Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-03 20:22:59    
Jama'a na wurare daban daban na Sin sun yi murnar ranar bikin tsakiyar kaka

cri
Yau wato ran 3 ga wata, rana ce ta bikin tsakiyar kaka a kasar Sin. Jama'a na wurare daban daban na duk fadin kasar Sin sun yi murnar ranar bikin ta hanyoyi daban daban.

Ran 15 ga watan Agusta na ko wace shekara bisa kalandar gargajiya ta Sin ranar ce ta bikin tsakiyar kaka, inda 'yan iyali su kan hadu tare. Haka kuma a wannan rana, mutane su kan yi murnar bikin ta hanyoyin kallon wata da cin wani irin waina da ake kiranta Yuebing da kuma kallon fitilu masu kyan gani.

A ranar bikin tsakiyar kaka ta shekarar da ake ciki, unguwoyin biranen Shanghai da Nanjing da Fuzhou da dai sauransu na kasar Sin sun tattara mazauna domin su yi wainar Yuebing da kuma yin hira tare. A birnin Chongqing kuma an shirya bikin karanta rubutattun wakokin da aka mayar da bikin tsakiyar kaka a matsayin babban takensa. Haka kuma a gefen kogin Songhuajiang na lardin Heilongjiang, mutane sun kunna fitilu domin begen iyalin da ke wurare masu nesa.(Kande Gao)