Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 10:49:21    
A ganin Kasar Amirka gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ta yi ba ya bisa doka ba

cri

A ran 4 ga wata, a Alkahira, madam Hilary Clinton, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amirka dake ziyarar kasar Masar ta bayyana cewa, a ganin kasar Amirka, gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ta yi ba ya bisa doka ba, kuma tana fatan Isra'ila za ta daina gina matsugunan Yahudawa.

Bayan da ta gana da shugaban kasar Masar Mohamed Hosni Moubarak, madam Hilary Clinton ta gaya wa manema labaru cewa, Amirka ba ta canja manufarta dangane da matsugunan Yahudawa ba, kuma ba ta amince da halalta gina matsugunan Yahudawa ba, kana tana tsayawa kan ra'ayinta cewa kamata ya yi a daina gina dukkan matsugunan Yahudawa, ba kawai matsugunan da ake ginawa a yanzu ba, har ma wadanda za a gina a nan gaba.

A gun hadadden taron manema labarun da ta yi tare da takwaranta na Masar Ahmed Aboul Gheit, madam Hilary Clinton ta ce, ya kamata tattaunawar da za a yi game da yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ta kasance kunshe da batun matsayin Jerusalem na karshe.(Asabe)