Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-26 16:32:25    
Manyan jami'an kula da harkokin kudi da haraji sun taru a Beijing don tattaunawa kan halin da ake ciki a fannin bunkasuwar kudi ta duniya

cri
A ran 26 ga wata, a birnin Beijing, an yi gagarumin taron tattaunawa game da samun kudin haraji na duniya a karo na uku, inda manyan jami'an kungiyoyin kasashen duniya kamar su bankin duniya, da hukumar ba da lamuni ta duniya wato IMF da dai sauransu, da kuma manyan jami'ansu dake kula da harkokin haraji suka taru don tattaunawa kan yiwuwar samun bunkasuwar harkokin kudi ta duniya da yankuna, da manufofin karbar haraji, da kuma hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin karbar haraji da sauran batutuwa.

Ministan kudi na kasar Sin Xie Xuren ya yi nuni da cewa, an tattauna kan wannan batu ne a karkashin halin da ake ciki na fama da matsalar kudi ta duniya, hakan zai amfana wajen tabbatar da ra'ayin daya da aka samu a yayin taron koli na G20 a Pittsburg, da kara daidaita manufofin haraji tsakanin kasa da kasa a fannin harkokin kudi, da kuma kyautata yanayin karbar haraji da harkokin kudi na duniya cikin adalci, kana da yin hobbasa wajen samun farfadowar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

Mataimakin shugaban gudanarwa na hukumar IMF Takatoshi Kato yana mai ra'ayin cewa, wannan taron ya samar da dama mai kyau ta yin tunani da samun bunkasuwar harkokin kudi.(Asabe)