Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 10:58:42    
Sin ta yi gyare-gyare ga dokar zabe

cri
A ran 27 ga wata, kwamitin kafa dokoki na Sin, wato zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya fara yin nazari kan daftarin yiwa dokar zabe gyare-gyare. Kafin wannan kuma, yau da shekaru 5 da suka gabata, an yi gyare-gyare ga wannan doka.

Daftarin ya tanadi cewa, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin zai tabbatar da yawan wakilan majalisar bisa yawan mutane na kowane lardi da yanki mai zaman kansa da na birni. Kuma yawan mutanen da kowane wakili ya wakilta ya yi daidai a birane da kauyuka, ta yadda za a tabbatar da cewa, kowane yanki da kabila da fanni yana da wakilansu. A sa'i daya, daftarin ya tanadi cewa, kamata ya yi membobin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na kananan hukumomin majalisar su wakilci jama'a da yawa, tare da kasancewar wasu fararen hula.

Idan an zartas da wannan daftari, Sin za ta zabi wakilan majalisar bisa yawan mutane a birane da kauyuka na Sin cikin adalci, ta yadda za a bayyana adalci na jama'a da na yankuna da na kabilu yadda ya kamata, a yunkurin kara demokuradiyyar jama'a.(Fatima)