Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-25 19:40:43    
Kasar Sin za ta rubanya kokarin raya aikin gona tare da yin tsimin ruwa

cri
Ran 25 ga wata, E Jingping, mataimakin ministan ayyukan yin amfani da ruwa na kasar Sin ya bayyana a nan Beijing cewa, kasar Sin za ta rubanya kokarin raya aikin gona tare da yin tsimin ruwa domin tabbatar da samun isashen hatsi.

An labarta cewa, yanzu yawan hatsin da Sin ta samu a ko wace shekara ya wuce kilogram biliyan dari 5 gaba daya, a maimakon kilogram biliyan dari 1 ko fiye kawai yau shekaru 60 da suka wuce, wato a daidai farkon kafuwar sabuwar kasar. Yanzu domin yin ban ruwa, ta kan yi amfani da ruwan da yawansa ya kai cubic mita biliyan 360, wanda ya kai kusan kashi 65 cikin dari bisa na ruwan da take yin amfani gaba daya.

Mr. E ya kara da cewa, kasar Sin za ta kafa karin na'urori da yin kwaskwarima ta fuskar yin tsimin ruwa a manyan yankuna 434 da ake yin ban ruwa bisa shirinta. Sa'an nan kuma, za ta yi kwaskwarima ta fuskar yin tsimin ruwa a matsakatan yankuna 1500 domin tabbatar da yin tsimin karin ruwan da yawansa zai wuce cubic mita biliyan 60 a shekarar 2020, tare kuma da samun wuraren da ake yin ban ruwa ba tare da bata ruwa da yawa ba da fadinsu zai wuce kashi 80 cikin dari bisa na wuraren da ake yin ban ruwa a duk fadin kasar Sin.(Tasallah)