Gasar kacici-kacici ta murnar "cika
shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin"

Shekarar da ake ciki shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A cikin shekaru 60 da suka gabata, gwamnati da jama'ar kasar Sin sun dukufa ka'in da na'in wajen raya kasar. Sabo da haka, karfin kasar Sin ya samu dagawa sosai. Ingancin zaman rayuwar jama'a ma ya samu kyautatuwa a kai a kai. An kuma samu babban ci gaba a fannoni daban daban, kamar su fannonin masana'antu da aikin gona da kuma kimiyya da fasaha da dai sauransu. Tashar CRI za ta shirya "gasar kacici-kacici ta murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin" ta rediyo da yanar gizo domin kara wa masu sauraronmu sanin sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da dai sauransu.

Wa'adin karbar amsoshinku: Tun daga ran 1 ga watan Yuni zuwa ran 1 ga watan Satumba na shekara ta 2009
Tsarin gasar´╝ÜGasar ta kunshi "amsa tambayoyi", da rubuta "fatan alheri ga kasar Sin"
Akwai tambayoyi guda 10 a kan Internet, za mu dudduba amsoshinku, duk wanda ya gabatar da amsa yana da damar samun lambar yabo.

Abin kyauta:
Lambar yabo ta musamman: Akwai mutane 10 za su sami lambar yabo ta musamman, duk wadanda suka sami lambar yabo ta musamman za su iya samun damar kawo ziyarar gani da ido a nan kasar Sin
Lambar yabo ta farko: Za mu ba ku abin kyauta na zane-zane da aka yi da siliki na kasar Sin
Lambar yabo ta biyu: za mu ba ku kayayyakin saka na kasar Sin
Lambar yabo ta uku: za mu ba ku tufafin wasa
Za mu buga sunayen wadanda da suka ci lambar yabo a shfinmu na Internet na CRIPlay
©China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040