Mutanen birnin Tianjin suna murnar Shagalin Yanayin Bazara na gargajiya mafi muhimmanci a kasar Sin

Yanzu ana yin murna da shagalin barka da sabuwar shekara bisa kalandar wata ta kasar Sin, wato shagali mafi muhimanci a kasar. Sinawa suna da al'adu iri iri lokacin da suke yin wannan shagali, kuma ana da al'adu iri daban daban a wurare daban daban. Tun daga yau zuwa ran Jumma'a ta wannan mako, za mu bayyana muku wasu shahararrun biraren kasar Sin a fannin yawon shakatawa domin ganin yadda ake yin wannan shagalin na barka da sabuwar shekara bisa kalandar wata ta kasar Sin.

Zango na farko da za mu kai ziyara yau shi ne birnin Tianjin wanda ke arewacin kasar Sin, kuma ke makwabtaka da birnin Beijing . Birnin Tianjin na daya daga cikin biranen da suke da al'adu iri iri mafi yawa. Alal misali, a kan titin al'adu na birnin Tianjin , za a iya ganin yanayin al'adu iri daban daban. Lokacin da ake murnar bukukuwa ko a karshen mako, a kan shirya nune-nunen al'adu da wasannin Pekin Opera da nune-nunen fasahar shan ti da na fina-finai. Mr. Zhang Ran, wanda yake shan iska a Tianjin yana farin ciki kuma ya gaya wa wakilinmu cewa, “Da isowata a birnin Tianjin, nan da nan sai na ga al'adun da aka kirkiro a yankunan kogin Haihe da fadar sarauniya ta sararin sama. Ana kiyaye al'adun jama'a kamar yadda ya kamata, kuma ana shirya bukukuwan nune-nunen wadannan al'adu da kyau.”

Tun daga ran 1 ga watan Janairu zuwa ran 9 ga watan Faburairu, wato ran 15 ga watan farko bisa kalandar wata ta gargajiya ta kasar Sin, lokaci ne da ake samun cikar jama'a a kan wannan titin al'adu da aka kafa shi yau da shekaru 600 da suka gabata. Lokacin da ake murnar shagalin barka da sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin a shekarar da muke ciki, an shirya bukukuwan nune-nunen al'adun jama'a da yawa a kan wannan tsohon titin al'adu domin jawo hankulan masu yawon shakatawa. Mr. Li Yongli, direktan sashen kamfanin raya titin al'adu na birnin Tianjin ya ce, “A shekarar da muke ciki, mun shirya jerin nune-nunen al'adu, ciki har da wasannin kwaikwayo na jama'a iri iri domin bayyana wa masu yawon shakatawa al'adun birnin Tianjin . Musamman, za a iya kallo wasannin kwaikwayo na ‘Sarki ya kawo mana arziki' da ‘Sarki ya kawo mana fatan alheri'. Dan wasa da ke sanya tufafin sarki zai yi wannan wasa da masu yawon shakatawa da ‘yan kasuwa cikin hadin gwiwa. Sabo da haka, ‘yan kasuwa za su iya samun fatan alheri da arziki, masu yawon shakatawa za su iya yin farin ciki lokacin da suke murnar sabuwar shekara bisa kalandar wata ta gargajiya ta kasar Sin a Tianjin .”

Idan ka sha iska a birnin Tianjin , ba ma kawai za ka iya jin dadin al'adun jama'a ba, har ma za a iya kallon shahararrun kananan gine-gine masu hawa biyu. A cikin mutanen da suke yin sana'ar yawon shakatawa a kasar Sin, a kan bayyana cewa, “Idan kana son sanin tarihin kasar Sin da ya shafi shekaru dari daya da suka gabata, sai ka je birnin Tianjin ”. Ba ma kawai an soma raya ilmin zamani da harkokin soja da jirgin kasa da gidajen waya da sana'ar sarrafa sinadari a birnin Tianjin ba, har ma muhimman al'amuran tarihi da yawa na kasar Sin sun auku a wannan birni. Tun daga shekara ta 2008, an zabi irin wadannan kananan gine-gine masu hawa 2 guda 10 da su zama wuraren yawon shakatawa. Mr. Jin Fan, direktan hukumar kula da al'adu da harkokin yawon shakatawa ta shiyyar Heping ta birnin Tianjin ya bayyana cewa, “Wadannan kananan gine-gine masu hawa biyu suna kunshe da tsohuwar fadar yarima da ke titin Chongqing da tsohon gidan marigayi Vi Kyuin "Wellington" Koo , wato wani muhimmin dan diplomasiyya na kasar Sin a da da wasu dakunan ajiyar kayayyakin tarihi da dai sauransu. Bugu da kari kuma, suna kunshe da wasu gidajen nagartattun mutane.”

Ba ma kawai a kan titi mai lamba 5 ana samun irin wadannan kananan gidaje masu kyan gani ba, har ma za a iya kai ziyara a unguwar kananan gidaje masu nuna al'adun kasar Italiya da ke bakin kogin Haihe. An soma raya wannan unguwar da fadinta ya kai murabba'in hekta 28 tun daga shekarar 1902, inda aka gina gidaje da kananan ofisoshin jakadanci da ofisoshin gwamnatin birnin Tianjin da hukumar masana'antu da sansanin soja da makarantun zamani wadanda suke bayyana al'adun kasashen yammacin duniya. Yanzu ta riga ta zama unguwa mafi girma da ake tsaronta da kyau, kuma ke bayyana al'adun kasar Italiya sosai.

A matsayin unguwar nune-nunen al'adun kasar Italiya da ke daya daga cikin unguwannin nune-nunen al'adun musamman guda 12 a birnin Tianjin, za a shirya bikin nuna al'adun kasar Italiya domin jawo hankulan masu yawon shakatawa. Mr. Bai Jiyuan, wani jami'in ofishin kula da harkokin kogin Haihe na birnin Tianjin ya ce, “Muhimman abubuwan da za mu nuna wa masu yawon shakatawa su ne, za mu gayyaci shahararrun kuku-kuku na kasar Italiya wadanda suke da fasahar yin nau'in abincin Pizza da taliya da kofi. Sannan za mu shirya bukukuwan nune-nunen al'adu iri iri, ciki har da wasannin kwaikwayo da ke nuna al'adun Italiya.”

Wakilinmu ya samu labari daga hukumar yawon shakatawa ta birnin Tianjin cewa, tun daga karshen watan Disamba na shekara ta 2008 zuwa watan Faburairu na shekara ta 2009, za a shirya bukukuwan yawon shakatawa har sau 34 a cikin birnin Tianjin da wasu gundumomin da ke karkashin birnin. Sabo da haka, mazauna birnin Tianjin da masu yawon shakatawa za su samu dama da wurare na shan iska da hutu. Mr. Wang Jun, direktan ofishin sa kaimi kan cigaban yawon shakatawa na hukumar yawon shakatawa ta birnin Tianjin ya ce, “Za a iya daukar hanyar dogo mai sauri zuwa birnin Tianjin domin shan iska a birnin. Mun riga mun yi share fagen bukukuwan yawon shakatawa iri iri domin murnar shagalin yanayin bazara na gargajiya na kasar Sin. A wancan lokaci, za a iya shan iska a yanayin dusar kankara da yin wanka a cikin tafkin ruwan dumi da sanin al'adun jama'a a cikin yanayi mai daukar sauti. Alal misali, an riga an soma shagalin wasan skiing tun daga ran 27 ga watan Disamba na shekara ta 2008. A waje daya kuma, a karo na farko an soma shagalin yawon shakatawa na gina jiki a gundumar Baodi. Masu yawon shakatawa za su iya jin dadin ruwan dumi a cikin lokacin sanyi mai tsanani. Bugu da kari kuma, mun gayyaci ‘yan wasa na kabilun Miao da Wa da suka fito daga kudancin kasar Sin a lambunan nune-nunen bishiyoyin yanayin zafi, inda masu yawon shakatawa za su iya sanin al'adun yanayin zafi na kudancin kasar Sin a birnin Tianjin wanda ke arewacin kasar.”

Tun daga ran 1 ga watan Agusta na shekara ta 2008, an soma kaddamar da hanyar dogo mai saurin gaske a tsakanin birnin Beijing da birnin Tianjin . Sakamakon haka, masu yawon shakatawa da yawa da suka fito daga sauran wurare a kasar Sin da kasashen waje sun soma san birnin Tianjin da kuma fahimtar birnin, har ma suna fatan za su iya samun damar kai ziyara ga birnin Tianjin. Mr. Jin Tielin, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta birnin Tianjin ya ce, “Bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing , wannan hanyar dogo mai saurin gaske ta hada birnin Beijing da birnin Tianjin . Muna samun moriya sosai daga wannan hanyar dogo mai saurin gaske. Bayan da masu yawon shakatawa na ketare suka kammala ziyararsu a birnin Beijing, su kan je birnin Xi'an da Guilin, amma yanzu suna kuma zuwa birnin Tianjin. A da, yawan mutanen birnin Tianjin da suka sha iska a sauran wurare yana da yawa, kuma yanzu yawan mutanen da suke zuwa birnin Tianjin domin yawon shakatawa yana ta karuwa. Wannan abin farin ciki ne.”

Jama'a masu sauraro, a lokacin da ake murnar shagalin yanayin bazara na gargajiya na kasar Sin, ana da bukukuwa iri iri a birnin Tianjin . Muna maraba da zuwanku birnin Tianjin domin sanin al'adun birnin Tianjin da na kasar Sin baki daya.