Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-23 10:18:50    
Mai yiyuwa ne tattalin arzikin kasar Afrika ta kudu zai ragu da kashi 2 cikin dari

cri
A ran 22 ga wata, ministan kudi na kasar Afrika ta kudu Pravin Gordhan ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne yawan GDP na kasar Afrika ta kudu a shekarar bana zai ragu da kashi 2 cikin dari, wannan ne karo na farko da tattalin arzikin kasar ya rage saurin karuwa bayan shekarar 1992.

Mista Gordhan ya ce, a cikin shekaru biyar da suka gabata, tattalin arzikin kasar ya kyautata, kuma karuwar tattalin arzikin kasar a kowace shekara ta kan kai kashi 5 cikin dari. Amma sakamakon matsalar kudi ta duniya, mai yiyuwa ne, tattalin arzikin kasar zai rage saurin karuwa a bana.

Bugu da kari, mista Gordhan ya furta cewa, duk da cewar matsalar kudi ta samo asali ne daga kasashe masu ci gaban masana'antu, amma sakamakon yaduwarta a duk fadin duniya, ta kawo illa ga kasashe masu tasowa da dama. Dadin dadawa, ya yi nuni da cewa, a shekarun baya, kafin abkuwar matsalar kudi, tattalin arzikin yankin Afrika ya rike karuwa da kashi 6 cikin dari a kowace shekara. Amma ana nuna damuwa cewa, karuwar tattalin arziki zai wuce kashi 1 cikin dari ne kawai a bana.(Asabe)