Mu zagaya a birni Xi'an na kasar Sin

Xian, wani tsohon birni wanda ya ke da daddaden tarihi a kasar Sin ,an ce yana daya daga cikin manyan birane guda hudu na zamanin can da a duniya. Birnin nan ya shahara sabo da mutum mutumin dawaki da na sojoji na kafin bayyanuwar Innabi Isa da aka gano da kuma husumiyar Dayanta ta addinin Budha da kuma wani abinci mai dadi ci na Musulmi. A gabanin ranar bikin yanayin bazara,wata muhimmiyar ranar biki ce a kasar Sin,wato sabuwar shekara ce ta kalandar gargajiya ta kasar Sin ko da ya ke mutanen Sin suna amfani da kalandar da sauran kasashen duniya ke bi amma suna bin dabiunsu na wannan ranar biki.Wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya zagaya da mu a wannan birni mai daddaden tarihi na kasar Sin.

“Jiaozi” wani nau'in abinci ne na musamman a kasar Sin musamman a arewancin kasa, abincin gurasa ne amma a kan sa nama a ciki da ganyaye iri iri,yawancin mutane na kasar Sin suna so cin wannan abinci. Birni Xian yana arewa maso yammacin kasar Sin shi ya sa mazauana birnin ma suna so wannan abinci. Wani dakin sayar da abincin Jiaozi da ake kira “Defachang” yana cibiyar birnin, ya yi suna sosai. An kafa shi ne a shekara ta 1936,wato tarihinsa ya wuce shekaru saba'in. Wannan dakin saida abinci yana bin al'adu da dabi'u na kasar Sin sosai, ya nuna kauna ga jama'a ya dukufa wajen dafa abinci,ya yi amfani danyun kayayyaki masu inganci da haka ya samu karbuwa daga mazauna birnin,madafun abinci ma sun kware wajen shirya abinci. Ko da ya ke an samu manyan sauye saure a tarihin kasar Sin, amma dakin nan na saida abincin Jiaozi yana da nasa kasuwa,wani sa'i ma ya ci kasuwa da dama, lale ya samu kudi ya wadata.

Mr Zheng Jianjun,madugun madafun dakin saida abinci ne ya yi mana bayani kan abincin na Jiaozi da suka shirya, ya ce an shirya wannan abincin ne bisa hanyar da ake bi a babban birnin kasar Sin Beijing ke bi wajen shirya irin abinci,hakan bai isa ba, dakin ya tsamo fasahohi daga sauran dakunan shirya abinci wadanda suka yi suna a arewa da kudu na kasar Sin. Ya ce, “Abincinmu Jiaozi ya sha banban da na sauran wuraren Sin, kowanensu ya na da siffa tasa ta musamman, abubuwan da aka sa a ciki sun banbanta da juna, akwai irin na kifaye da amfanin ruwa, kun sani da akwai amfanin ruwa masu dimbin yawa, haka ma da ganyayen ci iri iri na yanayi daban daban , sai abincinmu na Jiaozi ma sun yi yawa,mun dafa su ma ta hanyoyi daban daban,mu kan gasa shi ko soya shi ko tafasa shi. Idan muka shirya dina da Jiaozi, mun iya samun ire irensu sama da dari uku.daga cikinsu da akwai na nama da na kifaye da na ganyaye ko kuma da wasu irin namu na musamman. Abincin Jiaozi ya bayyana al'adummu na gargajiya na kasar Sin kuma a hade da tarihin birnin Xian.”

Wata hanyar da ake bi wajen cin abincin Jiaozi ita ce a kan sa karamar tukunya a kan teburin cin abinci a karkashinta a sa wuta,sannan a sa tafasashen ruwa a cikin tukunya, da ruwan ya tafasa, a sa cefane iri iri a ciki,sannan a sa Jiaozi a ciki,bayan kibtawa da bismila,abinbin Jiaozi ya dafu,ka iya ci shi. Da aka ci abincin Jiao,a kan hada abinci da al'adu. Idan aka sa Jiaozi daya a cikin kwanon cin abinci, yana nufi kome na tafiya daidai, idan aka sa biyu a ciki, a ce albishi biyu za su zo;idan aka sa uku,shida,da tara,yana nufin cewa za ka samu babban ci gaba a wannan shekara. Idan aka sa biyar a ciki,an ce ka samu kome da kake bukata; idan aka sa bakwai a ciki,burinka zai tabbata, idan aka sa takwas,yana nufin cewa kowane mutum yana da damar nuna kwarewarsa,idan aka sa goma a ciki,sai a ce muradinka zai cika.

Kowa yana kan hanyarsa ta gaba tare da farin ciki. Dakin saida abinci na Defachang ya kware wajen shirya abincin Jiaozi, suna iya shirya irin abincin da fasahohinsu, wasunsu siffarsu ta yi kama kifaye masu launi iri iri, wasu kuwa siffarsu ta yi kama da zomaye, wasun kuwa sun yi kama da ‘ya'yan itatuwa daban daban wasu kuwa sun yi kama lu'ulu'u, kwarewarsu wajen shirya abinci ta kan dauke hankalin masu cin abinci,lokacin da suka cin abinci a wannan dakin saida abinci, su kan yi mamaki da ganin kwarewar madafu, suka kan yi musu yabo. “Sifofin abincinsu na Jiaozi sun dauke hankalina, sun ba ni mamaki sosai sun yi kama abubuwan da nake gani yau da kullum. Lalle suna da kyaun gani sosai kuma suna da dadin ci. Duk lokacin da aminaina da dangina sun zo nan birnin Xian, na kan kawo su a nan dakin saida abinci na Defachang, mun bar su dandana abincinmu na musamman.”

A cikin shekarun baya, dakin cin abinci Defachang ya samu babban cigaba, yana ta inganta kwarewarsa wajen shirya abinci,kuma ya kan gabatar da sabbi maimakon tsofafi bisa yanayi.nau'o'in abincinsu na kara karuwa, masu cin abinci a wannan daki ma suna rika karuwa,wani sa'i ma ya cike da masu cin abinci.masu yawon shakatawa na gida da na waje sukan tafi dakin saida abinci na Defachang. Mr Zheng Jianjun ya ci gaba da cewa, “A cikin shekarun baya bayan nan Defachang ya mai da hankali wajen amfani da ganyayen ci, yana ci gaba tare da zamani ya dukufa wajen shirya abinci mai inganci kuma mai gina jiki ta hanyoyi daban daban yana kuma kokarin biyan bukatun mutanen gida da na waje da suka bakunci dakin.

Jama'a masu sauraro, yanzu wakilin gidan rediyonmu ya zagaya da mu a wani lambun shan iska mai suna Furongyuan wadda asalinta ta zo ne daga tarihin daular Tang na kasar Sin wadda ta yi shahara a duniya. Lambun nan yana kudu da birnin Xian,lambun shan iska ne na sarakuna a tarihi. Daular Tang wata daula ce da ta fi karfi da wadata a tarihin kasar Sin, shi ya sa kamaninsa ya bayyana halayar gidan sarauta. An gina sabon lambu ne bisa irinsa na tarihi kuma a wurin da ya shimfidu a tarihi, an bi hanyar gina lambunan gidan sarauta wajen shimfida sabo, lambun sha iska ne mafi girma ta fannin al'adu a arewa maso yammacin kasar Sin. Kuma lambu ne daya tak da ya bayyana tarihin daular Tang mai karfi a kasar Sin,fadinsa ya wuce kadada sittin.

A cikin lambun da akwai dakuna masu sifofi daban daban,wasu na kan tuddai,wasu na cikin duwatsu, wasu kuma na bakin ruwan tafki, wasu kuma na bakin kogi,akwai manya da kanana da kuma matsakaita,an yi musu fanti mai launi daban daban, a jikin banguna ma an zana zane iri iri hade da tatsuniyoyi da wurare masu ban sha'awa. In kana zagaya cikin lambun sai ka ce kana zagaya ne cikin zanen da aka tsara,lale yana da kyaun gani sosai,ya kuma dauke hankalin maziyarta kamar a ce kana cikin gidan aljana. Wata daliba mai suna Li Nan ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa ta shafe duk safiya tana lambun tana jin dadin yanayin lambun, ta ce da akwai abubuwa da yawa da suka dauke hankalinta a cikin lambu. Ta ce” abin da ya fi daukar hankalinta shi ne wani film da aka nuna ta hanyar zamani. Da aka fara nuna sinima kamar ka shiga wata duniya dabam, wani haske ya rufe ka,wata wuta jar wur ta tashi, ka kuma ji karar abubuwa, sun ba ni mamaki sosai. A cikin wannan lambu da akwai wasanni iri iri da aka shirya domin maziyarta,masu yawon shakatawa ma za su iya shiga ciki. An shirya wasan kwaikwayo na kokawa da aure na shekaru aru aru, idan ka shiga ciki wasan, kamar ka shiga cikin tarihi, wannan wasan ya shere masu yawon shakatawa,ya kuma ba su sha'awa ta wadannan wasannin da aka shirya kana jin dadin bakuncin a birnin Xian kana kuma kara ilminka na game da tarihin daular Tang na kasar Sin'.

A kan shirya wasanni bisa ruwan tafkin da ke cikin lambun Furongyuan na birnin Xian saboda fadinsa ya fi girma a duniya, an kuma dasa bishiyoyi da furani iri iri a ciki wasunsu suna da kamshi inda gine gine na gidan sarautar daular Tang suna tsaye,maziyarta su kan yi yawo a cikin wannan lambu domin jin dadin zamansu. A ranar bikin yanayin bazara na wannan shekara da muke ciki an shirya gaggarumin shagali domin murnar wannan ranar biki ta gargajiya ta kasar Sin. Jama'a masu sauraro, kun dai saurari shirinmu na zaman rayuwar Sinawa