Motsa jiki kullum ko a’a ya danganta da halayyar musamma ta mutane

CRI2021-03-10 09:36:33

Motsa jiki kullum ko a’a ya danganta da halayyar musamma ta mutane_fororder_u=1218756581,636921978&fm=26&gp=0

Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya gano cewa, bambancin da ke tsakanin mutane wajen daukar matakai bisa shiri, ya sanya abubuwan da suka yi a zaman rayuwar yau da kullum sun sha bamban. In an kwatanta su da wadanda ba su tsara shiri kafin su dauki matakai ba, mutanen da su kan tsara shiri don cimma manufa ta dogon lokaci sun gwanance wajen motsa jiki kullum. An kaddamar da sakamakon nazarin cikin mujallar ilimin sanin halayyar bil Adam ta kasar Amurka.

Dangane da halayyar musamma ta mutane, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani da cewa, a kan siffanta halayyar musamman ta mutane daga fannoni guda 5, ciki had da ko mutum na aiki tukuru bisa tsari, ko kowa ya amince da ita ko shi, hakan ana zaton cewa, yana da nasaba da aikace-aikacen mutane masu dacewa.

Masu nazari daga jami’ar Oregon sun rubuta yadda masu aikin sa kai 282 suka motsa jiki cikin makanni 20 a shekarar 2018, tare da tattara bayanan da suka shafi yadda suka motsa jiki a shekarar 2017. Ban da haka kuma, wadannan masu aikin sa kai sun gabatar da shirinsu na motsa jiki, sun kuma cika wata takardar tambaya dangane da ko za su tsara shiri kafin su fara daukar matakai ko a’a, da kuma ko za su dauki matakai bisa shirin da suka tsara.

A karshe an gano cewa, masu aikin sa kan wadanda suka tsara shiri kafin su fara daukar matakai, ko su kan dauki matakai bisa shirin da suka tsara, sun fi wadanda ba su mai da hankali kan tsara shiri ko kuma daukar matakai bisa shiri ba, motsa jiki kullum. A lokacin kaka, sun fi zuwa dakin motsa jiki sau 5.9, yayin da suka fi zuwa dakin motsa jiki sau 8.5 a lokacin sanyi.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, nazarin da suka yi ya taimaka wajen kara sanin tasiri da bambancin halayyar mutane yake bayarwa kan yadda suke yin abubuwa.   (Tasallah Yuan)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)