中国国际广播电台
Zhang Heng an haife shi ne
a gundumar Nanyang ta lardin
Henan a tsakiyar kasar Sin.
Tun lokacin da ya ke yaro
ne ya yi kokari a wajen karatu,
kuma ya gwanance a wajen wallafe
wallafe. A lokacin da ya ke
da shekaru 17 da haifuwa ne
ya bar garinsu ya je Changan,
wato birnin da ya zama hedkwatar
kasa na sarauta da dama a
kan tarihin kasar Sin. A nan
Zhang Heng ya yi bincike da
nazarin abubuwan tarihi, ya
bincike al’adun jama’a da
tattalin arzikin zaman tarayya.
Daga bisani gwamnati na wancan
zamani ta nada shi ya zama
jami’I na Luoyang, daga baya
kuma ya kama sauran mukamai.
Zhang Heng ya yi sha’awar
ilmin halitta kwarai da gaske,
amma ba ya sha’awar suna da
riba, ya yi murabus har sau
biyu. Ya yi shekaru 3 yana
bincike firosufiya da lissafi
da ilmin sararin sama, ya
samu ilmi da yawa, kuma ya
fara wallafa littafi.
A zamanin sarautar Han wato
kafin shekaru dubu 2, akwai
hasashe da dama game da samaniya.
A ganin Zhang Hen, duniya
ta yi kama da kwai, kasar
da mu ke zaune ta yi kama
da rawayan kwai, samaniya
ta fi kasa girma. Wannan ra’ayinsa
yana da ci gaba kwarai a wancan
zamani. A ganinsa tun can
farko duniya a harhade ta
ke, amma daga baya, abubuwa
maras nauyi sun yi sama sun
zama samaniya, abubuwa masu
nauyi sun nutsa har sun zama
kasa. A ganinsa nisan da ke
tsakanin taurari ne ya kudura
saurin tafiyar taurari.
Zhang Heng bai bincike hasashe
kawai ba, kuma ya sa muhimmanci
a wajen yin aikatawa. Shi
kansa ne ya bincike da kera
kayayyaki da yawa na auna
sararin sama da kasa. Misali
ya kago wata na’urar auna
girgizar kasa. A shekara ta
138, wannan na’urar auna girgizar
kasa ta yi nasarar auna girgizar
kasa da aka yi a lardin Shanxi.
Zhang Heng kuma ya bincike
ilmin sararin sama da yawa.
Misali ya ce, a tsakiyar kasar
Sin ana iya gani taurari misali
dubu 2 da 500. A ganin zhang
Heng, ko da ya ke da safe
da yamma, in an duba rana,
ta yi girma, amma da tsakar
rana ta yi karama, amma hasali
ma daya ne, domin da sassafe
da magariba, duniya ta yi
dan duhu. Amma da tsakar rana,
da haske da yawa, shi ya sa
an yi tsammani rana ta yi
karama. Misali in an duba
wuta da dare, ta kan yi girma,
amma da rana ta kan yi karama.
Irin wannan ra’ayin Zhang
Heng yana da gaskiya.
Zhang Heng kuma ya bincike
ilmin sararin sama da yawa.
Misali ya ce, a tsakiyar kasar
Sin ana iya gani taurari misali
dubu 2 da 500. A ganin zhang
Heng, ko da ya ke da safe
da yamma, in an duba rana,
ta yi girma, amma da tsakar
rana ta yi karama, amma hasali
ma daya ne, domin da sassafe
da magariba, duniya ta yi
dan duhu. Amma da tsakar rana,
da haske da yawa, shi ya sa
an yi tsammani rana ta yi
karama. Misali in an duba
wuta da dare, ta kan yi girma,
amma da rana ta kan yi karama.
Irin wannan ra’ayin Zhang
Heng yana da gaskiya.
Zhang Heng ba masanin ilmin
sararin sama kawai ba, kuma
shahararren mawallafi ne na
zamanin Donghan, kuma ya gwanance
a wajen zane. Shi ne daya
daga cikin shahararrun masu
zane 6 na wancan zamani. Bisa
lissafin da aka yi an ce,
Zhang Heng ya wallafa littatafai
har 32 don nuna ra’ayinsa
game da ‘yan Adam da karatu.
A cikin littatafan da ya wallafa
kuma ya siffanta al’amura
na wancan zamani wadanda su
ke da daraja kwarai a wajen
bincike tarihi na wancan zamani.
(Dogonyaro)
|