Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-12 15:31:23    
An kaddamar da taron hadin gwiwa na kwalejojin Confucius na yankin Afirka na shekarar 2009 a birnin Nairobi

cri

A ran 12 ga wata, an kaddamar da taron hadin gwiwa na kwalejojin Confucius na yankin Afirka na shekarar 2009 a birnin Nairobi. Kuma wakilai fiye da dari daya daga kwalejojin Confucius 23 na kasashe 16 na Afirka sun halarci taron.

Shugabar ofishin yada harshen Sinanci a kasashen duniya na kasar Sin kuma babbar direktar cibiyar kwalejin Confucius Xu Lin da mataimakin ministar kula da harkokin ilmi da kimiyya da fasaha ta kasar Kenya Kilemi Mwiria sun halarci taron.

Madam Xu Lin ta yi wani jawabi mai babban take a gun bikin kaddamarwar, inda ta furta cewa, lallai an sha wahala sosai yayin da ake kafa kwalejojin Confucius a nahiyar Afirka idan aka kwatanta yadda ake yi a sauran wasu yankuna masu ci-gaban tattalin arziki, wato ke nan wajibi ne a kara yin kokari. Tana fatan wakilai masu halartar taron za su yi musayar fasahohi da yin nazari ta hanyar wannan taro don warware matsalolin da ake fuskanta a yanzu a fannonin kaddamar da kwalejin Confucius da kuma ba da ilmi, kana tana fatan kwalejojin Sin za su yi amfani da wannan dama, da yin tattaunawa kan yadda za a samu ci gaba tare da kwalejojin Confucius na Afirka don ba da kyakkyawar hidima ga abokai a Afirka.(Zainab)