Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-02 10:34:35    
Ganawa tsakanin shugabannin Sin da Amurka

cri

A ran 1 ga wata, shugaban Sin Hu Jintao ya gana da shugaban Amurka Barack Obama a birnin London, inda bangarorin biyu suka cimma daidaito kan inganta dagantakar hadin gwiwa a duk fannoni tsakaninsu a karni na 21.

Hu Jintao ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen biyu su yi kokari tare wajen inganta dagantakar hadin gwiwa a duk fannoni tsakaninsu a wannan sabon karni.

Obama ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin Amurka da Sin muhimmiyar dangantaka ce a fadin duniya, ba ma kawai akwai dangantakar tattalin arziki tsakaninsu ba, hatta ma akwai moriyar bai daya kan manyan batutuwan duniya da yankuna.

Shugabannin kasashen biyu sun cimma daidaito kan kafa wani tsarin shawarwarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu. Bangarorin biyu za su yi shawarwari karon farko a birnin Washington a lokacin zafi na shekarar 2009.

Obama ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka ta tsaya tsayin daka a kan manufar Sin daya tak, da nuna goyon baya ga hadaddiyar sanarwa guda 3 tsakanin kasashen biyu. Amurka ta yi maraba da nuna goyon baya kuma kyautata dangantaka tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, da tana fatan za a samu ci gaba kan wannan batu. Yankin Tibet wani yankin kasar Sin ne, Amurka ta ki amincewa da yancin kan Tibet.

Shugabannin biyu sun amince da yin kokari tare don warware batutuwan nukiliya na yankin teku na Koriya da Iran, da ba da gudummawar jin kai a Sudan da kuma halin kasashen kudancin nahiyar Asiya da dai sauransu.(Zainab)