Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-01 15:19:46    
Kwararru a fannin wasannin fasaha na kasar Sin sun nishadantar da 'yan kallo don taya murnar ranar kafuwar kasashen Sin da Nijeriya

cri

A ran 30 ga watan Satumba, a otel din Hilton na birnin Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, mutame masu wasan fasaha da suka fito daga kungiyar wasan fasaha ta hukumar jiragen kasa ta kasar Sin sun nishadantar da  'yan kallo don taya murnar ranar kafuwar kasashen Sin da Nijeriya.

Ran 1 ga watan Oktoba ranar taya murna ce ta kafa sabuwar kasar Sin a karo na 60, kuma rana ce ta murnar samun 'yanci a karo na 49 na kasar Nijeriya. Sabo da haka, wasan da kwararru a fannin wasannin fasaha na kasar Sin suka yi ta kyautata hulda a tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Jakadar kasar Sin da ke kasar Nijeriya Xu Jianguo ya bayyana cewa, mun yi kokari wajen shirya wannan biki, a sa'i daya kuma, jama'ar Nijeriya sun mai da hankali a kan bikin murnar kafuwar sabuwar kasar Sin, wannan ya shaida kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Bisa wannan tushe, dangantakar za ta samu bunkasuwa sosai a 'yan shekaru masu zuwa.

Ministan kula da harkokin yawon shakatawa da harkokin al'adu na kasar Nijeriya ya bayyana cewa, wasan da kwararru a fannin wasannin fasaha na kasar Sin suka yin dan nishadantarwa yana da kyau, daga wannan wasa ya ga al'adu daban daban na kasar Sin, kuma yana fatan za a sake gayyatar kungiyar wasan fasaha ta kasar Sin don zuwa birnin Nijeriya ta nishadantar da 'yan kallo.(Abubakar)