Xun
中国国际广播电台

Kayan sarewa mai suna Xun shi ne daya daga cikin kayayyakin sarewa na tsohon zamani na da, kuma tsawon tarihin wannan kayan sarewa mai suna Xun ya kai fiye da shekaru dubu 7. Daga tsohon zamani na da, wato a wancan lokaci, mutanen da ba su iya yin zaman yau da kullun kamar na yanzu haka ba, wato ba su da kayayyakin neman samu abinci kuma ba su iya yin shuke shuke, sai su da hannunsa sukan kama dabbobin daji kawai, a karshe dai sun yi amfani da duwatsu masu kewaye don jefa wa dabbobin daji da kame su don neman samu namansu.Irin wannan kayan sarewa mai kewaye haka, , a karshe dai an haka ramuka a kansa, sai an iya yin bushe bushe masu dadin ji.

Daga baya, sigoggin irin kayan sarewa daban daban ne, amma yawacinsu masu kewaye ne.

A tsohon zamani, a fadar sarkin kasa, in kungiyar makada sun yi kide kide da kyau, a cikin ba shakka akwai irin kayan sarewa mai suna Xun da aka yi amfani da su wajen nuna wasannin opera iri iri

Daga shekaru 20 zuwa 30 na karnin da ya shige, wani farfesa na kolejin koyon kide kide na kasar Sin ya fara yin wannan kayan sarewa da tangaram, a karshe dai ya sami babban sakamako.(Dije)

Saurari: Wakar Chu