Babbar gasar nuna gwaninta mai taken “Ina son in je lardin Sichuan” ta gidan rediyon kasar Sin
Lokacin gasa:
Daga ran 1 ga watan Janairu zuwa ran 1 ga watan Yuli na shekarar 2010
Lambobin yabo:
Za a zabi lambobin yabo na matsayin musamman 10 dake hade da na rubutun bayani 4 da na daukan hoto 3 da kuma na zanen hoto 3. Ban da wannan kuma, wasu za su sami lambobin yabo na matsayin farko da na biyu da kuma na uku. Za a gayyaci wadanda za su samun lambobin yabo na matsayin musamman domin su kawo ziyarar gani da ido a lardin Sichuan na kasar Sin a watan Satumba na shekarar 2010.
Ayyukan gasa:
Wannan babbar gasa ta hada da ayyuka uku wato “rubutun bayani” da “daukan hoto” da kuma “zanen hoto da kayan fasahar aikin hannu”. Kana iya shiga daya daga cikinsu ko kana iya shiga dukkan ayyuka uku na wannan gasa.
A shekarar 2006 da ta 2008, gidan rediyon kasar Sin ya taba shirya gasar kacici-kacici kan batun kara sanin albarkatan yawon shakatawa na lardin Sichuan. A sanadin haka, masu sauraro da masu yin amfani da “yanar gizo” a duk fadin duniya sun riga sun kara sanin halin da lardin Sichuan ke ciki daga fannonin daban daban. Daga ran 1 ga watan Janairu zuwa ran 1 ga watan Yuli na shekarar 2010, gidan rediyon kasar Sin zai sake shirya wata babbar gasa ta nuna gwaninta mai taken “Ina son in je lardin Sichuan”. Masu shiga wannan gasa za su iya tunanin ni’imtattun wurare na lardin Sichuan dake zukatunsu ta hanyoyi iri iri, misali, rubutun bayani da daukan hoto da zanen hoto da kuma yin kayan fasaha da hannu.
Masu jagorantar wannan gasa:Gwamnatin lardin Sichuan ta kasar Sin
Gidan rediyon kasar Sin
Mai shirya wannan gasa:CRI Online
Ka’idar gasa:
Gasar rubutun bayani:  Idan ka taba zuwa lardin Sichuan, sai ka gaya mana me ka sani game da lardin Sichuan, idan ba ka taba zuwa can ba, sai ka rubuta wani bayani kan lardin Sichuan dake zuciyarka.
Rokon gasa:  Kana iya rubuta wani bayani kamar yadda kake so, waka ita ma za ta yi. Amma dole ne ka aiko mana taken wannan bayani da sunanka da asalin kasa da adireshinka tare da bayanin.
Gasar daukan hoto:  Idan ka taba daukan hoto a lardin Sichuan na kasar Sin, sai ka aiko mana, bari mu more tare, kuma za mu nuna hotunanka ga masu yin amfani da “Yanar gizo” a duk fadin duniya. Sai mun ji daga gare ka.
Rokon gasa:  Girman kowane hotonka ba zai wuce 5M ba, kuma dole ne kai da kanka ka dauka wannan hoto, ban da wannan kuma, ya fi kyau ka kara rubuta wani bayanin dake shafar wannan hoto.
Gasar zanen hoto da kayan fasahar aikin hannu:   Kila ne kana tunawa da lardin Sichuan ta hanyar zanen wani hoto ko yin wani aiki na kayan fasaha da hannu, muna fatan za ka aiko mana domin neman samun lambar yabo.
Rokon gasa:  Dole ne ka aiko mana taken hoto ko kayan fasaha da sunaka da asalin kasa da kuma bayanan da abin ya shafa.
Hanyar shiga gasa:   Sai ka aiko mana bayani ko hoto ko kayan fasahar hannu ga adireshi na email ko ta gidan waya, ga:
Hausa@cri.com.cn Kana iya aiko mana aikin gasa ta hanyar latsa nan “Zan shiga” a shafinmu na yanar gizo.
Hausa Service CRI-24
China Radio International
P.O.Box 4216 Beijing
P.R.China 100040
Karin bayani: masu kula da kuma jagorantar wannan gasa na da ikon yin bayani kan ka’idar ita gasa baki daya a sakamakon karshe.