|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-04-01 09:05:27
|
|
Shugaba Hu Jintao ya tashi zuwa Birtaniya domin halartar taron koli na G20
cri
A ran 1 ga wata da safe, bisa gayyatar firaministan Birtaniya Gorden Brown, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga birnin Beijing zuwa birnin London a Birtaniya domin halartar taron koli a karo na 2 na hada-hadar kudi na shugabannin kasashe mafiya karfin tattalin arziki 20. A gun taron kolin, shugabanni mahalarta za su yi shawarwari kan karfafa manufar tattalin arziki a manyan fannoni da kara sa ido kan hada-hadar kudi na duniya, da tabbatar da kasuwannin hada-hadar kudi, da yi wa hukumomin hada-hadar kudin duniya garambawul, domin tinkarar matsalar kudi da duniya ke fuskanta, da neman haryar farfado da tattalin arzikin duniya. A lokacin halartar taron kolin, shugaba Hu zai gana da shugaban Amurka Barack Obama da firaministan Birtaniya Gorden Brown da shugaban Rasha Dmitry Medvedev da sauransu, kuma za su yi musanyar ra'ayi dangane da dangantaka tsakanin bangarorin biyu da harkokin da suka fi jawo hankula.(Fatima)
|
|
|