Kasashen kungiyar kawancen tattalin arziki da kudi na yammacin Afirka guda 8 za su fitar da katin visa na bai daya a fannin yawon shakatawa don sa kaimi ga bunkasuwar yawon shakatawa ta kasashen dake cikin kungiyar.
A gun bikin rufe taron yawon shakatawa na duniya a karo na biyu da aka yi a Bamako, babban birnin kasar a ran 22 ga wata, ministan kula da harkokin sana'o'in hannu da yawon shakatawa na kasar Mali N'diaye Bah ya bayyana cewa, kasashe 8 na kungiyar suna yunkurin bullo da katin visa na bai daya a fannin yawon shakatawa a cikin 'yan shekarun nan don ba da taimako ga mutanen kasashen kungiyar dake tafiye-tafiye a kasashen cikin 'yanci, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar sana'ar yawon shakatawa.
An kafa kungiyar kawancen tattalin arziki da kudi ta yammacin Afika a shekarar 1994, wadda ta hada da kasashen Benin da Burkina Faso da Cote D'ivoire da Mali da Nijer da Senegal da Togo da kuma Guinea Bissau.(Zainab)
|