Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 11:10:01    
Kasar Sin ta kulla yarjejeniyar hadin kai ta fuskar fasahohin tattalin arziki da kasar Togo

cri
A ran 26 ga wata a birnin Lome na Togo, gwamnatin Sin da ta Togo sun sa hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin fasahohin tattalin arziki, kuma sun yi musayar takardu kan batun taimakawa Togo wajen hakan rijiyoyi 200.

Bisa yarjejeniyar da aka kulla, gwamnatin Sin za ta ba da tallafin kudi Yuan miliyan 60 kyauta ga gwamnatin Togo domin kaddamar da ayyukan da bangarorin biyu za su yi.

Ministan kula da hadin gwiwa da bunkasuwa da kuma harkokin kyautata yankunan kasar na Togo Mr Gilber Bawara ya darajanta dangantakar hadin gwiwa ta duk fannoni dake tsakanin Sin da Togo a yayin bikin sa hannu, inda ya ce, yana fatan kasashen biyu za su yi hadin gwiwa ta fuskar kiwon lafiya da sha'anin noma da manyan gine-gine da makamatansu.

Jakadan Sin dake Togo Mr Yang Min ya shedawa manema labaru bayan bikin cewa, kulla yarjejeniya da takardun musanya da aka yi ya kara bayyana kyakyawan fatan gwamnatin kasar Sin na yin hadin gwiwa da gwamantin Togo, bugu da kari, wannan ya bayyana yadda gwamantin Sin ta tabbatar da matakai 8 da ta gabatar a taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a 2006, kuma ya bayyana cewa, Sin tana cika alkawarinta ta hanyar ba da tallafi ga abokanta kasashe Afrika.(amina)