A ran 27 ga wata da dare, an kaddamar da taro kan yawan mutane na duniya a karo na 26 a birnin Marrakech dake kudancin kasar Morocco. Masana da kwararru kan ilmin yawan mutane da kidayar jama'a fiye da dubu 2 da suka fito daga kasashe da yankuna 114 sun halarci taron. Wannan ne karo na farko da aka gudanar da taron a wata kasa dake nahiyar Afirka.
A taron kwanaki 5, masu halartar taron za su tattauna cikin kungiya-kungiya kan batutuwa fiye da dari 2 a game da makomar jama'ar duniya, ciki har da dangantaka tsakanin batun yawan mutane da sauye-sauyen yanayi, da tsakanin kaurar mutane a duniya da rikicin tattalin arziki, da kuma tsakanin yawan mutanen da aka Haifa da tsarin jin dadi na zamantakewar al'umma. An yi tattaunawa da nune-nune kan batutuwan da dama game da yawan mutane a wurin taron.(Zainab)
|