Mataimakiyar shugabar ofishin harkokin waje ta birnin Shanghai Madam Wu Jinlan ta ce, birnin Shanghai ya ba da taimako gwargwadon karfinsa ga takwaransa na Afrika, ta yadda za a kara sada zumunci tsakanin jama’ar birnin Shanghai da Afrika. Shanghai da kasashen Afrika suna da kyakkyawar makomar hada kai.








Birnin Shanghai cibiya ce da ta fi girma ta fuskar tattalin arziki da hada-hadar kudi da cinikayya da kuma sufuri a teku, yana bakin teku na gabashin kasar Sin, ban da wannan kuma yana da sansanin masana’antu da tashoshin jiragen ruwa da suka fi girma a Sin. A shekarar 1985, Shanghai ta kulla dangantakar sada zumunci da birnin Casablanca na Morocco, daga nan, aka fara yin mu’amalla tsakanin birnin Shanghai da biranen kasashen Afrika. Ya zuwa yanzu, birnin Shanghai ya kulla dangankatar sada zumunci da birare 5 na kasashen Afrika, kamar birnin Alexander dake Masar da Windhoek da Okahandja dake Namibiya da Maputo dake Mozambique da kuma lardin KwaZulu-Natal dake Afrika ta kudu. A cikinsu, birnin Okahandja da garin Maqiao na birnin Shanghai sun kulla dangantakar sada zumunci, wanda ba a taba ganin irinta ba a tarihi.

Birnin Shanghai tashar farko ce ta tafiye-tafiyen da wakilan gidan rediyon CRI suka yi a biranen sada zumunta tsakanin Sin da kasashen Afrika, mataimakiyar shugabar ofishin harkokin waje ta Shanghai Madam Wu Jinlan ya shedawa manema labaru yadda birnin Shanghai ya yi mu’amala da biraren da suka sada zumunta da shi. Madam Wu ta ce, kasashen Afirka suna da al’adu iri daban-daban da albarka daga Indallahi sosai, saboda haka, suna da kyakkyawar makomar samun bunkasuwa. Dadin dadawa, Wu Jinlan ta ce, an yi ayyukan sarrafa birane da kiyaye muhalli da kyau a wasu yankuna a Afrika. Birnin Shanghai yana fatan yin hadin gwiwa da kasashen Afrika ta hanyoyi daban-daban. Kawo yanzu dai, ban da biraren da suka kulla dangantakar sada zumunci da birnin Shanghai, kuma Shanghai na kokarin yin mu’amala da sauran biranen kasashen Afrika, cikin har da birnin Tunis da Johannesburg dake kasar Afrika ta kudu da dai sauransu. Shanghai na da kyakkyawar makomar samun bunkasa dangantakar sada zumunci da biraren kasashen Afrika.