Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 19:05:19    
Kasar Sin ta kafa huldar yin hadin gwiwa kan kimiyya da fasaha da kasashe da yankuna 152

cri
A ran 30 ga wata, Mr. Wan Gang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing, cewar a cikin shekaru 60 da suka gabata bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin, kasar Sin ta riga ta kafa huldar yin hadin gwiwa kan harkokin kimiyya da fasaha da kasashe da yankuna 152, kuma ta kulla yarjejeniyoyi 104 na yin hadin gwiwar kimiyya da fasaha a tsakanin gwamnatoci na kasashe da yankuna 97. Kuma irin wannan hadin gwiwar da ake yi kan harkokin kimiyya da fasaha a tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya ta samu karfafuwa.

A yayin taron manema labaru da cibiyar watsa labaru game da bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin ta shirya, Mr. Wan Gang ya bayyana cewa, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin  su mambobi ne na kungiyoyin ilmin kimiyya da fasaha na kasashen duniya kusan dubu 1, kuma suna taka rawa sosai a cikin wadannan kungiyoyi. Bugu da kari kuma, Mr. Wan Gang ya bayyana cewa, kasar Sin ta kafa fitattun cibiyoyi da sansanoni da dama, inda ake sa kaimi ga kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani da yin hadin gwiwar kimiyya da fasaha. (Sanusi Chen)