A ran 25 ga wata, wasu 'yan jarida a gida da waje da suke bayar da labaru a game da bukukuwan murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin sun kai ziyara a masallacin unguwar Niujie dake a karamar hukumar Xuanwu ta birnin Beijing.
Unguwar Niujie tana daya daga cikin yankunan dake da sigar musamman ta kabilu a birnin Beijing, kuma ita ce yanki mafi girma da 'yan kabilar Hui suke zauna a birnin, inda akwai 'yan kabilu 27 na Hui da Man da Uyghur da Han da dai sauransu. Yawan 'yan kabilar Hui dake a yankin ya kai dubu 12, wato ya kai kashi 23% na dukkan mutanen dake a yankin.
Masallacin unguwar Niujie wani masallaci ne mafi dogon tarihi da girma a birnin Beijing, kuma yana daya ne daga cikin mashahuran masallatai a duniya, musulmai masu yawa su kan yi addu'a a masallacin a kowace rana.(Zainab)
|