Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-12 16:18:17    
An bayyana sakamakon sunayen mutane 10 aminan kasar Sin

cri
A ran 12 ga wata, an bayyana sakamakon wani zabe da aka gudanar a yanar gizo ta internet ta Sin, a yunkurin zaba mutanen ketare da suka fi ba da taimako ko kuma suke da alaka da Sin a kusan shekaru 100 da suka gabata. Gidan rediyon kasar Sin na CRI ya jagoranci wannan aiki, yayin da hukumar sada zumunta ga ketare ta jama'ar Sin da hukumar kula da masanan ketare ta Sin suka ba da taimako, kuma tashar internet ta CRI ta aiwatar da wannan aiki.

Ranar daya ga wannan wata ta kasance rana ce ta cika shekaru 60 da kafa jamhuriyyar jama'ar Sin, wannan ne daya daga cikin ayyukan da aka gudanar domin tunawa da wannan rana a Sin.

Daga karshe kuma, bayan kwanaki 40 da masu yin amfani da yanar gizo ta internet na Sin suka jefa kuri'a, aminai na ketare 10 daga cikin 'yan takara 50 sun yi nasara, wadanda su ne likita Norman Bethune, dan Canada da ya sadaukar da kansa domin ba da jiyya ga sojojin Sin a yake-yake da suka yi da sojojin Japan a shekaru 30 na karnin da ya gabata, da John Rabe, dan Jamus da ya ceci fararen hular Sin dubu 250 daga kisan kiyashi da sojojin Japan suka yi a wancan lokaci, da Juan Antonio Samaranch Toriello, tsohon shugaba mai daraja na kwamitin gasar wasannin Olympic na duniya, wanda ya dauki Sinawa a matsayin aminansa har abada, da kuma sa kaimi ga aikin neman samun ikon gudanar da gasar wasannin Olympic da birnin Beijing na Sin ya yi, da dan jaridar Amurka Edgar Snow, wanda ya gabatar da sojojin Sin da tsohon shugaban Sin marigayi Mao Zedong ga duniya baki daya bisa wani littafi mai suna "Red Star Over China", da masanin Birtaniya Dr. Joseph Needham, wanda ya yi amfani da shekaru kusan 50 domin wallafar wani muhimmin littafi mai suna "History of Science and Technology of China", da Basine Israel Epstein mai asalin Poland, wanda ya bayyana aikin yaki da hare-hare da kuma raya kasa cikin lumana da Sin ta yi bisa littattafai da labarai masu dimbin yawa a cikin shekaru sama da goma, da masanin zaman al'umma da tarbiyya na New Zealand Rewi Alley, wanda ya yi gwagwarmayar neman kafa jamhuriyar jama'ar Sin da bunkasuwarta a cikin shekaru 60, da likita Kwarkanath S. Kotnis na Indiya, wanda ya sadaukar da kansa a yake-yaken da hare-haren sojojin Japan a shekaru sama da 60 da suka gabata, da 'yar sarkin Thailand Maha Chakri Sirindhorn, wadda ta bayyanawa jama'ar Thailand tarihi da al'adun Sin cikin dogon lokaci, kuma ta ba da babbar gudummawa a fannin mu'amalar al'adun Sin da na Thailand da ta jama'ar kasashen biyu, da dan Japan Morihiko Hiramatsu, wanda ya fitar da manoman Sin masu dimbin yawa daga fatauci bisa aikin "Kafa wata shahararriyar alamar kayayyaki a kowane kauye ko gunduma ta Sin". A ciki, Norman Bethune dake kan matsayi na farko ya samu kuri'u sama da miliyan 4.6.

Tun daga ranar 31 ga watan Agusta da aka fara wannan zabe, mutanen Sin sun mai da martani sosai a yanar gizo ta internet. Ya zuwa ran 10 ga watan Oktoba, gaba daya an samu kuri'u sama da miliyan 56. A cikin bayanansu kuma, masu yin amfani da yanar gizo ta internet sun nuna godiya ga aminai na ketare.(Fatima)