Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 19:39:40    
Masu sauraron tashar CRI 10 daga sassan duniya sun kawo ziyara a nan kasar Sin

cri
Ran 27 ga wata, a nan Beijing, an yi babban taron ba da lambar yabo ta musamman ga wadanda suka yi nasarar gasar wasa kwakwalwar da gidan rediyon CRI ya shirya ga masu sauraro a  sassa daban daban na duniya domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Masu sauraronmu 10 da suka fito daga kasashe 10 sun samu lambar yabon tare kuma da samun damar yin ziyara a nan kasar Sin.

A watan Yuni na wannan shekara, gidan rediyonmu na CRI ya kaddamar da wannan gasa ta wasa kwakwalwa, inda kuma ta gidan rediyo da yanar gizonsa cikin harsuna 53 kuma ta hanyar nuna bidiyo da bayanai da hotuna, ya yi karin bayani kan tarihin kasar Sin a cikin shekaru 60 da suka wuce da kuma sauye-sauyen da mutanen Sin suka samu a zaman al'umma da tunani. A cikin watanni 3 kawai an samu wasiku don amsa tambayoyi misalin dubu 650 daga kasashe da yankuna 142 na duk fadin duniya. A yayin babban taron da aka yi a wannan rana, wadannan masu sauraro 10 sun bayyana cewa, wannan gasar wasa kwakwalwa ta bai wa masu sauraron CRI da suka fito da ga mabambantan kasashe kyakkyawar damar kara sani kan yanayin bunkasuwar kasar Sin.(Tasallah)