Ana murnar sallar yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin a Hongkong

Ranar sallar yanayin bazara ta gargajiyar kasar Sin ta zo wajenmu, a ko'ina a kasar Sin ana cike da halin fara'a na nuna murnar wannan rana . A yankin musamman na Hongkong na kasar Sin, an shiga irin wannan rana hali na yin murnar sallar.

Ana kiran Hongkong da cewar “shaharariyyar Kasuwar aljanna”. In masu yawon shakatawa suna son zuwa yawon shakatawa da kuma saye kayayyaki, to yawancinsu suna son zuwa Hongkong don cim ma burinsu. Tongluowan shi ne mashahurin yankin kasuwanci na Hongkong, filin da ake kira “Time's Square” da babban kanti da ke da lakabi “Sogo” wadanda suke kusa da yankin Tongluowan sun riga sun zama wuraren da masu yawon shakatawa suke da sha'awar kai ziyara gare su. Duk da yake masu yawon shakatawa na babban yankin kasar Sin suna da sha'awar ziyarartarsu , to, ka iya gano cewa, ma'aikatan wuraren nan biyu suna da himmar ba da hidima ga masu yawon shakatawa tare da yin amfani da harshen Ingilish da daidaitaccen sinanci.

Filin” Time's Square” wani babban gini ne da ke da benaye 16, ba ma kawai yana daya daga cikin manyan cibiyoyin sayen abubuwana Hongkong ba, hatta ma yana daya daga cikin ni'imtattun wurare mafi girma da kungiyar yawon shaktawa ta Hongkong ta zaba wajen sayen abubuwa a Hongkong. Wata malama mai suna Ling Yuan, babbar manaja ta filin “Teme's Square” ta bayyana cewa, Filin “Teme's Square” shi ne kasuwa daya tak da ake iya sayen duk abubuwan da kake son sayensu a sa'I daya a Hongkong. Farashin kayayyakin da ake sayarwa na da arha ko tsada, iri iri ne da ake yi , har ma da akwai abincin da ake sayarwa tare da dakunan nuna wasannin kwaikwayo da kantunan zamani, kai, filin yana kunshe da abubuwa da yawa, kamar dai yana da kome da kome. A lokacin da ake murnar sallar Chrismeti na shekarar da ta shige, an kafa wani lambu na irin surar kankara da kankara mai taushi a wurin waje da babban ginin filin, amma a lokacin da ake murnar sallar yanayin bazara ta gargajiyar kasar Sin, an kafa wani lambu na irin surar maraba da yanayin bazara, sa'anan kuma an yi masa babban batun da ke cewar “Shanun zinariya”, duk saboda shekarar da muke ciki bisa kalandar noma ta gargajiyar kasar Sin ita ce shekarar da ke alamanta shekarun haihuwar mutane ta hanyar amfani da shanu. Sa'anan kuma da akwai ginshikan zinariya da kujerun da aka kafa don biyan bukatun masu yawon shakatawa wajen yin hutu, ta hanyar nan ne za a iya kawo alheri gare mu.

Ban da Tongluowan, sauran wurare kuma su ne filin da ake kira “Pasific” da ke tsakiyar Hongkong da Jiansazui da ke yankin Jiulong, wadanda wurare ne mafi kyau da ake iya sayen abubuwa iri iri da yawa. Wadannan wurare na da manyan kasuwanni tare da kananan shaguna iri iri da yawa wadanda suka jeri kafada da kafada, inda ake sayar da abubuwa kusan kome da kome da ake bukata.

Ban da sayen abubuwa, ana iya kai ziyara a ko'ina a Hongkong yadda aka ga dama, ana iya hangar bakin teku na Vitoria a dari daga wani tudu mai suna Taiping, sauransu da akwai dakin mutum-mutumin da aka yi da kyandir na Madam Tussaud's da filin Zijin na zinariya har da lambun teku na Hongkong da lambun Disneyland.

Lambun teku na Hongkong na da dakunan nuna amfanin teku mafi girma a kudu maso gabashin Asiya da lambun shan iska da annashuwa da ke da babban batu. Suna dab da duwatsu da teku, suna da ni'ima sosai, masu yawon shakatawa suna son kai ziyara a wadannan lambuna. Inda ana iya ganin filayen teku iri iri da wasannin da kifayen teku da ake kira “dolphin” cikin Turanci suke yi . Sa'anann kuma ana iya shiga sauran wasanni. Yanzu sai mu saurari bayanin da shugaban lambun teku na Hongkong mai suna Sheng Zhiwen ya yi.

Sunana Sheng Zhiwen, kuma ni ne shugaban lambun teku na Hongkong. Lambunmu shi ne lambun jama'a. A shekarar da ta shige, yawan masu yawon shakatawa da suka kawo ziyara a nan ya wuce miliyan 5. Inda ake iya ganin naman daji da yawa da kifayen teku da ake kira “dolphin” cikin turanci da Panda da sauransu, a gaskiya dai kusan akwai kome da kome, ina fatan masu yawon shakatawa su zo nan Hongkong don yin yawon shakatawa, kuma ina fatan kowa da kowa zai yi zaman alheri.

Ana kuma kiran Hongkong da cewar “Hedkwatar wuraren cin abinci”, yawan gidaje da dakunan cin abinci ya wuce dubu 9.

A gidaje da dakunan cin abinci, ana iya cin abinci irin na kasashen Vietnam da Malasiya da Korea ta kudu da na Japan da na Turai da na Amurka da sauransu, abinci iri iri da ake yi a Hongkong sun hada da halayen musamman na kasashen yamma da na gabas.

Mutanen Hongkong su kan karya kumanlo a dakunan cin abinci, ko ma su karanta jaridu a wadannan dakuna.

A Hongkong, ana sayar da amfanin ruwa da yawa a lokacin sallar yanayin bazara, masu yawon shakatawa suna iya zuwan kauyen kamun kifaye ko dakunan nuna zane-zane da ba su da nisa da cibiyar Hongkong don cin kifaye iri iri da yawa da sauran amfanin ruwan teku, ko ma su iya more ni'imtattun wurare ta hanyar daukar jiragen ruwa zuwa tsibirin Nanya da Dayushan da sauransu.

A lokacin sallar yanayin bazara, in masu yawon shakatawa sun kai ziyara a Hongkong, za su iya duba wasannin iri iri da yawa, kamar su, yin zirga-zirgar kekuna masu surorin furanni iri iri, da wasan wuta da ke iya bayyana surar shanu da sauransu.

Hongkong da ke da yayi sosai a duniya tana kara karfin jawo hankalin mutane a bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin, ana maraba da zuwa masu yawon shakatawa a Hongkong don murnar sallar bazara ta gargajiyar kasar Sin tare da mutanen Hongkong.