Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-29 09:34:53    
Kasashen duniya sun sa kaimi ga Amurka da ta dakatar da kangiya kan Cuba

cri
A ran 28 ga wata, babban taron MDD a karo na 64 ya zartas da daftarin kudurin "Dole ne a dakatar dasanya takunkumi da Amurka ta yiwa Cuba a fannin tattalin arziki da masana'antu da hada-hadar kudi" bisa samun yawancin kuri'un da aka kada, a yunkurin sa kaimi ga Amurka da ta daina sanya takunkumi ga kasar Cuba.

Wannan ne jerin shekaru 18 da aka zartas da irin wannan kuduri.

A wannan rana kuma, yayin da yake yin jawabi a babban taron, zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Yesui ya bayyana cewa, kowace kasa mai 'yanci na da ikon zaben tsarinta na zamantakewar al'umma da hanyar samun bunkasuwa da ya dace da halin kasar cikin 'yanci. Kuma kowace kasa ba ta da ikon kakabawa sauran kasashen duniya takunkumi ta aikin soja da siyasa da tattalin arziki da dai makamantansu. A halin yanzu da duniya take fuskantar rikice-rikice da dama, kangiya da takunkumin da Amurka ta sanya wa kasar Cuba sun fi tsanani fiye da da.

Dadin dadawa, a wannan rana, shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya furta cewa, kamata ya yi shugaban Amurka Barack Obama ya kawo karshen takunkumi da Amurka ta yiwa Cuba na tsawon shekaru 47, zai tsaida kudurin da ya dace da matsayinsa mai karbar lambar yabo ta Nobel.(Fatima)