Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-23 09:23:57    
Kawancen kasashen Turai zai kara yin hadin kai da kasashen Afrika ta fuskar sufuri

cri
A ran 22 ga wata, kwamitin kawancen kasashen Turai, EU ya sanar da cewa, zai kara yin hadin kai da kasashen Afrika ta fuskar harkokin sufuri, ta yadda za a samu damar kyautata halin sufuri na Afrika da taimakawa kasashen Afrika wajen bunkasa tattalin arziki.

A wannan rana, kwamitin EU ya gabatar da shirin kara yin hadin kai tsakaninsa da kasashen Afrika kan harkokin sufuri a dandalin harkokin sufuri na nahiyoyin Turai da Afrika da aka yi a Naples dake kasar Italiya. Bisa labarin da aka bayar, an ce, wannan shiri zai taimakawa kasashen Afrika wajen kyautata yanayin ababen hawa da kuma kirkiro wani kyakkyawan sharadin yin zirga-zirga cikin kwanciyar hankali da zummar bunkasa tattalin arzikinsu ta hanyar tallafa musu da tarayyar Turai za ta yi.

Mataimakin shugaban kwamitin EU Antonio Tajani ya furta cewa, mumunan yanayin sufuri da kasashen Afrika suke ciki yana kawo cikas ga bunkasuwar tattalin arzikinsu, saboda haka, kara yin hadin gwiwa tsakanin EU da kasashen Afrika a fannin sufuri zai taimakawa kasashen Afrika wajen zama muhimman abokan ciniki na EU.(amina)