|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-10-22 09:52:55
|
Farashin man fetur ya karu zuwa dala 81 ko wace ganga a ran 21 ga wata
cri
A ran 21 ga wata, saboda yawan cinikin man fetur da aka tanada a Amurka ya ragu fiye yadda aka yi tsamani, farashin man fetur na kasa da kasa ya karu har ya zarce dala 81 a ko wace ganga.
Bisa sabbin alkaluman da hukumar samar da bayanan makamashi ta Amurka ta bayar, an ce daga ran 9 zuwa 16 ga watan Octoba, yawan cinikin man fetur da aka tanada a Amurka ya ragu da ganguna miliyan 2.3 wanda ya fi yadda masu bincike suka yi hasashe yawa. A sa'i daya, da yake yawan gurbataccen man fetur da aka tanada ya karu da ganguna miliyan 1.3, amma bai kai ganguna miliyan 1.8 da aka yi tsammani a kasuwa ba, hakan ya sa farashin man fetur ya karau bayan da aka gabatar da rahoton.(amina)
|
|
|