Tatsuniyar jajibirin sabuwar shekara

A rana ta karshe ta watan Desamba da dare na kowace shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ana kiransa Chuxi. Kalmar Chu wadda ma'anarta wato kawar da wani abu ne, Xi kuwa dare ke nan. Chuxi wato kawar da dare na karshen shekarar da ake ciki da yin maraba da zuwan sabuwar shekara. A kasar Sin kuma akan kira jajibiri da sunan “kawar da dare”, ko “daren shekara”, ko kuma “Ran 30 ga Disamba na shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin”.

Jama'ar kasar Sin suna da al'adu da yawa game da jajibirin sabuwar shekara. Al'adar tsabtar gama-gari a jajibirin tana da dogon tarihi. Cikin ‘yan kwanaki na gabannin jajibirin, mutane sukan share dakunansu na gida da na waje sosai. Aranar jajibirin kuma akan mai da babban karfi wajen tsabtar gama-gari don “fid da rubabbu da daukar sababbi”. Irin wannan al'ada ta zo daga tatsuniyar zamanin da, an ce a zamanin da sarkin Zhuanxu yana da wani dansa malalaci wanda ya ba ni kunya, yakan sa tufaffi tsumma da shan kunu a zaman yau da kullum. Ya mutu a jajibirin wata sabuwar shekara da dare a wata kusurwar dakinsa sabo da sanyi da yunwa. Sabo da haka, lokacin da mutane ke tsabtace dakunansu a ranar jajibirin, sukan fitar da tufaffi tsumma da abincin da suka yi musu saura, akan zubar da su kafin zuwan sabuwar shekara, wannan yana nufin cewa an hana shigowar talauci cikin gida.

Bayan tsabtar gama-gari, mutane sukan manna takardun waka-kwar-biyu a jikin kofofinsu, da rataye fitilu domin haifar da halin annashuwa. A jajibirin kuma mutane sukan sha wani irin abin sha da ake kira “Tusu” wanda aka yi da giya da ruwa. An ce, cikin wata bukkar da ake kira “Tusu”, an zaunar da wani mutum da ba safai akan irinsa ba, wanda ya tono saiwoyin tsime musamman cikin dazuzzukan tuddai. A duk lokutan jajibiri, yakan ba wa iyalan kauyawa kyautar maganin gargajiya na kasar Sin da ya hada, kuma ya gaya musu cewa, dukkan ‘yan iyalansu za su sha irin wannan magani a rana ta farko ta sabuwar shekara, da haka ne za su iya kawar da cututuka da masifa. Kuma ya gaya wa kauyawa irin saiwoyin tsime da ya yi amfani da su cikin magungunan da ya hada ba tare da rage kome ba, don haka kauyawa suke kira irin wannan magani da sunan “Tusu”. A kashin gaskiya kuwa mene ne maganin “Tusu”? Bisa abubuwan da aka rubuta cikin littattafan magungunan zamanin da an ce, an hada shi ne da ire-iren magungunan gargajiya na kasar Sin har guda 7 ciki har da irin maganin da ake kira Rheum officinale da jijiyar lemu wadanda ke da amfani don yin rigakafi da warkar ciwace-ciwace.

A jajibirin sabuwar shekara da dare, akan hadu don cin abinci, kusan an ce wannan ya zama al'adar gargajiya ta kowace iyali. A wannan rana, duk wadanda suke aiki a sauran wurare, idan sun samu dama, sai su koma gida don haduwa da ‘yan iyalansu, kuma sun dafa abinci iri-iri masu dadi don ci tare a jajibirin da dare.

A wurare daban-daban na kasar Sin, irin abincin da ake ci a jajibirin da dare su ma sun sha bamban. A kudancin kasar abincin yakan hada ne da nama da ganyaye wadanda yawan irinsu ya kai fiye da 10, daga cikinsu tilas ne da akwai irin abincin da ake kira “Tofu” wanda aka yi da wake da kuma kifi, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne sabo da kalmar “Fuyu” wadda lafazinta cikin Sinanci ya yi daidai da na “arziki”. A arewancin kasar, yawancin iyalai suka ci abincin Jiaozi a jajibiri da dare, ‘yan iyali duka suna yin Jiaozi tare, irin wannan abinci an yi shi ne ta hanyar kunsa daddatsattse nama mai dadin ci cikin kullin garin alkama mai siffar da'ira, bayan da aka kammala aikin yin Jiaozi, sai a dafa su cikin tafasassen ruwa, kuma an sa kayan zaki a cikin, duk ‘yan iyalin sun zauna a kewayen tebur suna cin Jiaozi tare cikin annashuwa. “Jiaozi” yana alamta haduwar ‘yan iyali.

A ranar jajibiri da dare, mutane sukan yi jagorar yaransu zuwa wajajen dangi da aminansu don ba su kyautar abubuwa, da yi musu barka da sabuwar shekara, haka ake kiran shi “Kuisui” wato ba da kyauta ga shekarar da ta wuce. Idan da baki sun zo sun ci abinci tare da ‘yan iyali a jajibirin sabuwar shekara da dare, sai a ce “Biesui” ke nan wato yin ban kwana da shekarar da ta wuce. Bayan cin abincin, dukkan mutane sukan nuna wa juna godiya da yi wa junansu barka da sabuwar shekara, daga baya kuma kowa ya koma gidansa, wannan shi ake kira “Sansui” wato a tashi daga tsohuwar shekara. Cikin gida, ya kamata mutane matasa su nuna gaisuwa ga dattawa, mutane dattawa kuma su yi wa matasa wasu maganganun gargadi, kuma su bai wa yaran da ba su isa zuwa wurin aiki ba kudin kyauta domin murnar sabuwar shekara, kuma sun yi wa juna barka da sabuwar shekara, haka ake kira “ban kwana da tsohuwar shekara” A wannan lokaci, dukkan mutane ba su son su yi barci, ‘yan iyali duka suna kallon talabijin, ko yin wasan kati, suna more zaman jin dadi har zuwa sabuwar shekara, haka ake kira “yin kwana zaune a jajibirin sabuwar shekara”.

“Yin kwana zaune a jajibirin sabuwar shekara” ta zama wani aiki ne da aka saba yi a jajibirin. Cikin waka mai suna “Yin kwana zaune a jajibirin sabuwar shekara” da Lu You, mawakin tsohon zamanin kasar Sin ya rubuta, akwai jumloli masu kyau kamar haka, “Yara sun tsaya ba su yi barci ba, sun yi kwana zaune suna yin kwaramniya a tsakar dare”. A lokacin da ake yin kwanan zaune a jajibirin sabuwar shekara, yara sun fi farin ciki, don su yara wadanda ake tsayawa sosai a kansu a kullum, su ma sun karya dokokin da aka yi musu a wannan lokaci, sun yi farin ciki tare da manyan mutane wajen yin kwana zaune har gari ya waye na rana ta farko ta sabuwar shekara, ana cike da kyakkyawan halin annashuwa na yi ban kwana da tsohuwar shekara da yin maraba da zuwan sabuwar shekara.