Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-01 14:06:54    
Bangarori suna sanya ran samun sakamako a taron koli na hada-hadar kudi

cri
A ran 31 ga watan Maris, kafin taron koli na hada-hadar kudi, shugabannin wasu kasashe da na kungiyoyin duniya sun bayyana cewa, suna fatan za a sami sakamako a gun taron kolin, domin ba da gudummawa wajen daidaita matsalar kudi da kafa tsarin hada-hadar kudi mai adalci a duniya.

Firaministan Birtaniya Gorden Brown ya ba da jawabi a birnin London cewa, dole ne taron koli na kasashe masu karfin tattalin arziki 20 ya yi imani ga tattalin arzikin duniya, kuma ya kawo sabon fata ga jama'ar kasa da kasa.

Jose Manuel Barroso, shugaban kungiyar tarayyar Turai ya bayyana a Brussels cewa, dole ne G20 ta yaki manufar kariyar cinikayya a bayyane. A sa'i daya, Barroso ya yi kira ga G20 da ta yi amfani da asusun ba da lamuni na duniya domin taka muhimmiyar rawa.

Babban darektan kungiyar WTO Pascal Lamy ya bayyana a Geneva cewa, kamata ya yi shugabannin G20 su jaddada matsayi na yaki da manufar kariyar cinikayya.

Shugaban bankin duniya Robert Zoelik ya furta cewa, yayin da shugabanni masu halartar taro suka tinkari matsalar kudi, kada su manta da jama'a masu fama da talauci a kasashe masu tasowa da matsalar kudi ta fi yin illa.(Fatima)