Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-23 20:09:16    
Ya kamata rukunin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki ya kafa tsarin sa ido kan shirin sa kaimi ga tattalin arziki

cri

A ranar 22 ga wata, yayin da shugaban bankin duniya Robert Zoellick ya halarci taron tattaunawa na Brussels, ya ba da shawara cewa, kamata ya yi rukunin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki ya yi la'akari da kafa wani tsarin sa ido domin tantance sakamakon da suka samu wajen sa kaimi ga tattalin arziki.

Zoellick ya ce, ya kamata taron koli na rukunin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki kan hada-hadar kudi da za a yi a ranar 2 ga watan Afril a birnin London ya yi la'akari da kafa wani tsarin sa ido, sabo da yawancin kasashe za su ci gaba da aiwatar da shirin sa kaimi ga tattalin arziki da suke aiwatarwa a yanzu zuwa ga shekarar 2010, dole ne bayan da aka tantance sakamakon da kasashen duniya samu, a yanke shawara ko za a ci gaba da daukar matakai da suke dauka a yanzu.

Zoellick ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su kafa tsarin kansu, don ba da tabbaci ga shirin sa kaimi ga tattalin arziki, kana kuma yayin da suke daukar matakai wajen sa kaimi ga tattalin arziki, dole ne su yi la'akari da yawan gibin kudaden da suka samu.

A sa'i daya kuma, Zoellick ya yi kashedin cewa, shekarar bana, shekara ce da aka fi fama da rikicin tattalin arziki, ya kimanta cewa, tattalin arzikin duniya zai ragu da kashi 1 ko kashi 2 cikin kashi 100, kuma ba a taba ganin irin raguwa ba tun bayan da shekaru 30 na karnin da ya wuce, watau lokacin da aka fama da mumunan rikicin hada-hadar kudi a dukkan duniya.(Bako)