Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 09:59:39    
Kamfanin CIT na kasar Amirka yana neman kariya daga durkushewa

cri

A ran 1 ga wata, domin ya kasa samun taimako daga gwamnatin kasar da yin garambawul ga basusuka, kamfanin CIT, hukuma wadda ke da tarihi na shekaru dari daya kuma mafi girma a Amirka wajen ba da rancen kudi ga masana'antu matsakaita da kanana yana neman kariya daga durkushewa.

Batun durkushewar kamfanin CIT shi ne daya daga cikin batutuwan durkushewar masana'antu masu girma a tarihin kasuwanci na kasar Amirka. Kafin rugurgujewar kamfanin, yawan jarinsa ya kai dala biliyan 71, kuma yawan basusukansa ya kai dala biliyan 64.9.

Kamfanin ya ba da sanarwar cewa, bayan da masu bin bashi na kamfanin suka cimma matsaya daya, kamfanin ya nemi kariya daga durkushewa daga wata kotun kula da harkokin durkushewar kamfanoni na yankin kudu na birnin New York. Amma kamfanonin dake karkashin kamfanin CIT ciki har da bankin CIT na jihar Utah za su ci gaba da aiki yadda ya kamata.(Asabe)