Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 09:21:15    
Manufar tattalin arzikin Sin da yawan kudin musanya na RMB da kudaden kasashen waje za su ci gaba da tsayawa da gindinsu

cri
A ran daya ga wata a birnin Guangzhou, ministan ciniki na kasar Sin mista Chen Deming ya bayyana cewa, manufar tattalin arziki ta Sin da yawan kudin musanya na RMB da kudaden kasashen ketare za su ci gaba da tsayawa da gindinsu, wadanda za su kawo alheri ga ci gaban kamfanoni da masana'antu na kasar Sin.

Yayin da yake hira da 'yan jarida, Chen Deming ya yi nuni da cewa, yanzu cinikayyar da Sin take yi da kasashen ketare tana fara karuwa. Duk da haka, tana fuskantar abubuwa da dama marasa tabbas da dorewa. A sakamakon haka, mista Chen ya jaddada cewa, yanzu manufar tattalin arziki ta Sin a manyan fannoni za ta ci gaba da tsayawa da gindinta, ciki har da manufar kasafin kudi mai yakini da manufar kudi mai sassauci, tare da yin gyare-gyare kadan ga tsari da hanyar da babban fannin zuba jari.

A sa'i daya, Chen Deming ya bayyana cewa, sha'anin shigi da fici na cinikayyar da Sin ke yi yana bunkasuwa yadda ya kamata, wannan ba ma kawai wata alama ce mai kyau ga tattalin arzikin Sin ba, hatta ma zai nuna goyon baya mai karfi wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya da samun farfadowar tattalin arziki tun da wuri.(Fatima)