Ranar 31 ga watan Oktoba da dare, a cibiyar al'adu da fasahohi ta Al-Assad dake birnin Damascus na kasar Syria, an kaddamar da bukin nunin fim na kasa da kasa a karo na 17, wanda ya yi suna sosai a yankin Gabas ta Tsakiya.
Za'a shafe tsawon kwanaki 8 ana wannan buki, wanda kuma zai samu halartar wasannin fina-finai 275 daga kasashe da yankuna 52, a karshe dai za'a bayar da lambobin yabo na zinariya, da azurfa da tagulla, tare kuma da fitar da fim din harshen Larabci mafi nagarta.
Har wa yau kuma a yayin bukin, za'a shirya aikin "Palestine a wasannin fina-finai", a kokarin nuna wasannin fina-finai 8 dake shafar Palestine, da gudanar da taron karawa juna sani kan wasannin fina-finai na Palestine.(Murtala)
|