Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 11:05:55    
Kasar Sin tana kare yancin bin addini cikin sahihanci

cri

A ran 3 ga wata, jaridar People's Daily ta bayar da wani bayanin da mataimakin shugaban hukumar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin Ye Xiaowen ya yi. Bayanin ya ce, kasar Sin tana kare yancin bin addini cikin sahihanci.

Tun daga watan Mayu na shekarar 1995 zuwa watan Satumba na shekarar 2009, malam Ye Xiaowen ya kasance shugaban hukumar kula da harkokin addinai ta kasar Sin. Malam Ye Xiaowen ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana girmamawa hakkin jama'ar kasar na bin addini cikin yanci bisa al'adun gargajiya na dogon tarihi da hakikanin bukatar Sin ta kafa zaman al'umma mai jituwa.

Ye Xiaowen ya furta cewa, sakamakon kokarin aiki da aka yi, Sin ta ba da isasshen tabbaci ga hakkin jama'ar kasar na addini cikin yanci. A halin yanzu dai, yawan masu bin addinai na kasar Sin ya kai miliyan dari daya ko fiye, yawan malaman masu bin addinai ya kai kimanin dubu 360, kuma yawan wuraren da ake aiwatar da aikace-aikacen addinai ya kai kimanin dubu 130, kana yawan kungiyoyin bin addinai ya kai dubu 5 da dari 5, ban da haka kuma, yawan kwalejojin koyar da addinai ya zarce 110. Dukkan kungiyoyin addinai sun buga jaridu da litattafansu, kuma sun buga litattafan addinai da dama.(Asabe)