Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-28 09:23:38    
Hadin gwiwa da Sin da Afrika suke yi ya amfanawa bunkasuwar tattalin arzikin Afrika

cri
A ran 27 ga wata, ministan harkokin waje na Kenya Mr Moses Wetangula ya furta cewa, Sin da kasashen Afrika sun sami sakamako mai kyau ta fuskar hadin gwiwa da suka yi, wanda kuma ya kara kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika.

Kafin ya aiyarce Massar domin halartar taron ministoci na 4 na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, Wetangula ya bayyana cewa, tun lokacin da aka yi taron koli na Beijing na dandalin a 2006, Sin da kasashen Afirka sun sami ci gaba da dama a fannin hadin gwiwa. Zuwa yanzu dai, kasashen Afrika da dama suna hada kai da Sin kan ayyuka da yawa, ban da wannan kuma Sin ta zuba jari ga ayyuka da dama da kasashen Afrika suke yi. Wasu ayyuka, musamman ma a fannin gina manyan gine-gine da taimako ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika.

Dadin dadawa, Wetangula yana fatan kasar Sin za ta kara hada kai tare da Kenya ta fuskar cinikayyar amfanin gona. A sa'I daya, gwamantin Kenya tana fatan kara yin mu'amala da Sin a fannin yawon shakatawa.(amina)