Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 11:05:51    
Mukaddashin shugaba na kasar Afrika ta kudu Kgalema Motlanthe ya gana da Wang Zhaoguo

cri

A ran 4 ga wata da yamma, mukaddashin shugaba na kasar Afrika ta kudu Kgalema Motlanthe ya gana da memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma mataimakin shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Wang Zhaoguo.

Da farko, Wang Zhaoguo ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Hu Jintao da mataimakin shugaban kasar Xi Jinping. Ya ce, a cikin shekaru 11 da kasashen Sin da Afrika ta kudu suka kulla huldar diplomasiyya, kasashen biyu sun zama abokai bisa manyan tsare-tsare. Kwanan baya, shugaban kasar Sin Hu Jintao da shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma sun cimma sabuwar matsaya daya kan kara karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a dukkan fannoni a wajen taron MDD na 64 na birnin New York. Kasar Sin tana son tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka samu da ci gaba da karfafa hadin gwiwarsu don daga matsayin hadin gwiwa da kara samun bunkasuwar huldarsu mai kyau.

Kgalema Motlanthe ya amince da shawarar da Wang Zhaoguo ya bayar kan aikin bunkasa huldar dake tsakanin kasashen Afrika ta kudu da Sin. Ya ce, kasar Afrika ta kudu tana son ci gaba da bunkasa huldarta da kasar Sin da kara hadin gwiwa a dukkan fannoni don ingiza bunkasuwar huldarsu. Ya kuma kara da cewa, jam'iyyar ANC ta Afrika ta kudu tana son kara musanyar ra'ayi tare da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.(Lami)