki sani, a cikin shekarun 30 da suka wuce, sabo da yanayin talauci, mutane da dama ba za su iya samun isassun abinci ba?

[Kande]: I, Malam Bello, wannan sai ka tambaya? Yayin da muke kananan yara, ba wai kamar haka mu kan ji, "A ci a sha a rage don gobe." Yanzu tare da juyawar zamani, "Abincin wani, ba na wani ba ne".

[Bello]:oho! malama Kande, kwarai kuwa, mutane na iya zaba dukkan abincin da suke so su ci, ba wai kamar yadda a da ba, mu kan ci kome da muke da su, lalle "Bayan wuya sai dadi".

[Kande]: To masu saurarommu, a cikin shirimmu na yau, za mu gabatar muku canje-canjen da muka samu a fannin abinci a iyalin Inna Li a shekarun 30 da suka gabata.

[Bello]: Inna Li, 'yar asalin Beijing, mai shekaru 50 da haihuwa, tana son baki kwarai, yayin da muka shiga gidanta, sai ta dauki wani katin sayen abincinta daga akwatin tebur, ta fada mana cewa, wannan kamar dukiyarta ce.

Wannan shi ne katin sayen hatsi, wannan kuma katin sayen man girki, wannan kuwa katin sayen hatsi da ake iya amfani da shi a duk fadin kasar Sin.

[Kande]Da aka tabo maganar katin sayen abinci, matasa da yawa za su shiga cikin rudani, amma a zukatan tsoffafin mutane, ba za su iya mantawa da wannan tarihi ba har abada.

Galiban Sinawa na son katin sayen hatsi da ake iya amfani da shi a duk fadin kasar, sabo da ana iya amfani da shi a ko ina a kasar. Wasunsu da ake bayarwa gare mu a zaman yau da kullum su ne katin sayen hatsi da ake iya amfani da su a Beijing kawai. Sa'an nan kuma, ga wadannan katuna, launukansu sun sha bamban da juna. Dalilin da ya sa haka shi ne domin launukan katunan sayen hatsi kan sha bamban da juna a ko wane wata, ta haka ake iya gano watannin da aka bayar da wadannan katuna.

[Bello]:I, na tuna fa, an yi amfani da katin sayen abinci tun daga shekarar 1955 har zuwa shekarar 1993 a kasar Sin, a wancan lokaci duk abubuwan da kake so ka saya, ya kamata ka saye su ta hanyar yin amfani da kati, mutane na zama kamar "Na hannu baka hannu kwarya."

A wancan lokaci, do da yake muna da kudi, amma babu abubuwan babu abubuwan da za A kantuna, ana sayar da waina, amma in ba ka da katin sayen hatsi, to, shi ke1 nan, Iyayena sun saya mini wasu a wasu lokuta, amma akwai sharadi, a ko wane wata, aniya sayen wasu kadan. Sa'an nan kuma, ba ma iya sayen waina sai muna da isasshen abinci.

[Kande]: Haba! mutane na zama cikin matsananciyar yunwa, "A albarkacin sauyawar lokaci kamar farkon yanayin hunturu, sai mu kan je sayen kabeji don adana su don maganin yunwa a lokacin sanyi. Ban da kabeji, a wasu wurare da dama a arewacin kasar Sin, mutane su kan adana dankalin Turawa da karas da kabewa don maganin yunwa a lokacin sanyi."

[Bello]: Inna Li ta gaya mana cewa, "Ga wannan kabejin da na saya jiya, sabo da yanzu, za mu iya samun isasshen abinci a ko yaushe, da haka ba za mu bukatar adana kabeji kamar yadda muka yi a da ba."

Da sassade mutane cikin tufafi maganin sanyi suka fara jira a cikin layi. Bayan da manyan motocin daukar kabeji suka iso, masu sayar da kabejin suna share fage, sai bayan da suka gama, suke fara sayar da kabejin, amma a wancan lokaci, mutane sun shan sanyi kwarai da gaske. Ban da wannan kuma, an raba kabejin zuwa kashi 3, an kayyade yawan kabeji na aji na farko da na biyu da ko wane mutum yake iya saya. Sabu adadin da aka kayyade ga na aji na uku.

[Kande]: Halin da ake ciki wajen adanan kabeji ya sami kyautatuwa a kai a kai, , mutane na iya samun kaji da agwagwa da kifi da jata lalle da kaguwa da rago da shanu da kayan lambu a kasuwanni.

[Bello]: Ba ma kawai mutane na iya samun wadatattun abinci ba, hatta ma a karshen shekarun 1980, bayan da abinci na kasashen waje suka shigo kasar Sin, zaman rayuwar Sinawa ya canja sosai.

[Kande]: A ranar 12 ga watan Nuwamba na shekarar 1987, a wani wurin da ke kusa da QianMen, an bude wani wurin cin abinci na "KFC" a Turance.

[Bello]: Ana sayar da wannan kaji da kudin Sin Yuan 2.5, amma ga shi a wancan lokaci a kasar Sin, wannan kamar abincin marmari ne, sabo da albashin ma'aikaci da shehu malami bai wuce Yuan 60 ko 70 ba, amma duk da haka, mutane na yin rige-rigen sayen abinci, haka kuma 'yan sanda sun fito fili don kiyaye zaman oda da doka a wurin.

[Kande]: Koukou ita ce 'yar Inna Li, mai shekaru 26 da haihuwa, ya zuwa yanzu, ita ma, za ta iya tunawa da halin da ake cikin, yayin da ta je cin abinci a KFC.

A wancan lokaci, akwai mutane da yawa da ke jira a wannan wuri. A ganina, naman kaji da ake sayarwa a katin cin abinci na KFC yana da mamaki, ya sha bamban da abubuwan da na kan ci. A zahiri, ba na son irin wannan dandano, wanda ya sha bamban da yadda nake tunani.

[Bello]: A wancan lokaci, mutanen da suke sayen abinci a wannan KFC sun iya sayi-nan-ci-gida, amma ba wanda yake son ya ci a gida, dukkansu sun ci abinci a cikin gidan abinci, don jin yanayin da ke da banbanci da na gidan abinci na kasar Sin. Kou Kou dake da shekaru 6 da haihuwa ya taba bayyana fatansa a lokacin da yake cin abinci a KFC a karo na farko.

[Kande]: To, a cikin kasuwar sayar da kayan lambu na kasar Sin a shekaru 90 na karnin da ya gabata, ka iya saye duk kayayyakin da suka so, kamarsu kayan lambu, 'ya'yan itatuwa, kwal, kaji, nama, kifi da sauransu. Kuma an iya sayen shinkafa a lokacin da ake bukata, ban da wannan kuma, farar hula sun iya cin 'ya'yan itatuwa da abincin teku a lokacin da suke so. Tun daga wancan lokaci, mutane sun fara mai da hankali kan ko abinci yana da dadinci sosai. Yawan abinci ba na hatsi ba ya rage, kuma yawan shinkafa ya karu. Kifaye, nama, kaji, jatan lande da dai sauransu su kan zama abincin farar hula. Ana iya cin abinci iri daban daban, kuma zaman rayuwa ya yi kyau.

[Bello]: I, kamar yadda kuka sani, sabo da matsayin zaman rayuwa ya inganta, kuma ana gaggauta yin ayyukan, hanyar cin abinci ta canja. Mutane da yawa suna son sayen abinci za su taru a gidajen abinci. A lokacin da ake murnar biki, iyaye da abokai a gidajen abinci, ko sayen abincin sayi-nan-ci-gida. Musamman a ranar bikin sabuwar shekara, da akwai mutane da yawa suka ci abinci a gidajen abinci iri daban daban, hatta ma a kan oda tebur kafin aka je. Bugu da kari, wasu mutane suka dauki kuku zuwa gidaje don shirya musu abinci, wannan ya rike da al'adar cin abinci a gida, da rage yawan kudin da za a kashe, kuma ba za su dafa abinci da kansu ba.

A sakamakon bunkasuwar zaman al'ummar kasa, kowa da kowa na amincewa da cin abinci a gidajen abinci a jajibirin bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. A duk lokacin bukukuwa da salla, mutane su kan ci abinci a gidajen abinci, ta haka dukkan mambobin iyali suna iya hira tare, bayan cin abinci, suna yin Allah-Allah kan cin abinci tare a nan gaba. Amma a da, in an ci abinci a gida, a jajibirin bikin bazara, wasu suna yin hira, wasu dafa abinci, ba a iya ganin duk iyali son hadu dan yin hira tare.

[Kande]: Har zuwa karshen shekaru 90 na karnin da ya gabata, da akwai gidajen abinci na kasashen daban daban da yawa a kasar Sin. An kafa gidajen abinci na Faransa, da Rasha, da Japan, da Korea ta Kudu, da Thailand, da kuma Arabia da dai sauransu a kasar Sin. A lokacin nan a kasar Sin, ana iya ganin gidajen abinci iri daban daban a kowane wuri. Kuma za a iya cin abinci musamman na wurare daban daban na Sin da na kasashen waje a kusa da gida.

[Bello]: Amma, kowa ya sani, sannu a hankai, a sakamakon cin nama da yawa, mutane da dama suna kamuwa da cututuka, kamarsu CDC, ciwon sukari da sauransu. Sabo da haka, an soma canja hanyar cin abinci.

[Kande]: Madalla. Bayan shiga sabon karnin da muke ciki, farar hula na kasar Sin sun fara neman lafiya, a kasuwa, mutane suna mai da hankali kan danyun kayayyaki, amma ba su mai da hankali kan farashi ba. Su kan zabi abinci da ke kawo tasiri mai kyau ga lafiya. A takaice dai, abubuwan da mutane suke hira shi ne wane irin abinci zai iya kawo lafiya ga mutane.

[Bello]: Yanzu, a cikin babban kanti, ana sayar da naman sa na iri daban daban, kuma da akwai kayayyakin madara iri daban daban. Abinci masu kyau ga lafiyar mutane suna jawo hankulan jama'a. A zaman uwar gida, inna Li tana shan wahala wajen biyan bukatun dukkan iyayenta.

A sakamakon kyautatuwar zaman rayuwar jama'a, mutane sun fara mai da hankali kan cin abubuwa masu gina jiki ta hanyar kimiyya. A da, muna cin abinci ne domin koshi kawai. Amma yanzu kowa da kowa na neman kyautata zaman rayuwa yadda ya kamata.

"Yanzu, dole ne a ci kayayyakin lambu masu rashin abin damuwa, kuma a ci shinkafa na shekarar da ake ciki. Jama'a suna mai da hankali ga ingancin abinci, amma ba farashi ba."

[Kande]: To, Kou Kou tana sayen wani littafin dake shafar abinci da lafiya ga uwarta.

Ina son mahaifiyata ta iya fahimtar ilmin zamani kan cin abinci ta hanyar kimiyya, ta haka za ta iya samar da abinci mai dadi tare da kiyaye lafiyarmu.

[Bello]: To, jama'a masu sauraro. Tun daga lokacin shan wuya wajen cin abinci, zuwa yayin da aka sayen abinci tare da tikit, daga lokacin dake da kwando dake ba kome a ciki zuwa yayin da aka iya ci duk abin da ake so, zaman rayuwar farar hula ya canja sosai. A cikin shekaru 30 da aka fara aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa a kasar, hanyar cin abinci ta Sin ta shaida bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Zaman rayuwa na birane da na kauyuka ya kyautata da yawa.

  Babi na bakwai: Kai Sama
Bunkasuwar gidajen kwana na jama'ar kasar Sin cikin shekaru 30 da suka wuce

Tun daga shekarar 1978 zuwa shekarar 2008, wato a cikin shekaru 30 da suka wuce yayin da kasar Sin ke gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje, gidajen kwana na jama'ar kasar Sin sun samu kyautayuwa kwarai da gaske: daga kananan wuraren zama zuwa masu girma, daga zamanin zaman tare zuwa kowa yana da gidan kwana. A cikin gidajen kwana, labarai iri iri na iyalai daban daban sun faru, kuma sun yi bayani kan hanyar bunkasuwa da ke bayyana halin musamman na kasar Sin. A cikin shirinmu na musamman na yau, za mu gabatar da muka labarin iyalin Mr. Jin Yujun, ta haka domin yin bayani kan bunkasuwar gidajen kwana na jama'ar kasar Sin.

"A cikin wannan daki mai fadin muraba'in mita biyu, akwai dakunan dafa abinci ciki cunkus, hanya ta kan cunkus, dukkan iyali, kaka, da baba, suna zaune tare, ko iyalai biyu wato mutane 4 suna zaune tare. Ana son kyautata sharadin gidan kwana kwarai. Mutane 8 na iyalin Mr. Wang Lizeng wanda ya yi ritaya daga aiki suna zaune cikin wani daki mai fadin muraba'in mita 13, yana son samun wani sabon gidan kwana kwarai."

Wannan shi ne wani babi da ke cikin wani fim mai suna "muna son dubban gidajen kwana" da kasar Sin ta yi a shekarar 1982, yanayin da ke cikin wannan fim ya bayyana halayen da gidajen kwana suke ciki a wancan zamani, wato, "karami, mai sauki, tsoho, cike cunkus".

Shekarar 1978 shekara ce ta farko da aka fara gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje, kafin wannan kuma, ana gudanar da tunanin "yin aiki da farko, kana jin dadi daga baya.", ba a kula da bukatun zaman rayuwar jama'a sosai ba, kuma gwamnati tana ba da kudi kan ayyukan kawo albarka, ba ta da cikakken kudi domin gina gidajen kwana masu yawa. A wancan zamani, yawancin mutanen kasar Sin suna yin bayani kan gidajen kwana da wata kalma guda daya kawai, wato "matsala".

Madam Tan, wata nas mai jiyyar mutane a cikin asibiti ita ma ta tuna tarihin gidanta. A shekarar 1981, ni da mijina mun yi aure, amma a lokacin ba mu samu wani gida ba tukuna. Shi ya sa mun shirya bikin aurenmu cikin wani gidan da muka yi aro daga 'yan uwa. Ko da yake gidan ba shi da girma, fadinsa mita 29 ne kawai, amma muna sonsa kwarai. Muna tsamanin cewa, idan muna da wani gida kamar haka, gaskiya ne, Allah ya yi mun sa'a ke nan. Mr. Jin Yujun wanda shekarunsa ya kai 63 da haihuwa, kafin ya yi ritaya, wani malami ne. cikin shekaru 80 na karni na 20, shi da matarsa, da yarinyarsa suna zaune cikin wani daki mai fadin muraba'in kusan mita 10 ne kawai."A wancan zamani, wurin zama ya yi kankanta sosai. Ban da wajen ajiye gado, da tebur, da akwatin tuffafi, ba sauran wuri ba. Idan wani lokaci akwai baki, dakin kan cunkushe. sosai."Daidai kamar yadda Mr. Jin ya ce, a wancan zamani, mutanen kasar Sin ba su son gayyatar abokai zuwa gidajensu, dalili na farko shi ne saboda bubu cikakken wurin zama, na biyu shi kuma babu kudi.

A wancan lokaci, iyalin Jin suna zaune cikin wani karamin daki, wannan daki yana cikin wata "babbar farfajiya" mai dakuna shiyya hudu" na kasar Sin a tsohon zamani, amma. A wancan lokaci, iyalai guda bakwai ko takwas suna zama tare cikin wannan "babbar farfajiya", ko wane iyali suna da wani daki, amma suna yin amfani da dakin dafa abinci, da ruwan sha, da bayan gida da dai sauransu bai daya.Che Lin, wata malama mai koyarwa a wata jami'ar da ke Beijing ta tuna a lokacin ba a samun ruwan famfo, sai dai an je bakin kogi dake dab da gidansu don wanke shikafa ko tufafi. Ko kuma an je wajen wata rijiya an debi ruwa, sa'an nan an ajiye ruwan a cikin wani babban tanki a gida, an zuba garin magani a cikin ruwan don tsabtace shi.

A lokacin, ko babban iyali da ke kunshe da kakanni da iyayen yara da yara, ba su da babban gida, sai dai wasu kananan dakuna 2 da suke zaune tare a ciki. Shi ya sa, ba yadda zai yi a kasa gida kashi daban daban bisa yin amfani da shi, dakin shakatawa shi ma ana dafa abinci da cin abinci a ciki, dakin kwana shi ma ana karatu a ciki, iyaye da yara suna kwana a cikin daki daya. Ban da Da-Za-Yuan, Tong-Zi-Lou shi ma wurin zama ne na jama'ar Sin a lokacin. Cikin mawuyacin hali na rashin isashen gidajen zama, wasu kamfanonin sun fara mayar da wasu ofisoshi kan matsayin wuraren zama na ma'aikata, don sassauta tsananin bukatun da ake wa gidajen zaune. Wadannan gidajen wucin gadi ana kiransu 'Tong-Zi-Lou' , sunan na nufin siffar wurin zama kamar wata tsawon hanya ta hada dakuna da yawa tare. A wurare daban daban a kan samu 'Tong-Zi-Lou' mai salon iri daya, wato ya kasance da wata hanya a tsakiya, sa'an nan ana samun gidajen zama a jere, wadanda ake samunsu ta hanyar yin kwaskwarima kan dakunan ofis, a duk gyaffa 2 na hanyar.

Bisa hanyar mai matsatsi da ke tsakanin dakuna, a kan ajiye kayayyakin da ba safai a kan yi amfani da su ba, haka kuma ana dafa abinci a kan hanyar domin a kan ajiye kuka da kayayyakin da ake amfani da su don dafa abinci a can. Yayin da ake zama a cikin Tong-Zi-Lou, ba wanda ke iya kebancewa daga sauran mutane, kome abun ana yinsa ne bisa sa ido na saura, shi ya sa a kan samu sabani a tsakanin mazaunen wurin. Shu Kexin, wata mai nazarin harkokin jama'a ta kasar Sin, ta ce, 'wane abinci kake dafawa a gida, ko yau ma kuna cin Jiao-zi a gida, kwal nawa ka sayo gidanka, duk wadannan abubuwa makwabtanka za su sani. Domin za a ajiye kome da kome cikin hanyar da ke tsakanin dakuna. So, a hakika, a lokacin can, ba wanda ke iya boye wani sirri. 'Lokacin da kasar Sin ta fara bude kofa ga kasahen duniya da kuma yin kwaskwarima a gida, yawan jama'ar da ke zama cikin biranen kasar ya karu da sauri, amma yawan kudin da gwamnatin kasar ta zuba wa harkar gina gidaje bai kai kashi 1% na jimlar kudin kayayyakin da ake samarwa a kasar ba.

Shi ya sa a lokacin, abin da ake yi shi ne jiran kamfanoni da su rarraba wa ma'aikatansu wurarren zaune, wato matakin da aka dauka mai lakabin 'rarraba gidaje don jin dadin jama'a'.Malama Che Lin ta ce a lokacin, wato daga shekarar 1978 zuwa ta 1988, ita ma ta shiga cikin wani gidan da kamfanin da iyayenta ke aiki ya ba su don su zauna a ciki. a lokacin mun fara samun wani dakin shakatawa da wani dakin dafe-dafe, da sauran dakuna 2. Amma babu dakin bayangida a ciki, sai dai mutane da yawa na unguwar suna yin amfani da bayan gida daya. A shekarar 1988, iyayenta sun sake kaura zuwa wani sabon gida, inda aka samu dakunan kwana 3, da kuma baranda 2, inda ake dasa furanni da ciyawa ko kuma shanya tufafi. Gidan ya kasance a cikin wani gini mai benaye, shi ya sa mutane suna iya kulle kofa su zauna su kadai, ba kamar a da ba, yayin da suka yi amfani da bayangida daya da dakin dafe-dafe daya, ba wanda ke iya boye sirrinsa. Bayan da suka shiga cikin gini mai benaye, sun samu jin saukin zama da kwaciyar hankali.

Bayan Malama Che Lin ta shiga cikin jami'a don karatu, ta bar gidan iyayenta, ta kaura zuwa cikin gidan dalibai na jami'ar. Da ta gama kararu a shekarar 1993, ta samu aikin koyarwa a cikin jami'ar. Sa'an nan jami'ar ta ba ta wani dakin da fadinsa ya kai muraba'in mita 12 don ita da wata abokiyar aikinta su zauna a ciki, salon dakin ya yi kama da gidan 'Tong Zi Lou' da muka ambata, wato yana tare da sauran dakuna da yawa, inda mutane masu zama a ciki suka yi amfani da wasu dakunan bayangida da wurin wanke-wanke tare. A hakika an fara amfani da gidan Tong Zi Lou a shekarun 1950, amma har zuwa shekarun 1990 ana amfani da shi. Malama Che Lin ta ce, da yawa daga cikin malamai masu koyar mata ilimi, su ma sun yi zama a cikin Tong Zi Lou, har ma yayin da suka yi aure suka haihu ba su samu sabbin gidaje ba.Madam Tan ba ta samu mallakar gida ba, sai a shekarar 1984 kamfanin mijinta ya ba su wani karamin gidan da fadinsa mita 10 ne kawai da wani abu. sabo da kankantar gidan, ko kayan gida ma da kyar aka sa su ciki.

Wasu kayayyakin har mun ajiye su a wurin aiki, domin ba mu iya samun sauran wuri don ajiye su ba. Gidan da suka samu wani tsohon gida ne, inda akwai iska mai danshi a ciki. Da Madam Tan ta shiga gidan, ta zauna, ta fara jin ciwon jiki. Haka ya sa, a shekarar 1986 sun samu damar kaura zuwa wani gida na daban bisa kokarin da suka yi. Gidan na cikin wani gini mai benaye 2, kuma ya kasance da gidaje 15 a bene daya. Kowane gidan na da dakuna 3 da kicin daya, amma ba su da dakin bayan gida. Ban da wannan kuma, gidan yana da nisa sosai zuwa wurin aiki. Duk da haka, iyalin Madam Tan sun yi kaunar gidan sosai, domin yana da kyau, idan an kwatanta da shi da tsohon gidan da suka taba zama a ciki.Yanzu bari mu koma gidan Mista Jin Yu Jun. Domin diyarsa tana kara girma, Mista Jin ya ji cewa, karamin dakin da iyalinsa suka zama a ciki bai iya ishe bukatunsu ba.'Da ta yi girma, muna jin cewa, kamata ya yi, a ba ta wani dakin inda ita kadai ke zama a ciki. A lokacin, mu kan ga gine-gine masu benaye kan hanyarmu zuwa wurin aiki, wannan ya sa mu samu burin cewa, wata rana watakila za mu samu damar kyautata halinmu a wajen zaune, yadda za mu kaura cikin wani gini mai benaye kamar wasu mutane suka yi. 'Jin Yu Jun da iyalinsa sun jira sun jira har shekaru da yawa sun wuce, daga baya a shekarar 1997, kamfanin Mista Jin ya ba shi wani sabon gida, wanda ke da dakuna kwana 2 da dakin shakatawa 1. Fadin gidan ya kai murabba'in mita 80, yana hawa na 8 a cikin wani gini mai benaye 18.

Bayan sun kaura zuwa sabon gida, Jin Di, karamar diyar Mista Jin ta fi jin murna.'Wannan karo na farko ne da na yi zaune a cikin gini mai benaye, zama a cikin gidan yana sha bamban da na da, da ka hau wuri mai tsayi, za ka iya hangen nesa. A karshe dai na samu dakin kaina, sa'an nan na samu wurin ajiye abubuwana.'Amma, mutanen da suka gamu da katari suka samu gidaje kamar Mista Jin da iyalinsa ba su da yawa. A lokacin can, kamfanonin ba su da isashen gidaje don su rarraba wa ma'aikata, shi ya sa, gida ya zama wani abu da kowa da kowa ke kokarin neman samu kuma su kan ci tura. Jin dadin zaman mutum ya zama dogara kan ko kamfaninsa zai ba shi gidan zama. Ba wani abu da za a iya yi, sai dai jira.aikin nan na rarraba gidaje, an yi shi ne bisa tsawon lokacin da ma'aikatan suka yi aiki a cikin kamfanin, in ji Malama Che Lin. Wato idan ka yi aiki a cikin kamfanin har shekaru da yawa, za a ba ka gida kafin a ba saura. Kuma kana da damar samu gida mafi girma, kuma wanda ke fuskantar kudu, yadda aka fi samun iska mai dumi a lokacin sanyi.

A lokacin, domin Malama Che Lin ba ta yi shekaru da yawa tana aikinta ba, shi ya sa ba ta wani dakin da aka samu bisa hanyar yin kwaskwarima kan gidajen Tong Zi Lou na da. Sai dai yanzu an gyara gidajen don suka dace da zaman iyali. Fadin gidan ya kai mita 28.Cikin gidan, ya kasance da wurin dafa abinci da dakin shakatawa da dakin bayangida. B

isa mukaminta a lokacin na wata malama da ta kama aikin koyarwa ba da dadewa ba, ta gamsu da gidan da ta samu. Amma gidan da aka ba ta, ba wai ita ce ke da ikon mallakarsa ba, a'a, jami'ar ce ke da wannan ikon, sai dai an ba ma'aikatan damar amfani da shi. Domin a lokacin, jama'ar kasar Sin ba su da ikon mallakar gidajensu, balle saye ko sayar da gidaje. Amma, bisa hawan mukamin mutum, bayan ya yi zama a cikin wani gida har na tsawon shekaru, a kan ba shi wani gida na daban da ya fi gidansa na da kyau. Don haka, kamfanin da mijin Malama Che Lin ke aiki ya ba shi wani gida mai dakuna kwana 2. Gidan ya fi gidansu na da kyau, amma a lokacin Malama Che Lin da mijinta suna shirya haihuwa, shi ya sa gidan bai isa biyan bukatunsu sosai ba. Domin suna bukatar dakin yara, da dakin baki, inda iyayensu za su iya zama a ciki. Amma, bisa manufar raba gidaje, za su jira shekaru da yawa don samu wani gidan da ya fi girma.Wannan halin da ake ciki an yi masa kwaskwarima a shekarar 1998.

A watan Yuli na shekarar , gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, za a daina matakin rarraba gidaje don jin dadin jama'a, kuma za a fara gyare-gyare kan manufar samar wa jama'a gidajen zama.'A karshen rabin shekarar bana za mu fitar da sabuwar manufa, wato za mu daina raba gidaje, maimakon haka za mu kafa kasuwannin gidaje, inda za a sayi da sayar da gidaye bisa 'yancin kai.'Sa'an nan an soke manufar raba gidaje, an fara sayar da gidaje a kasuwa. Ma'aikata za su iya yin amfani da kudin alawus da kamfaninsu ya ba su, da kuma samun rancen kudi daga banki don sayen gidajensu. Sabuwar manufar ta ba Sinawa damar zaba gidajen da suke so da kansu. Sannu a hankali an bar lokacin jin kunya da rashin boye sirrin kansa.Soke manufar ba da gidaje kyauta ya canza burin jama'a. Tare da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, matasa na sabon zamani sun fi dora muhimmanci kan kiyaye asirinsu. Ba su iya hakurin halin zama maras kyau ba, wato kamar iyali na wasu zuriyoyi suna zama tare da juna a cikin daki daya. Matasa sun fara yin kokari domin kyautata halin zama, kamar kara wurin zama da kara ingantar zamansu. Sabo da haka, sayen gida ta hanyar yin amfani da rancen kudi, wato cimma buri ta hanyar yin amfani da kudin nan gaba ya sami karbuwar matasa, kuma ya zama sabon salon zaman rayuwa da matasa suka saba da shi sannu a hankali.

Malama Che Lin ta ce, ta sayi wani gida a shekarar 2004, bisa kudin alawus da jami'arta ta ba ta, da rancen kudin da ta samu daga wajen banki. Sa'an nan sun ba da tsohon gidansu haya, ta yadda za su iya farke bashi. Kafin su sayi gidan, sun yi bincike kan gidajen da ake sayar da su a kasuwar Bejing sosai, sa'an nan sun zabi wani gidan da ya yi kusa da jami'ar Malama Che Lin, kuma fadin gidan ya fi mita 150 don haka ya dace da zaman iyali. Gidan na kunshe da dakuna kwana 3 da dakunan bayangida 2, kuma ya kasance da babban dakin shakatawa da na cin abinci. Malama Che Lin ta nuna yabo kan gyare-gyaren da aka yi wa manufar raba gidaje. Ta ce, a da mutane suna ta jira, har sai sun zama kakanni ba su samu wurin zama mai kyau ba. Amma, yanzu mutane sun samu damar sayen gidajen da suke so kafin su tsufa. A shekarar 1997, Madam Tan ita ma ta sayi wani gida na kanta.

Ita da mijinta tare suka zabi wannan gidan da ya yi kusa da asibitin da suke aiki a ciki, sa'an nan gidan ya yi kusa da makarantar da dansu ya ke karatu a ciki. Gidan na da dakunan kwana 3, kuma yana tare da dakin bayangida na kansa. A kewayen gidan, ana samun kasuwa da wurin shakatawa, wannan ya kawo sauki ga zaman mutum. Sayen gidan ya sa Madam Tan ta yi aron kudi. Amma, ba da dadewa ba, asibitin da take aiki a ciki ya ba ta wani gida, kuma ta biya asibitin kudi don ta samu ikon mallakar gidan. Domin gidan ya yi nisa zuwa asibitin, kuma ba shi da kyau kamar gidan da take zaune a ciki, shi ya sa ta sayar da gidan, ta mayar da kudin da ta yi aro. Jin Di, yar wani tsoho mai suna Jin Yujun, ta balaga tare da aikin gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima ta kasar Sin, kuma ta sadu da duk sauye-sauyen gidaje da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima ta kawo wa jama'ar Sin. Bayan ta fito daga jami'a, ta fara aiki a cikin wani kamfanin fasahar IT, ta sami kudin shiga cikin dorewa.

A shekarar 2004, ta sayi wani gida tare da masoyinta da rancen kudi. Ta ce,"Kudin da muka biya a karo na farko shi ne kudin ajiyar namu bayan 'yan shekarun da muka yi aiki, kuma 'yan uwanmu sun ba mu wasu kudin agaji, daga bisani, mun samu rancen kudi yuan dubu 300 daga banki, za mu biya wannan bashi cikin shekaru 20 a nan gaba. Sabo da ayyukanmu suna cikin dorewa, shi ya sa muna so mu biya rancen kudin sannu a hankali." Tun lokacin da gidaje suka zama muhimman kayayyakin cinikayya a cikin zaman jama'a, sha'anin hada-hadar cinikin gidaje ya kara bunkasuwa. A shekara ta 2007, sha'anin kafa gidaje ya riga ya kasance sha'ani mafi girma na hudu a kasar Sin. Yawan kudin da aka samu ta hanyar yin cinikayyar gidaje ya kai fiye da kashi 9 cikin kashi dari na GDP. Mutane da dama sun fara bukatar muhallin zama mai inganci. Amma sannan farashin gidaje ya kara hauhawa. A shekara ta 2007, farashin gidaje a birnin Beijing ya kai fiye da yuan 12000 a kowace muraba'in mita. Ba zato ba tsammani, gidajen da kowa ya bukata a cikin zaman yau da kullum sun zama kayayyaki masu daraja sosai.Jin Di ta gaya mana cewa, sabo da hauhawar farashin gidaje a birnin Beijing, abokan aikinta da yawa ba su iya biyan kudin gidaje yanzu ba. Ta ce,"Abokan aikina da yawa suna hayar gidaje suna zama a yanzu, sabo da farashin gida ya kai fiye da yuan miliyan daya. Shi ya sa ba za su sayi gidaje ba har sai farashin gidaje ya ragu."

Yin zama da kuma aiki cikin jin dadi shi buri ne na jama'ar kasar Sin cikin dogon lokaci, kuma matsala ce da gwamnatin kasar Sin ta fi neman daidaitawa a karkashin manufar rike ragamar mulki domin jama'a. A cikin shekarar bana, yawan kudin da aka zuba domin kafa gidajen ba da tabbaci a cikin kasar Sin ya kai fiye da yuan biliyan 100. A cikin shekaru 3 masu zuwa, gwamnatin tsakiya ta Sin za ta zuba jari yuan biliyan 900 wajen kafa gidajen haya da gidaje masu araha da kyautata yankunan gidajen rumfuna.Madam Tan ta ce, da ta tuna abin da ya faru a da, wato da farko ba ta da gida, daga baya ta samu gida mai mita 20 da wani abu, har zuwa yanzu ta samu gidan da fadinsa ya fi 100. Madam Tan ta yi kaura zuwa sabon gida har sau 6, kuma a ko wane karo ta kan samu gidan da ya fi na da. Shi ya sa tana farin ciki kwarai, kuma ta gamsu da irin wannan cigaba da suka samu a wajen zama.Yayin da muka waiwayi shekaru 30 da suka gabata na gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, murabba'in gidaje na kowane mutum na gari ya karu daga mita 6.7 a shekarar 1978 zuwa mita 26 a shekarar 2007. Yanzu Sinawa ba za su sifanta wurin zama a cikin tunaninsu da cewa wurin zamansu mai kunci ne ba. A kan hanyar cigaba, kome wahala, ba zai tsayar da yunkurin jamar kasar Sin na samun zaman rayuwa mafi dacewa ba har abada.

  Babi na takwas: Kai Sama
Sauyawar keke samfurin ¡°Yong Jiu¡± a cikin shekaru 30 da suka gabata

Shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 30 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin. A cikin shekaru 30 da suka gabata, hanyoyin da Sinawa suka bi wajen yin zirga-zirga sun samu manyan sauye-sauye, daga yin tafiya da kafafuwa zuwa hawan keke mai tayoyi biyu, daga tukin babur zuwa tukin mota, amma a karshe dai mutane sun koma zuwa hawan keke. Yayin da muke tabo wannan tarihi, akwai wata muhimmiyar kalmar Sinanci wadda ta burge Sinawa kwarai da gaske, kalmar nan ita ce "Yong Jiu", wato "Forever" cikin Turanci.

"Yong Jiu", wani samfuri ne na keke, wanda ya yi suna kwarai da gaske a kasar Sin a cikin shekaru 80 na karnin da ya gabata, wannan keke samfurin "Yong Jiu" yana da babbar ma'ana ga mutanen Sin da dama a wancan zamani. A lokacin, keke ya kasance wani muhimmin abun hawa ga jama'ar kasar Sin a zaman yau da kullum, wanda kuma Sinawa suka dauke shi kamar ma'auni ga zaman rayuwarsu.

Yang Xiaoyun, mai shekaru 52 da haihuwa ya ce: "A wancan lokaci, keke ya kasance wani abun hawa wanda kowane saurayi ke so ya mallaka a kauyuka. Matsayin keke a lokacin ya yi kamar matsayin mota samfurin BMW a wannan zamani. Kowannenmu yana son mallakar keke, wanda ya alamanta matsayin saurayi a kauyuka." Saboda wani keke samfurin "Yong Jiu", Yang Xiaoyun ya shahara a dukkanin kasar Sin shekaru 27 da suka gabata. A watan Agusta na shekarar 1981, wato shekara ta uku da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, manomi Yang Xiaoyun a gundumar Yingcheng ta lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, wanda ya yi girbi mai armashi sakamakon manufar yin kwangila bisa iyalan manoma kan yawan amfanin gona da aka samu da gwamnatin kasar ta tsara, ba ma kawai ya sauke nauyin da gwamnatin kasar ta danka masa ba na bayar da hatsi ga gwamnatin, hatta ma ya sayar da rarar hatsin da nauyinsa ya kai kilogiram dubu 5 ga kasar. Sabili da haka, manomi Yang Xiaoyun ya sami lambar yabo daga wajen gwamnatin kasar Sin. Daga baya, Yang ya nuna bukatarsa ga gwamnatin kasar tare da cikakkiyar jaruntaka, wato yana son a ba shi damar sayen wani keke samfurin "Yong Jiu" da aka kera a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin.

A wancan lokaci, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen waje ba da jimawa ba, ana karancin kayayyakin masana'antu iri-iri, ciki har da keke samfurin "Yong Jiu", wanda ya kasance kayan alatu da ba kasafai akan ga irinsa ba a birane, balle ma a kauyuka. Saboda haka, an bayyana bukatar manomi Yang Xiaoyun ta sayen wani keke samfurin "Yong Jiu" a Jaridar People's Daily, wadda ta fi bugawa a nan kasar Sin. A wancan zamani, bukatar da Yang Xiaoyun ya yi ya kawo kalubale ga tsarin tattalin arziki bisa shiri da kasar Sin ta gudana a lokacin.

Shugaban masana'antar kera kekuna ta Shanghai ta wancan lokaci, Wang Yunchang ya bayyana fatansa na baiwa Yang Xiaoyun kyautar wani keke samfurin "Yong Jiu", haka kuma Jaridar People's Daily ta bayar da bayanin edita, inda ta goyi-bayan abin da masana'antar kera kekuna ta Shanghai ta yi. Ba tare da bata lokaci ba ne, masana'antar ta aika da kekuna samfurin "Yong Jiu" zuwa gundumar Yingcheng.

"Ayarinmu dake da kekuna 3 ya nufi gundumar Yingcheng, inda muka sami lale marhabin daga wajen mazauna gundumar. A ganina, irin wannan marhabin da mazauna Yingcheng suka yi, ba gare ni mutum daya tilo ba, marhabin ne da jama'ar wurin suka yiwa dukkanin ayarinmu, inda manoma suka bayyana fatansu na samun kayayyakin masana'antu a kauyukansu."

Keke samfurin "Yong Jiu" da Yang Xiaoyun ya samu, keke ne da masana'antar kera kekuna ta Shanghai ta kera, musamman ma domin biyan bukatun manoma. Keken yana iya daukar kayayyaki masu nauyi, shi ya sa ya sami karbuwa sosai daga wajen manoma. Har yanzu dai irin wannan keke samfurin "Yong Jiu" ya kasance keke da ba'a taba ganin irinsa ba cikin tarihin kera kekuna na duniya.

Wannan keke ba ma kawai ya taimakawa Yang Xiaoyun wajen gudanar da muhimman ayyuka ba, hatta ma Yang Xiaoyun yakan baiwa mutane da dama aron keken, domin yin wani abu mai ban sha'awa.

"Idan wani mutum ke son yin amfani da kekena domin auren macen da yake so, to, zan ba shi aro. A wancan lokaci, keke shi ne abu mafi kyau da aka iya yin amfani da shi wajen yin aure."

Wannan keke samfurin "Yong Jiu", ba ma kawai ya daukaka kwarjinin Yang Xiaoyun da na iyalansa ba, abu mafi muhimmanci shi ne, wannan lamari ya sanya masana'antun kasar Sin sun samu muhimman sauye-sauye, wato daga yin kirkire-kirkire da sayar da kayayyaki daidai bisa shiri, zuwa sayar da su da nufin kansu. A wancan lokaci, gwamnatin Sin ta riga ta fara cire shamaki ga masana'antun kasar, kuma ta bullo da jerin matakai na bada 'yancin kai ga masana'antu. Bukatar Yang Xiaoyun ta samar da kyakkyawan zarafi ga masana'antun Sin wajen gudanar da harkokin saye da sayarwa cikin 'yanci ba tare da tsangwama ba.

"A cikin wannan matakin da muka dauka na tallafawa aikin gona da manoma, manoma da dama sun sami kwarin-gwiwa. Hakan ya fadakar da ni kan yadda zan yi domin neman 'yancin kan masana'antata."

Aikin da Wang Yunchang ya yi na aikawa da kekuna zuwa kauyuka da yankunan karkara, ya sa kaimi ga sayar da kayayyakin masana'antu cikin 'yanci, kuma ya daukaka cigaban yunkurin yin gyare-gyare kan kera kayayyakin masana'antu bisa shirin da aka tsara. Daga nan ne yawan kekuna samfurin "Yong Jiu" da aka kera ya karu ainun a kasar Sin.

"Yawan kudin da kasarmu ta zuba kalilan ne, shi ya sa ya kamata mu nemi bunkasuwa da karfin kanmu. Mun yi amfani da ribar da muka samu domin samar da alheri ga ma'aikata, da sabunta na'urorin masana'antarmu, ta yadda sikelin masana'antarmu ya habaka, har yawan kekunan da ta kera ya karu daga miliyan daya zuwa miliyan uku cikin 'yan shekaru kadan."

Tare da karuwar yawan kekuna samfurin "Yong Jiu" da aka kera, an shiga cikin lokacin tsakiya da karshen shekarun 80 na karnin da ya gabata. Sinawa da suka wadata sun soma yin amfani da irin wannan abun hawa¡ª¡ªkeke, adadin kekunan da Sinawa ke da shi ya kai miliyan 500 a tarihi. Sabili da haka, an lakabawa kasar Sin sunan "Sarkin Keke". Sakamakon karuwar bukatar keke da jama'ar kasar ke yi, an kara samun samfura iri daban-daban, kamar su samfurin "Fei Ge", da "Feng Huang" da dai sauransu, amma keke samfurin "Yong Jiu", keke ne da ya yi fice a cikin kekuna iri-iri. Ana sayar da kekuna samfurin "Yong Jiu" zuwa ko'ina a kasar Sin.

Dong Jianjun, wanda ya fara sayar da kekuna tun daga wancan lokaci, ya dade yana kaunar keke samfurin "Yong Jiu". Ya ce:

"Yayin da nike aiki a siton kekuna, na harhada sassa daban-daban na keke samfurin 'Yong Jiu'. Ta nuna hazaka mun hada kowane sashi na keke samfurin 'Yong Jiu'."

A cikin shekaru 10 ko fiye da suka shige, sayar da kekuna samfurin "Yong Jiu", muhimmiyar harka ce da Dong Jianjun ke gudanarwa. A cikin kantin sayar da kekuna mallakin Dong, akwai wata kofa dake dauke da kwali wanda ke kunshe da manyan kalaman Sinanci hudu cewa "Shang Hai Yong Jiu".

"Na dade ina sayar da kekuna samfurin 'Yong Jiu'. Salon keken ya sami sauye-sauye cikin sauri a shekaru da dama da suka wuce, wanda ya iya biyan bukatun jama'a da kasuwanni. Kusan a cikin kowane kantin sayar da kekuna, akwai kekuna samfurin 'Yong Jiu' da ake sayarwa. Muna iya cewa, in babu 'Yong Jiu', babu kantina."

Sakamakon cigaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da kyautatuwar zaman rayuwar Sinawa, ana kara samun ababen hawa da suke kawo sauki ga zirga-zirgar mutane, sannu a hankali sabbin ababen hawa sun maye gurbin keke. Amma, ana kara samun cunkoso sakamakon karin motoci, kuma hayakin da motocin suke fitarwa na gurbata muhallin halittu. Sabili da haka, keke ya sake dawowa zaman rayuwar mutane na yau da kullum. A halin yanzu, yawan kekunan da Sinawa ke da su ya kai miliyan 470, a shekarar bara kuma, adadin kekunan da aka kera a kasar Sin ya zarce miliyan 85. Dong Jianjun ya sami riba mai tsoka daga wajen harkar sayar da kekuna, inda ya ce:"Kowane lokaci ba za mu yi watsi da keke ba. Keke ya kawo sauki ga zaman rayuwarmu na yau da kullum. Alal misali, idan aka gamu da cunkoson motoci, yin amfani da keke ya fi sauki ga kowa da kowa."

Kamar yadda Dong Jianjun ya ce, a wannan zamani, ba ma kawai mukan yi amfani da keke a matsayin wani abun hawa na zaman yau da kullum ba, a'a, ba haka ba ne. A halin yanzu, ana kara samun kekunan zamani iri-iri, da hanyoyin yin amfani da su daban-daban, ciki har da hawan duwatsu, da yin gasanni, da motsa jiki. Ba kamar yadda aka kera kekuna na gargajiya samfurin "Yong Jiu" ba, an yi amfani da kayayyakin zamani wajen kera kekuna na yanzu.

Wang Yunchang, wanda ya shafe tsawon shekaru 40 ko fiye yana aiki tare da keke na "Yong Jiu" ya ce:"A ganina, ko da yake ana kara samun motoci a halin yanzu, amma za'a sake komawa ga yin amfani da kekuna a karshe. Saboda tsimin makamashin da keke ya yi, akwai kasashe da birane da dama wadanda suke kokarin shimfida hanyoyi na musamman wajen yin zirga-zirgar kekuna."

Daga yin tafiya da kafafuwa zuwa hawan keke mai tayoyi biyu, daga tukin babur zuwa tukin mota, a cikin shekaru 30 da suka gabata, sauye-sauyen ababen hawa sun alamanta cigaban zaman rayuwar Sinawa da habakar tattalin arzikin kasar. Ko shakka babu, keke samfurin "Yong Jiu" zai dade da kasancewa cikin zukatan jama'ar kasar Sin.

 

 

Email Us

hausa@cri.com.cn

Contant Us Kai Sama

Tel: 8610-68892509, 8610-68892424

 
 

China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040

 
http://www.beijing-olympic.org.cn/