Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-29 21:17:38    
An samu kyawawan sakamako a yayin taro a karo na 20 na JCCT tsakanin Sin da Amurka

cri
A ran 29 ga wata, an kira taro a karo na 20 na kwamitin hadin kai a fannin kasuwanci da cinikayya wato JCCT a tsakanin Sin da Amurka a birnin Hangzhou na kasar Sin, inda aka samu kyawawan sakamako.

Wang Qishan, mataimakin firayim ministan kasar Sin da Gary Locke, ministan kasuwanci na kasar Amurka kana da wakilin Amurka kan cinikayya Ron Kirk su ne suka shugabanci taron.

Chen Deming, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana wa kafofin watsa labarai bayan taron, cewar Sin da Amurka sun bayyana cewa, ya kamata su yi yaki da samar da kariyar ciniki da zuba jari tare, da kuma bin ra'ayi daya da aka samu a yayin taron koli na G20 cikin tsanaki. Bangarorin biyu suna ganin cewa, idan ana son warware matsalar gibin kudi wajen ciniki a tsakanin Sin da Amurka, ya kamata a nemi samun daidaito wajen raya cinikayya a tsakaninsu a maimakon kayyade shigar da kayayyaki daga kasar Sin. Haka kuma bangarorin biyu sun amince da inganta hadin kansu a fannonin muhallin makamashi da hada-hadar kudi da samo kayan smar da wutar lantarki da suka gama aiki, da inganta kayayyakin masarufi, kana da sanya ido kan ingancin amfanin gona.(Kande Gao)