Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-28 11:25:36    
Kamata ya yi a raya cinikayyar tufafi ta duniya mai dorewa bisa 'yanci

cri
A ran 28 ga wata a birnin Kunshan na lardin Jiangsu na Sin, mataimakin ministan masana'antun Sin Chen Jian ya bayyana cewa, dole ne a raya cinikayyar tufafi ta duniya mai dorewa bisa 'yanci.

A wannan rana a gun dandalin tattaunawa kan cinikayyar tufafi na duniya da aka shirya a kasar Sin a shekarar 2009, Chen Jian ya bayyana cewa, an samu sashen cinikayyar tufafi mai dorewa a duniya. Kamar kasar Sin, a kowace shekara, ta kan shigar da auduga sama da ton miliyan daya, da kayayyakin da aka yi amfani domin samar da tufafi sama da ton miliyan goma, wanda ya kyautata matsalar neman guraben aikin yi na ma'aikatan masana'antu da na manoma a Amurka da Japan da Koriya ta kudu da sauransu. A sa'i daya, a kowace shekara, Sin ta fitar da tufafi da darajarsu ta kai sama da kudin Amurka dala biliyan 100 ga kasashen duniya, ta ba da kayayyakin masarufi masu kyau ga mutanen duniya.

Taken dandalin tattaunawa a wannan karo shi ne "Neman samun bunkasuwa da kuma waiwaye baya ga cinikayyar tufafi ta kasa da kasa bayan abkuwar matsalar kudi ta duniya". Wakilai sama da 200 daga Italiya da Japan da Amurka da Pakistan da Bangladesh sun halarci wannan taro.(Fatima)