Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-05-15 16:54:38    
An yi taron musayar ra'ayoyi kan batun hakkin bil Adam tsakanin Sin da Amurka cikin halin da ya dace

cri
A ran 13 da ran 14 ga wata, kasashen Sin da Amurka sun yi taron musayar ra'ayoyi kan batun hakkin bil Adam, inda bangarorin biyu suka ba da dalilin cewa, sun yi wannan taro ne a sahihanci kuma a fili cikin halin da ya dace.

Mr. Chen Xu, direktan hukumar kula da harkokin kasa da kasa a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da Mr. Michael Posner, mai ba da taimako ga sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka wanda ke kula da harkokin bil Adam suka shugabanci wannan taro, inda bangarorin Sin da Amurka suka sanar wa juna sabon ci gaban da suka samu a fannin kiyaye hakkin bil Adam, kuma suka yi musayar ra'ayoyi sosai kan batutuwa da yawa, kamar su batun yin hadin gwiwa game da zancen hakkin bil Adam a majalisar dinkin duniya da na aiwatar da ikon mulkin kasa bisa dokoki da batun bayyana ra'ayoyin jama'a cikin 'yanci da na kiyaye ikon 'yan kwadago da kuma batun tinkarar magance nuna bambancin launin fata da dai makamatansu.

Bangaren Sin ya bayyana cewa, yana son ci gaba da yin musayar ra'ayoyi da yin mu'ammala da kasar Amurka a fannin hakkin bil Adam bisa ka'idojin zaman daidai wa daida da girmamawa juna domin kara fahimtar juna da sassauta ra'ayoyi daban daban da ke kasancewa a tsakaninsu da kuma kara neman ra'ayi daya. Sannan bangaren Amurka ya yaba wa kasar Sin game da sabon ci gaban da ta samu a fannin hakkin bil Adam. Kuma zai yi kokarin yin musayar ra'ayoyi da yin mu'ammala da kasar Sin a fannin hakkin bil Adam. (Sanusi Chen)