Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-10 15:26:06    
An rufe taron koli na kafofin yada labaru na duniya a Beijing

cri

A ran 10 ga wata da safe, a birnin Beijing, an rufe taron kafofin yada labaru na duniya wadda mashahuran kafofin yada labaru guda 9 na duniya suka shirya kuma kamfanin yada labaru na Xin Hua ya dauki nauyin yinsa. A gun taron, an zartas da sanarwar bai daya ta taron koli na kafofin yada labaru na duniya.

Sanarwar ta ce, jigon taron shi ne "Hada kai da tinkarar matsaloli, da kuma samu nasara da bunkasuwa tare". A gun taron, an yi mu'amala kan batutuwa guda takwas, kuma an yi nazari kan halin da ake ciki a sana'ar yada labaru ta duniya da halin bunkasuwarta, kana an tattauna matsaloli a jere da kafofin yada labaru ke fuskanta yayin da ake fama da matsalar kudi ta duniya, kuma bukatun jama'a masu sauraro ke sauyawa da sauri, kana ana yi ta samun sabbin fasahohi da kimiyya.

Bugu da kari, sanarwar ta furta cewa, an yi imani da cewa a gun taron, an zurfafa ra'ayoyi, da kara samu ra'ayi daya a fannoni da dama, kuma an samu sakamako mai kyau. Taron da aka yi zai kawo tasiri mai kyau ga sana'ar yada labaru ta duniya cikin tsawon lokaci, da sa kaimi kan kafofin yada labaru da su tinkarar matsala tare da kara hadin gwiwa don samun bunkasuwa tare.(Asabe)