Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-28 15:26:31    
An yi bikin nune-nunen hotuna na nuna zumuncin dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa

cri
A ran 28 ga wata, a Beijing, an yi bikin nune-nunen hotuna na tsofaffin jakadun kasar Sin da suka yi aiki a kasashen Gabas ta tsakiya wadanda suka sheda dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa. Baki na gida da na waje kimanin dari uku sun halarci bikin bude taron.

A gun bikin, an nuna hotuna fiye da 150 da tsofaffin jakadun kasar Sin 22 da suka yi aiki a kasashen Gabas ta tsakiya suka tanada. Wadannan hotuna sun nuna zaman rayuwar jakadun kasar Sin a kasashen Larabawa, da ma'amalar da aka yi tsakanin Sin da kasashen Larabawa. An yi wannan biki ne don murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, da taya murnar bunkasuwar dangantakar a tsakanin Sin da kasashen Larabawa cikin goman shekaru da suka gabata, ta yadda za a nuna gudummawar da tsofoffin jakadun kasar Sin a kasashen Gabas ta tsakiya suka bayar domin bunkasa dangantakar a tsakanin Sin da kasashen Larabawa.(Asabe)