Idan ‘yan makarantar midil ba su yi karin kumallo ba, to, kila ba za su samu maki mai kyau ba

CRI2021-05-30 08:15:38

Idan ‘yan makarantar midil ba su yi karin kumallo ba, to, kila ba za su samu maki mai kyau ba_fororder_u=3361443859,1965039448&fm=26&fmt=auto&gp=0

Masu nazari na kasar Birtaniya sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya cewa, idan an kwatanta su da wadanda su kan yi karin kumallo kullum, to, ‘yan makarantar midil wadanda ba safai su kan yi karin kumallo ba, ba su samu maki mai kyau cikin jarrabawa ba.

Masu nazarin daga jami’ar Leeds ta kasar Birtaniya sun gudanar da bincike kan ‘yan makaranta 294 wadanda shekarunsu suka wuce 16 amma ba su kai 19 a duniya ba, suna kuma zama a yankin West Yorkshire, inda suka gayyace su waiwayi yadda suka yi karin kumallo a lokacin da suke karatu a makarantar midil. Masu nazarin sun gano cewa, kaso 29 na wadannan ‘yan makaranta ne ba safai su kan yi karin kumallo ba har ma wasu ba su yi karin kumallo baki daya. Kaso 18 daga cikinsu kan yi karin kumallo lokaci-lokaci, sa’an nan kaso 53 daga cikinsu su kan yi karin kumallo kullum.

Masu nazarin sun yi la’akari da matsayinsu a zamantakewar al’ummar kasa, kabilansu, shekarunsu na haihu, jinsinsu da dai sauransu baki daya, sun gano cewa, idan an kwatanta su da wadanda su kan yi karin kumallo kullum, to, wadanda ba safai su kan yi karin kumallo ba, ba su sami maki mai kyau cikin jarrabawar GCSE da ake gudanarwa tsakanin ‘yan makarantar midil a duk fadin Birtaniya ba. Jarrabarwar GCSE, wata jarrabawa ce da ake gudanawa tsakanin dukkan ‘yan makarantar midil na kasar Birtaniya don su kammala karatu daga makarantar midil. An raba makin da ‘yan makarantar midil suka samu cikin jarrabawar zuwa matsayi daban daban har guda 9.

Dangane da yadda yin karin kumallo yake taka rawa a fannin karatu, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, “Yin karin kumallo yadda ya kamata da sanyin safiya yana iya samar wa kwakwalwar matasa kuzari isasshe kafin su fara karatunsu a kowacce rana. Don haka idan matasa ba su yi karin kumallo yadda ya kamata ba, to, zai kawo illa ga makin da za su samu.” (Tasallah Yuan)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)