Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-28 16:00:19    
Kasar Sin ta samu manyan ci gaba ta fannoni biyu kan sha'anin samar da ilmi, in ji jami'in hukumar ba da ilmi

cri
A ran 28 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin ministan ilmi na kasar Sin Mr Hao Ping ya furta cewa, a cikin shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, an samu manyan ci gaba biyu, ciki har da aiwatar da tsarin ba da ilmin tilas na shekaru 9 ba tare da biyan kudi ba da kuma ba da ilmin jami'a ga dukkan jama'a.

A gun taron manema labarun da cibiyar yada labaru ta Sin ta yi domin taya murnar cika shukaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, Hao Ping ya fadi cewa, a lokacin da aka kafa sabuwar kasar Sin, mutanen kasar Sin na kashi 80 bisa 100 ko fiye suna da karancin ilmi, amma, ya zuwa yanzu, kashi 3.6 bisa 100 na matasan kasar Sin ne kawai suke cikin irin wannan hali, kuma yawan mutanen da suka shiga makarantar firamare da ta midil ya kai kusan kashi 99 bisa 100. Dadin dadawa, yawan daliban jami'a ya kai miliyan 20 wanda ya kai matsayi na farko a duniya.

Hao Ping ya bayyana cewa, bunkasuwar sha'anin samar da ilmi da Sin ta samu ta samar da kwararru miliyoyi ga kasar. (amina)