Abinci irin na gargajiyar kasar Sin wato Jiaozi

A lokacin bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin, A yawancin wuraren kasar Sin, dole ne a ci wani abinci irin na gargajiyar kasar Sin wato Jiaozi ke nan, wannan ya riga ya zama wata al'ada ga mutanen kasar Sin.

Sifar Jiaozi tana tamkar yadda sifar sabon wata ya ke da ake yi ta hanyar yin amfani da garin alkama da ganyayen lambu da nama da gishiri da sauransu, kuma ana sanya jiaozi a cikin ruwan da ke tafarfasa sosai har zuwa lokacin da ya nuna. Dayake sifar Jiaozi ta yi kama da sifar tsohon kudin kasar Sin wanda ake kiransa da cewa “Yuanbao” cikin Sinanci, shi ya sa a cikin al'adar kasar Sin, Jiaozi yana almanta dukiyoyin da ake da su, saboda an hada da garin alkama da ruwa, kuma an yi amfani da guntayensu, an sanya nama da ganyayen lambu da sauransu a ciki, sifarsa ta yi kama da abun da'ira, shi ya sa a wajen jama'a, jiaozi yana alamanta bikin ganawa da juna. Saboda haka a kowanen bikin sabuwar shekara, ana cin Jiaozi, wannan yana kawo kyakyawan alheri ga jama'a wajen samun wadatuwa da yin bikin ganawa da juna.

A cikin al'adar kasar Sin, game da abubuwan da ake sanyawa a cikin jiaozi, da sifofinsa da yadda ake ci, dukkansu ana yi ne bisa ka'idojin musamman. Da farko, za mu yi bayani dangane da abubuwan da aka sanya a cikin Jiaozi, wasu mutane su kan sanya abubuwa na irin nama tare da ganyayen lambu da gishiri da sauransu, amma wasu mutane daban suna son sanya abubuwa irin na ganyayen lambu da gishiri da sauransu kawai ba tare da nama ba. Muhimmin aikin yin jiaozi shi ne yayyanka nama da ganyayen lambu da kuma sanya sauran abubuwa kamar su gishiri da citta da masoro da citta mai ‘kwaya da man girki da dai sauran irinsu a ciki. Lokacin da ake yayyanka nama da ganyayen lambu, wuka da katakon kichin suna yin karo da juna sosai, suna fitar da sauti mai karfi sosai, wato Peng! Peng! Peng!------, mutane suna son saurarar irin sautin da ke da kara sosai cikin dogon lokaci, saboda a cikin harshen Sinanci, sautin kalmar nama shi ne “You”, amma sautin kalmar ganyen Lambu shi ne cai , an hada kalmomin You da Cai, don su zama kalmomi kamar yadda “You Cai” ke nan, to, wannan ya yi kamar yadda ake cewa, “ da akwai dukiyoyi ke nan” , in ana yin aikin cikin dogon lokaci, to kamar yadda ana samun dukiyoyi cikin dogon lokaci, in wani iyali yana dafa jiaozi da yawa, to wannan ya almanta cewa, iyalin yana zaman rayuwa cikin wadatuwa da faranta rai sosai.

Bayan da aka gauraya nama da ganyayen lambu da masoro da citta da man girki da sauran irinsu gu daya, sai a soma yin jiaozi, an yi sifar jiaozi bisa al'adar da ake bi, wato yawancin iyalai sun yi jiaozi bisa sifar gargajiya wato irin ta sabuwar wata. An yi aikin nan kamar haka: da farko, an sami wani guntun abun da ke kunshe da garin alkama da ruwa, an murza su don yin sifarsu kamar yadda da'ira ta ke, an sa nama da ganyayen lambu da sauran abubuwan da aka hada su gu daya, sa'anan an hada wanda aka kammala murza shi don sifarsa ta zama sifar sabon wata.

Bayan da aka kammala aikin nan, sai a soma sanya Jiaozi cikin ruwan da ke tafarfasa sosai, har zuwa lokacin da ya dafu sosai. Bayan da aka sanya Jiaozi cikin ruwan da ke tafarfasa sosai, sai a yi amfani da cokali don tuka su a cikin tukunya, don kada su nutse a tukunya, ana kan zuba ruwan sanyi a cikin tukunya har sau uku, kamar yadda aka sami alheri sau uku ke nan, in lokacin ya wuce minti goma ko 20, sai Jiaozi ya dafu, sa'anan kuma a soma cin Jiaozi mai dadin ci sosai.

Wasu mutane su kan sanya tsabar kudi ko dabino a cikin Jiaozi, don nuna fatansu na samun dukiyoyi a sabuwar shekara.

Cin Jiaozi shi ne al'adar kasar Sin, in bakin kasashen waje sun sauko kasar Sin, ya kamata su dandana Jiaozi, ana cewa, in ba su taba cin Jiaozi ba, to ba su san abubuwan kasar Sin sosai ba. A wajen mutanen kasar Sin, dukkan mutanen iyalinsu sun taru gu daya, suna dafa Jiaozi, suna murna sabuwar shekara cikin farin ciki sosai, suna taya junasu murnar sabuwar shekara da yi wa junansu fatan alheri da samun kanciyar hankali.